ukarofi

11625 Posts
Nijeriya za ta nemi gudunmawar rigakafin Kwalara bayan ta’azzarar annobar cutar

Nijeriya za ta nemi gudunmawar rigakafin Kwalara bayan ta’azzarar annobar cutar

Gwamnatin tarayya na tunanin neman rigakafin cutar kwalera ganin yadda annobar cutar ke ƙara ta'azzara a ƙasar. Shugabar hukumar Gavi, Dr Sania ta wallafa a shafinta na X cewa, Gavi ta damu da ɓarkewar annobar kwalera a Najeriya, don haka a shirye suke don su bada nasu tallafin rigakafi wajen ganin an shawo kan matsalar. Magunguna uku da Hukumar lafiya ta duniya ta sahale amfani dasu sun haɗa da Dukoral, Shancol da Euvichol.
Read More
Ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen jidon kuɗin sata, inji Ministan Sufurin Sama

Ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen jidon kuɗin sata, inji Ministan Sufurin Sama

Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo, yace aña amfani da jirage masu zaman kansu wajen jidon kuɗaɗe da aka sata da safarar miyagun ƙwayoyi. Ministan ya bayyana haka ne a yayin wani taro na hukumar sufurin jiragen sama, inda ya bayyana cewa taron ana yin sa ne domin kawo ƙarshe ayyukan bijirewa doka da jirage masu zaman kansu suke yi. Keyamo ya ƙara da cewa, wasu dayawa sun karya ƙa'idojin lasisin da aka basu domin suyi aiki. Wanda hakan ya jawo ma Najeriya asarar kuɗaɗen shiga da dama. Daga ƙarshe ya kafa kwamiti wanda zasu bincika ayyukan jiragen masu zaman…
Read More
Dogo Giɗe na ba manoma kariya a Zamfara

Dogo Giɗe na ba manoma kariya a Zamfara

Mazauna garin Magami dake ƙaramar hukumar Gusau sun yi murna sosai saboda dawowar Dogo Giɗe wannan yankin. Giɗe ya ba yan garin umarnin su koma gonakin su ba tare da tsoron wani zai kama su ba. Dogo Giɗe shine shahararen ɗan bindigar nan, wanda dashi a cikin wanda suka sace yara yan makaranta na garin Kuriga dake jihar Kaduna. Bayan artabun shi da sojoji, Giɗe ya dawo wani gari da ake kira Kizara, wanda yake gabashin Magami. A nan ne yace mutane su koma gonakin su zai basu kariya.
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙi Rarara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙi Rarara

Daga Umar Garba a Katsina Wasu 'yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afka gidan hajiya Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Adamu Kahuru Rarara a gidanta dake Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina. Rahotanni da Blueprint Manhaja ta samu na nuna cewar 'yan bindigar sun yi dirar mikiya a gidan hajiya Halima da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar dare. Mazauna garin da lamarin ya faru a gabansu sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa,  “A kafa suka zo, kuma kasancewar ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin sun yi garkuwa da ita…
Read More
Filisɗine ta yi kira ga Najeriya ta amince da ita a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta

Filisɗine ta yi kira ga Najeriya ta amince da ita a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta

Filisɗine ta aika wa gwamnatin najeriya wata takarda a ranar 27 ga watan Yuni, inda ta buƙaci Najeriya ta aminta da Filisɗine a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Bayan nan, sun yi kira ga ƙasashe da su taimaka wajen ganin an gurfanar da Isra'ila gaban kotun duniya sabida laifuka yaƙi da suka tabka a harin da suke kaiwa Filisɗine din wanda ya shafe watanni ana fama dashi. A cewar takardar, kullum alƙaluman da ke fitowa daga Filisɗine abun tsoro ne. Kuma sun koka da yadda cewa duk wani dokar ƙasa da ƙasa baya aiki in dai ƙasashen yamma sun…
Read More
Yunwa ce ta tilasta mani kai wa ɓarayin daji harsashin bindiga – Aisha

