ukarofi

12364 Posts
KEDCO ta katse wa Jami’ar Dangote lantarki kan bashin miliyan N248

KEDCO ta katse wa Jami’ar Dangote lantarki kan bashin miliyan N248

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya katse wutar lantarki ga Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, kan bashin Naira miliyan 248. Manajin Darakta na KEDCO, Alhaji Abubakar Yusuf, ya shaida wa manema labarai a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Litinin da ta gabata cewa kamfanin ba shi da wani zaɓi illa ɗaukar mataki. Ya ce, jami'ƙr ta biya Naira miliyan 20 ne kawai daga cikin Naira miliyan 248. Yusuf ya sha alwashin cewa za a maido da wutar lantarki ne kawai idan hukumar ta yi "biya na mutunci". Ya kuma bayyana cewa KEDCO…
Read More
Dangote ya soki ƙarin kuɗin ruwa da CBN ta yi

Dangote ya soki ƙarin kuɗin ruwa da CBN ta yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya soki sabon ƙarin kuɗin ruwa zuwa kusan kashi 30 cikin 100 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi. Aliko Dangote ya ce, yin hakan zai ƙara durƙusa sana'o'i tare da rufe ƙofa ga waɗanda suke ƙoƙarin fara sana'a. Yayin da yake jawabi a wajen buɗe taron kwanaki uku da ƙungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta shirya a ɗakin taro na Banƙuet da ke fadar gwamnatin tarayya Abuja, a ranar Talata, Dangote ya ce ‘yan kasuwa ba za su iya jurewa halin da ake ciki yanzu ba. Alhaji Aliko Dangote…
Read More
Tinubu ya yi kuskure wajen aiwatar da cire tallafin fetur, inji Moghalu

Tinubu ya yi kuskure wajen aiwatar da cire tallafin fetur, inji Moghalu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Farfesa Kingsley Moghalu, ya ce cire tallafin man fetur da rage darajar Naira da Shugaba Bola Tinubu ya yi, manufofin suka ƙara tagayyara Nijeriya. Farfesan a fannin tattalin arziki ya ce duka tallafin man fetur da kuma canja fasalin naira da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan CBN, Godwin Emefiele suka yi ba ita ce manufa mafi dacewa ga ƙasar nan ba. Moghalu ya ce abin da ya dame shi su ne cire tallafin man fetur da kuma hauhawar Dalar Amurka akna naira. Kuma Shugaba Tinubu ya…
Read More
Tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyancin hali – Shettima

Tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyancin hali – Shettima

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya amince da cewa a halin yanzu tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyanci hali. Sai dai ya jaddada cewa wannan matsala ba Nijeriya kaɗai ke fuskanta ba, don haka ya buƙaci 'yan ƙasar da su marawa shugaba Bola Tinubu baya kan shawo kanta. Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taron kwana ɗaya da ƙungiyar ba da damar kasuwanci ta ƙasa (PEBEC) ta shirya a Abuja ranar Juma’a. Ya ce, “Dole ne mu haɗa kai da Shugaba Tinubu a wannan mawuyacin lokaci. Haƙiƙa tattalin arzikinmu yana fuskantar matsaloli, amma wannan…
Read More
Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Kaduna, Kano da Katsina

Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Kaduna, Kano da Katsina

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da yanayin da duniya ke ciki, NIjeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin abinci da ba a tava yin irinsa ba. Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya fitar a jihohin Kaduna, Kano da Katsina ya nuna cewa ba bar Nijeriya a baya ba. Misali, wani bincike da NAN ta gudanar a Kaduna ya nuna cewa an samu qaruwar farashin shinkafa, biredi, sikari, garri, naman sa da kwai da dai sauran su, waxanda su ne ginshiqin abinci a gidaje. Haka nan, hauhawar farashin ya yi tasiri a rayuwar yawancin gidaje, domin kuwa yanzu suna fuskantar…
Read More
Ɗan sandan da ya ƙi karɓar cin hancin miliyan N150 ya samu kyautar fili a Abuja

