29
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Talata ne ɗaliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Federal Polytechnic Bauchi da ke zaune a unguwar Gwallameji suka fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da yawaitar matsalar fashi da makami da fyaɗe a yankin. Ɗaliban a yayin zanga-zangar sun tare babbar hanyar gwamnatin tarayya da ke kan hanyar Bauchi zuwa Dass. A cewar wata sanarwar manema labarai da rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta fitar, ta ce zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon wani lamari da wasu ’yan daba suka kutsa kai cikin gidajen ɗalibai tare da yi wa wani Cletus Chomo, ɗan…