Yunwa ce ta tilasta mani kai wa ɓarayin daji harsashin bindiga – Aisha

Daga Umar Garba a Katsina Matar nan mai suna Ai'sha Abubakar da jami'an tsaro suka cafke ɗauke da tarin harsashin bindiga ta ce yunwa ce ta jefa ta harkar yi wa 'yan bindiga safarar harsasai. A ƙarshen makon da ya gabata Blueprint Manhaja ta rawaito cewar jami'an tsaron dake sintiri a kan hanyar Abuja sun kama wata mata da ta hau motar sufuri ta jihar Katsina wato KTSTA daga jihar Nassarawa zuwa jihar Katsina. An kama ta ne ɗauke da harsashin bindiga da ba a ƙididdiƙe yawansa ba cikin buhu a ƙoƙarinta na kai wa 'yan bindigar dake ta'addanci a…
Read More
Babbar kasuwar Karu ta kama da wuta

Babbar kasuwar Karu ta kama da wuta

Rahoto da yake isa jaridar Blueprint ya nuna cewa wata babbar kasuwa a Karu ta kama da wuta. Ƙwararren ɗan jaridan nan, Ezeocha Eze ne ya sanar ta manhajar WhatsApp a daren Alhamis. Yace masu yaƙi da gobar sun hallara domin kashe gobarar amma duk da haka wutar na cigaba da ci. Har ya zuwa lokacin wallafa rahoton, hukumomi ba suyi magana ba.
Read More
Shugaban hukumar EFCC ya umarci a kama jami’an hukumar da suka faɗa ɗakin otal a Legas

Shugaban hukumar EFCC ya umarci a kama jami’an hukumar da suka faɗa ɗakin otal a Legas

Shugaban hukumar EFCC Mr Ola Olukoyede, ya umarci da a kama jami'an hukumar waɗanda suka faɗa otal a Legas. A wani faifan bidiyo, an nuna wasu jami'an EFCC din sun kutsa kai cikin wani ɗakin otal inda suka mari wata mata da tace ma'aikaciya ce a otal din. Duk abinda ya faru wata kyamaran CCTV dake otal din ta naɗa. Shugaban hukumar ya cigaba da cewa atisayen ranar, ya faru da safiya sannan sunyi nasarar cafke masu laifi da dama. Yace kuma jami'an sa da suka wuce gona da iri, za ai bincike mai zurfi domin hukunta su.
Read More
Rikicin masarauta: Na zo Kano don aiki, ba don wasu ba – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Rikicin masarauta: Na zo Kano don aiki, ba don wasu ba – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Sabon Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Salman Dogo ya musanta zargin da ake na cewa yana da alaƙa da Sarkin Kano da aka tuɓe, Aminu Ado Bayero. Yace yazo Kano ne domin ya hidimtawa al'umma baki ɗaya. Ba batun bambancin addini ko ƙabila. Domin yace shi ɗan Najeriya ne, don haka aikinsa shine ya hidimtawa Najeriya ko a ina. Ya roƙi cewa yan Kano su bashi haɗin kai domin ganin sun yi maganin abunda ke damun jihar.
Read More
Guguwa da ruwan sama sun ruguza gine-gine a makarantar koyon kiwon lafiya ta Jahun

Guguwa da ruwan sama sun ruguza gine-gine a makarantar koyon kiwon lafiya ta Jahun

Daga Umar Akilu Majeri Dutse Wata Guguwa Mai ƙarfin gaske da ruwan Sama mai ƙarfin gaske sunyi sanadin ruguza Gine Gine masu yawa a makarantar nazarin Kiwon Lafiya ta Jahun a daidai lokacin da ɗalibai suke ƙoƙarin dawowa makarantar domin cigaban da zangon karatu karon farko. Guguwar tayi Mummunan ta adi wadda idan gwamnatin batayi wani na mijin ƙoƙari za aiya samun tangarɗa a harkokin karatu na makarantar dubada yadda gwamnatin ta damu akan Matsalar karancin likitoci da karancin ma aikatan lafiya a fadin asibitocin dake jihar da Kuma yadda Gwamnatin tàke kashe makudan kudade a duk shekara da nufin…
Read More