29
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dakarun Operation SAFE HAVEN na rundunar Sojojin Nijeriya sun kama wasu mashahuran ’yan bindiga, masu safarar makamai da kuma ƙwato makamai a wasu ayyukan sirri da suka gudanar a jihohin Filato da Kaduna cikin mako guda da ya wuce. A ranar 21 ga watan Yunin 2024, sojoji sun gudanar da wani samame na fatattakar 'yan bindiga da wasu masu aikata laifuka a maɓoyarsu da ke dajin Pandam a ƙaramar hukumar Ƙua’anpan ta Jihar Filato. A yayin samamen, sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3, cinkun alburusan AK-47 guda 5 da harsashi 75 mai tsawon 7.62mm…
