17
Jul
Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Zuriyar Ibrahim Ahmadu Mai ƙarfe ta gudanar da taron sada zumunci karo na biyar domin ƙarfafa alaƙar zumunci da kuma tattauna hanyoyin tallafa wa marasa galihu daga cikin zuriyar. Shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Sadiƙu Sulaiman Yalwa, ya bayyana cewa taron ya zama wata hanya ta haɗa 'yan uwa da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da suke fuskanta. Ya ce Ibrahim Mai ƙarfe ya shahara da sana'ar ƙira da ɗinkin kayan sarauta a Kano, kuma zuriyarsa na ci gaba da riƙe kyawawan dabi'unsa na taimakon jama'a da kyautata mu'amala. Ya ƙara da cewa zuriyar ta…
