ukarofi

12364 Posts
COAS ya raba kayan sawa da takalma ga yara marasa galihu 400 a Zamfara

COAS ya raba kayan sawa da takalma ga yara marasa galihu 400 a Zamfara

Daga Sanusi Muhammad, Gusau A ci gaba da kokarin inganta hadin gwiwar rundunar sojoji da farar hula, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar TA Lagbaja, ya raba wa yara marasa galihu 400 tufafi da takalma a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Kwamanda rundunar ta daya, 1 brigade Gusau, Brig. Janar S. Ahmed wanda ya wakilci babban hafsan soji a lokacin rabon kayan da aka gudanar a asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau ya ce, taron wani bangare ne na bikin ranar sojoji ta shekar 2024, yayinda sojojin Najeriya ke gudanar da ayyukan gaggawa ga al'ummomin da ke zaune a…
Read More
Layin mai ya dawo Abuja, yayin da ake sayar da litar mai N850

Layin mai ya dawo Abuja, yayin da ake sayar da litar mai N850

Dogon layi a gidajen mai ya fara dawowa a babban birnin tarayya Abuja, Niger da wasu sassa na Jihar Niger. Hakan na faruwa ne bayan gidajen mai da dama sun rufe gidajen man su. Wannan dawowar layin mai, ya sanya tsoro cikin mutane , masu abun hawa da fasinjoji. Wannan yayi sanadiyar ana sayar da mai nera 850 a kan duk lita ɗaya a wasu gidajen man. Masu bunburutu anga sun dawo bisa hanya, wannan alama ce da ke nuna man ya fara wahala. A bunburutu aƙalla lita na kai wa har nera 1000. Mutane da dama na kokawa kan…
Read More
Masoud Pezeshkian ya lashe zaɓen ƙasar Iran

Masoud Pezeshkian ya lashe zaɓen ƙasar Iran

Masoud Pezeshkian ne yayi nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar Iran. Masoud ya sami wannan nasarar ne bayan doke abokin hamayyar sa Saeed Jalili. An ayyana Masoud a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kaso 53.3% na kuri'un da aka kaɗa. Abokin hamayyar shi, ya samu kaso 44.3.Wannan zaɓen shine zagaye na biyu bayan da ba a samu yawan adadin da ake bukata ba na cin zaɓen. Wannan zaɓen an yi shi ne, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar a wani haɗarin jirgi a watan Mayu. Shugabannin ƙasashe irinsu Rasha, China da Indiya sun taya sabon shugaban murna.
Read More
Ɗan majalisar dokokin Jihar Zamfara ya aurar da marayu 105 da ‘yan bindiga suka kashe iyayensu

Ɗan majalisar dokokin Jihar Zamfara ya aurar da marayu 105 da ‘yan bindiga suka kashe iyayensu

Daga Sanusi Muhammad, Gusau Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bungudu da Maru a jihar Zamfara Hon. Abdulmalik Zubairu ya dauki nauyin auren ‘yan mata 105 da ‘yan bindiga suka mayar marayu a mazabar sa. Da yake jawabi yayin bikin da aka gudanar a garin Bungudu hedikwatar karamar hukumar Bungudu a yau Asabar, Hon. Zubairu ya bayyana cewa manufar shirin shine, a baiwa ‘yan matan damar yin aure cikin sauki. A cewarsa, kayayyakin da aka bai wa sabbin ‘yan matan da aka aurar da su sun hada da gadaje, cikakkun Katifu, tufafi, saitin Kujeru da kuma kayan dafa abinci.…
Read More
Euro 2024: Ƙasar Faransa ta doke Portugal, yayin da Jamus ta sha ƙashi hannun Spain

Euro 2024: Ƙasar Faransa ta doke Portugal, yayin da Jamus ta sha ƙashi hannun Spain

