28
Jun
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ɗauki ma'aikata 17,400 domin tsare makarantun firamare a faɗin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya sanar da hakan a shafinsa na Ɗ, ya ce matakin wani ɓangare ne na ci gaba da aiwatar da ayyuka domin dacewa da muradin gwamnatin na dawo da ƙimar ilimi a jihar. Gwamnan ya ce " za a ɗauki ma'aikatan ne daga kowacce ƙaramar hukuma domin su tsare sabbin azuzuwan da za a gina da kuma tabbatar da lafiya da tsaron malamai da ɗalibai". Wannan dai na zuwa ne 'yan awanni bayan…
