17
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufa’i Sani Hanga, wanda shi ne kaɗai Sanatan NDC daga Jihar Kano, a gidansa da ke Abuja a daren ranar Laraba. Rahotanni sun ce, a cewar mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Umar Saminu Mai-Adashi, ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, inda ɓangarorin biyu suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi siyasar Nijeriya da ci gaban ƙasa. Mai-Adashi ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa tattaunawar ta fi karkata ne kan yadda za a ƙarfafa dimokuraɗiyya, da…