Ƙasar Spain ta samu nasarar doke twakararta ta ƙasar Jamus, wanda sune masu masaukin baƙi. Mikel Merino shine yayi nasarar jefa ƙwallo a cikin ragar Jamus a minti na 119. Wannan wasan, ya kasance wasa mai zafi da mutane da dama ke ganin dole sai an kai ruwa rana, wanda tabbas wasan ya kayatar matuƙa. A ɗayan fannin kuma, Ƙasar Portugal tasha kashi hannun ƙasar Faransa a bugun fanereti. Wasan shima ya ƙayatar sosai, tunda aka tashi kunnen doki. Wannan wasannin sun zama wasa na karshe ga yan wasa Cristiano Ronaldo, Pepe da kuma Toni Kroos daga Jamus.
Read More
Gamsuwa da gwamnatin Abba ya sa ƙasashaen labarawa suka bai wa al’ummar Kano tallafin ilimi – Sheikh Tijjani Auwalu

Gamsuwa da gwamnatin Abba ya sa ƙasashaen labarawa suka bai wa al’ummar Kano tallafin ilimi – Sheikh Tijjani Auwalu

Daga MUHAMMADU MAJITTABA a Kano Kwamishinan Al'amuran Addini na Jihar Kano Hon. Tijjani Sani Auwalu ya bayyana cewa gamsuwa da yadda gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ne musabbabi kuma dalilin da ya sa wasu ƙasashan Musulmi Larabawa kamar irin su Misra, Kuwait, Maroko, Turkiyya, Saudiyya da sauransu, suka yarda su zo, su bai wa gwamnatin Kano tallafin bunƙasa ilimi domin amfanin al'ummar Kano a wannan lokacin. Bayanin hakan ya fito ne daga baki Sheikh Tijjani Sani Auwalu a lokacin hira da manema labarai a birnin Kano, inda ya ce yanzu haka akwai wata gidauniyya da ake kira Alfijir…
Read More
NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci a harkokin man fetur na Nijeriya – Kyari

NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci a harkokin man fetur na Nijeriya – Kyari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin man fetur na gwamnatin Nijeriya NNPCL ya ce ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar. Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya ce sun ɗauki matakin ne da zimmar haɓaka yawan man da ake haƙowa, yana mai cewa bincikensu ya nuna "Nijeriya za ta iya haƙo fiye da ganga miliyan biyu duk rana". "Mun ayyana yaƙi ne a kan ƙalubalen da muke fuskanta a harkokin haƙo fetur. Mun shaida wa abokan hulɗarmu, muna da kayan aikin aiwatar da hakan kuma mun san abin da za mu yi,"…
Read More
 Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa ba su da kishin Nijeriya — Matawalle

 Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa ba su da kishin Nijeriya — Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana wadanda ke shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a 2027 a matsayin ’yan siyasa marasa kishin ƙasa. Ya kuma kara da cewa babu wani taron-dangi da zai hana shugaban ƙasa tsayawa takara da kuma lashe zaɓen 2027. Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan yunƙurin da wasu ‘yan siyasar Arewa ke yi na kushe gwamnatin Tinubu, inda su ke bada misali da salon mulkinsa. Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar,…
Read More
Kotu ta yanke wa masu garkuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa masu garkuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya

  Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Osun ta yanke wa wasu masu garkuwa biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin sace wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Adamu, tare da kashe shi. An gurfanar da mutanen biyar a gaban alƙali bisa tuhume-tuhume da suka ƙunshi haɗa baki don yin garkuwa da mutumin da kuma laifin kisan kai, zargin da suka musanta a lokacin da aka fara gurfanar da su ranar 28 ga watan Oktoban 2021. BBC Hausa ta ruwaito cewa a lokacin zaman sauraron shari’ar, lauyan gwamnati, Faremi…
Read More
Wasu manoma a Ɗanja sun nemi gwamnatin Jihar Katsina ta biya su diyyar gonakinsu

Wasu manoma a Ɗanja sun nemi gwamnatin Jihar Katsina ta biya su diyyar gonakinsu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wasu manoma a Ƙaramar Hukumar Ɗanja sun nemi gwamnatin Jiihar Katsina da ta biya su diyyar gonakinsu da ta karɓa tsawon shekara biyar. Mai magana da yawun manoman, Shugaba Ɗan'azumi ya faɗi haka a lokacin da yake miƙa takardar koke ga wakilin Sarkin Kudun Katsina hakimin Ɗanja.                                          Manoman da wakilin hakimin Sarkin Fulani Ɗanja Alhaji Yazid Sadiƙ, wakilin manoman ya ce Naira miliyan goma ne adadin kuɗin da gwamnati za ta basu amma har yanzu…
Read More