Ɗan sandan da ya ƙi karɓar cin hancin miliyan N150 ya samu kyautar fili a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshen makon da ya gabata ne wani Sufetan 'yan sanda (SP), Ibrahim Ezekiel Sini, wanda ya ƙi karɓar cin hancin Naira Miliyan 150 daga hannun wani ɗan kasuwa a Legas kuma wanda ya kafa Platform Capital, Akintoye Akindele, an karrama shi tare da ba shi fili a Abuja. Kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, wanda ya ba da kyautar filin a madadin abokan aikinsa na 'yan sandan, ya ce halin da SP Sini ya nuna ya sa rundunar ’yan sandan Nijeriya alfahari. Har ila yau, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya…
Read More
Dalilinmu na kai farmaki ga kadarorin masu ta’ammali da ƙwayoyi – Marwa

Dalilinmu na kai farmaki ga kadarorin masu ta’ammali da ƙwayoyi – Marwa

Daga MAHD M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, Mohamed Buba Marwa ya bayar da hujjar matakin da hukumar ta ɗauka na bin kadin kadarorin ɓarayin shanu da masu safarar miyagun ƙwayoyi a cigaba da ɗaukar matakin da ya dace na yaƙi da miyagun ƙwayoyi. Marwa ya bayyana dalilin da ya sa hukumar ta sake yin sabon yunƙuri a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Laraba 19 ga watan Yuni 2024 don fara gudanar da ayyuka na tsawon mako guda don murnar zagayowar ranar yaƙi da muggan ƙwayoyi da safarar miyagun ƙwayoyi…
Read More
Sanata Marafa zai janye tsayawar da yi wa Sanata Yari a EFCC

Sanata Marafa zai janye tsayawar da yi wa Sanata Yari a EFCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sanata Kabiru Garba Marafa, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, ya bayyana aniyarsa ta janye tsayar da ya yi wa tsohon Gwamna Abdulaziz Yari. Wannan matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara kunno kai a cikin jam’iyyar APC ta Zamfara, wanda ke nuna gagarumin sauyi a fagen siyasar jihar. A baya dai, Sanata Marafa, ya taka rawa wajen ganin an saki Yari daga hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa ta EFCC bisa beli. Ana kallon wannan aiki a matsayin wata alama…
Read More
Ɗan Majalisar Wakilai daga Abiya ya nemi Buhari ya sa baki kan sakin Kanu

Ɗan Majalisar Wakilai daga Abiya ya nemi Buhari ya sa baki kan sakin Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan majalisa Obi Aguocha (jami'iyyar LP a Abia) ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tare da buƙatar sa baki don ganin an sako Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara, IPOB. Aguocha, mai wakiltar mazaɓar Ikwuano/Umuahia ta Arewa/Umuahia ta kudu a jihar Abia, ya bayyana ma’anar ziyarar ta sa a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Ya ce, ya je Katsina ne domin ya nemi Buhari ya shiga tsakani da kuma neman goyon bayan sa don tattaunawa ta siyasa da kuma kyakkyawar alaƙa. Wannan, a cewarsa, zai haifar da…
Read More
 Yadda direban tasi a Birtaniya ke karɓar albashin gwamnatin Nijeriya

 Yadda direban tasi a Birtaniya ke karɓar albashin gwamnatin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A duk lokacin da ka ajiye aiki, abu na farko da ke faruwa da kai shi ne daina samun albashi daga wajen aikin da ka bari, amma ba haka abin yake ba ga ma'aikatan gwamnati da dama a Nijeriya. Suna samun aiki a wasu wurare na daban, wani lokaci ma a ƙasashen waje kuma duk da haka suna ci gaba da karɓar albashi daga tsohon wajen aikin nasu. Labarin irin wannan yanayi ya yi ƙamari ta yadda sai da ta kai ga a makon jiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike…
Read More