06
Jul
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Bankin Fidelity ya gudanar da taron ganawa da abokan hulɗarsu da kuma faɗakar da jama'ar Jihar Kano tsarin sayar da hannun jarin da bankin ya soma. Daraktan a bankin, Alhaji Isa Muhammad Inuwa ya shaida wa manema labarai a yayin taron da aka yi ranar Talata cewa sun yi taron ne domin sanar da mutane da jawo hankalin musamman abokan hulɗar su muhimmancin sayen hannun jari a bankin. Ya ce sun tattauna da nunawa mutane yanda za su iya sayen hannun jarin bankin da kuma dalilai da ya kamata mutane su sanya jarinsu da za…
