ukarofi

11614 Posts
Majalisa ba ta taɓa yin ƙudirin siyo wa Tinubu da Shettima sabon jirgi ba – Akpabio

Majalisa ba ta taɓa yin ƙudirin siyo wa Tinubu da Shettima sabon jirgi ba – Akpabio

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya musanta zargin da ake na cewa, majalisa ta 10 na yunƙurin sahale siyowa Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa sabon jirgi. Akpabio, a yayin zantawarsa da yan jarida a Maiduguri yace wannan zargin Ƙaryane kawai. A cewar wata sanarwa daga mai taimaka ma Akpabio ɗin na shafukan sada zumunta Jackson Udom, yace Kakakin Majalisar yaje Maiduguri ne domin yin ta'aziyya ga Sanata Mongunu sabida rashin mahaifinsa. Akpabio yayi murna ƙwarai ganin yadda zaman lafiya ya dawo garin Maiduguri. Yace wannan kaɗan daga cikin irin jajircewa ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne.
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: Babban jami’in Kwastom ya rasu yayin gurfana a Majalisar Wakilai

DA ƊUMI-ƊUMI: Babban jami’in Kwastom ya rasu yayin gurfana a Majalisar Wakilai

Wani babban jami'in kwastom ya rasu a asibitin majalisa dake Abuja. Marigayin baƙo ne da yazo majalisa domin amsa kiran da majalisa tayi wa hukumomin gwamnati dake tara haraji. Yana cikin tambayar 'ƴan majalisa sai ya faɗi. An kaishi asibitin cikin majalisar cikin gaggawa inda rai yayi halinsa. A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar ya fitar, Akin Rotimi, yace yana sanar da al'umma rasuwar jami’in kwastom da ya gurfana gaban majalisar. Sabida mutuntawa ba zamu faɗi sunan jami'in ba.
Read More
Ku yi amfani da damar da arewa-maso-yamma ta samu na ƙarfafa nasarar ci gaba- Fall

Ku yi amfani da damar da arewa-maso-yamma ta samu na ƙarfafa nasarar ci gaba- Fall

Yayin da Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma da Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya ke yunkurin tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi amfani da damar da yankin Arewa-maso-Yamma ya samu masu yawa ta hanyar karfafa nasarar cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) da kuma kafa hanyar samar da ci gaba na dogon lokaci da magance matsalolin al’ummar yankin. "Bari mu kuma shiga cikin babbar damar da yankin ke da ita don karfafa…
Read More
Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto

Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto

Daga Umar Garba a Katsina Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto game da wasu rahotanni dake bayyana cewar gwamnatin jihar ta tura wata doka zuwa majalisar dokokin jihar wadda za ta rage wa Sarkin Musulmi ƙarfin iKon da yake da shi ko kuma ta kore shi daga kan kujerar ta sa. " Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, kujera ce wadda wajibi ne dukkanmu mu kare ta, mu ɗaukaka ta don amfanin ƙasa." Inji shi.Shettima ya bayyana haka ne a wajen taron haɗin gwiwa wanda gwamnonin jihohin arewa maso yamma haɗin gwiwa…
Read More
Sojoji sun kuɓutar da mutane 98 daga hannun yan ta’adda, cikinsu har da ƴar Chibok

Sojoji sun kuɓutar da mutane 98 daga hannun yan ta’adda, cikinsu har da ƴar Chibok

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da aƙalla mutane 98 daga hannun yan ta'adda, cikinsu harda yarinya ɗaya daga cikin yan matan Chibok da akai garkuwa dasu shekerun baya. Anyi wannan nasarar ne a wani atisayen soja mai taken " Operation Lake Sanity II" wanda cigaba ne daga atisayen baya mai taken "Operation Hadin kai" Wasu bayanai na sirri da Zagazola, ƙwararre a harkar tsaro ya samu ya nuna yar Chibok ɗin da aka ceto itace mai lamba ta 64 a cikin jerin sunayen yan matan Chibok ɗin da akai garkuwa dasu.
Read More
Shoprite za su rufe ofishinsu na Abuja 30 ga watan Yuni

Shoprite za su rufe ofishinsu na Abuja 30 ga watan Yuni

Babban kantin nan na Shoprite sun sanar da niyyar su na rufe ɗaya daga cikin ofishinsu dake Abuja daga ranar 30 ga watan Yuni. Sun sanar cewa, za su rufe ofishin nasu dake Novare Central Mall, Wuse Zone 5. Wani ma'aikacin Shoprite ɗin wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, yace zancen gaskiya ne, suma haka suke samun labari.
Read More
‘Ƴan bindiga sun kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo

‘Ƴan bindiga sun kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo

'Ƴan bindiga sun kashe mataimakin Shugaban Jami'ar Usmanu Dan fodio Farfesa Yusuf Saidu. A litinin ɗin yau makarantar ta fitar da sanarwa cewa hakan ya faru ne a kan hanyar shi daga Kaduna zuwa Sokoto. Sanarwar ta ce " mutuwar Farfesa Saidu Yusuf, Mataimakin Shugaban Jami'ar a kan ƙirkire ƙirƙire da cigaba na Jami'ar" Hukumar makarantar ta bayyana mutuwar shi a matsayin wani babban rashi ga makarantar, suna addu'a Allah ya jiƙanshi, yayi mashi rahama.
Read More
Za a iya ɗaukar shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga – Sarkin Musulmi

Za a iya ɗaukar shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga – Sarkin Musulmi

Daga Umar Garba a Katsina Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce za a iya ɗaukar tsawon shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga da ta addabi yankin arewa maso yammacin ƙasar nan. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a yau Litininin, wajen babban taron haɗin gwiwa wanda gwamnonin Jihohin arewa maso yamma haɗin gwiwa da hukumar jinƙai ta majalisar ɗinkin duniya (UNDP) suka shirya a jihar Katsina don inganta yanayin tsaro a jihohin yankin. “Abin da ya kamata mu yi shi ne ƙalubalantar waɗannan 'yan bindiga saboda mun san irin illar 'yan ta da ƙayar…
Read More
Surukar Mataimakin Shugaban Ƙasa ta rasu

Surukar Mataimakin Shugaban Ƙasa ta rasu

Surukar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Hajiya Maryam Albishir, ta rasu a jiya lahadi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Mai magana da yawun da Mataimakin Shugaban ƙasa Stanley Nwkocha ne ya fitar a wata sanarwa ranar Litinin. Mr Nwkocha ya ƙara da cewa za a yi jana'izar ta da yammacin ranar Litinin a jihar Kano kamar yadda musulunci ya tanada. Marigayiyar an mata shaida a matsayin mutum mai jajircewa da tausayi.
Read More