ukarofi

12546 Posts
Kakakin majalisar dokokin Legas ya gana da shugabannin Arewa Community

Kakakin majalisar dokokin Legas ya gana da shugabannin Arewa Community

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Kakakin majalisar dokokin jihar Legas Mudashiru Ajaiye Obasa ya gana da shugabannin al'ummar Arewa ƴaƴan jam'iyyar APC mazauna Legas reshen Agege ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sa'adu Yusuf Ɗandare Gulma.Da ya ke jawabi, Alhaji Obasa ya nuna jin daɗin sa bisa ga amsa goron gayyatar da ya yi sannan ya bayyana cewa akwai buƙatar a haɗa hannu tare domin a gudu tare a tsira tare.Ya zama wajibi ga dukkan mu da mu natsu mu kalli matsalolin da ke dabaibaye da mu, mu magance su domin samun siyasa mai tsafta duk da bambance-bambancen yare da al'adu da ke…
Read More
Gwamnatin Kano ta fara gyaran matatar ruwan Joda bayan shekaru bakwai ba ta aiki

Gwamnatin Kano ta fara gyaran matatar ruwan Joda bayan shekaru bakwai ba ta aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kwamishinan ma'aikatar albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahiru M. Hashim, ya bayyana cewa an fara aikin gyaran cibiyar samar da ruwan Joda Regional Water Scheme nan take bayan ziyarar duba aikin da aka kai makon da ya gabata. Ya ce cibiyar ba ta samar da ko lita guda na ruwa ba tsawon shekaru bakwai, lamarin da ya sa fara aikin gyaran cikin gaggawa ya zama muhimmin ci gaba. A cewarsa, an riga an gyara rijiyoyin burtsatse guda hudu, kuma yanzu suna aiki tare da cika tankunan ajiyar ruwa guda…
Read More
Dalilina na amincewa da gagarumin garambawul ga hukumar NYSC – Tinubu

Dalilina na amincewa da gagarumin garambawul ga hukumar NYSC – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta amince da gagarumin garambawul ga tsarin Hukumar Yi Wa ƙasa Hidima ta Matasa (NYSC) ne domin bai wa matasan Nijeriya ƙwarewar aiki mai amfani, inganta hidimar ƙasa da kuma shirya su yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ƙasar. An amince da waɗannan sauye-sauyen ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar ranar Litinin. Shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan shi ne mafi girman sauyi da aka taɓa yi wa shirin NYSC tun bayan kafa shi a shekarar 1973, kuma yana…
Read More
CBN ya soke lasisin bankunan bada lamuni 46

CBN ya soke lasisin bankunan bada lamuni 46

Daga MAHDI MISA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya soke lasisin wasu bankunan gudanar da harkokin bayar da lamuni ga ƙananan masu sana'o'i guda 46 a faɗin ƙasar nan, sakamakon gaza cika muhimman ƙa'idojin da hukumar ke shimfiɗawa. A cikin wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Sashen Sadarwar Kamfanoni ta CBN, Malama Hakama Sidi-Ali, ta fitar a ranar Laraba, bankin ya bayyana cewa matakin ya fara aiki nan take. CBN ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa ikon da Sashe na 12 da na 13 na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA), 2020 suka ba ta, bayan gano manyan…
Read More
Mata huɗu da yara biyu sun tsere daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Mata huɗu da yara biyu sun tsere daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mata huɗu da yara biyu sun tsere daga hannun 'yan bindiga bayan sun shafe kwanaki a tsare, inda dakarun Rundunar Sojojin Nijeriya suka ceto su a yankin ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina. A cikin wata sanarwa da kakakin Birged ta 17, Kyaftin Abayomi Adisa, ya fitar, ya ce dakarun rundunar sun gano mutanen a yankin Unguwar Doka a ranar 29 ga Yuni, yayin da suke yawo cikin daji bayan sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane. Binciken farko ya nuna cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da su ne daga Unguwar…
Read More
Sarautar Sarkin Arewa da Sarkin Kano ya ba ni alamar ƙauna ce – Alhaji Dahiru Giɗaɗo

Sarautar Sarkin Arewa da Sarkin Kano ya ba ni alamar ƙauna ce – Alhaji Dahiru Giɗaɗo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sabon Sarkin Arewa na Masarautar Kano, Alhaji Dahiru Sa'idu Gidado, ya bayyana cewa naɗin sarautar da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya yi masa alama ce ta ƙauna, amana da kuma girmamawa. Alhaji Dahiru Gidado ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai bayan karɓar sarautar, inda ya nuna matuƙar godiyarsa ga Sarkin Kano bisa amincewar da ya yi da shi. Ya ce, "Wannan naɗi babbar ƙauna ce da aka nuna mini. Ina addu'ar Allah Ya saka wa Mai Martaba Sarki da alheri, Ya biya masa buƙatunsa, Ya ƙara masa lafiya,…
Read More
Abba Kabir ba ya nuna ƙabilanci wajen tafiyar da mulki – Tsohon Kansila

Abba Kabir ba ya nuna ƙabilanci wajen tafiyar da mulki – Tsohon Kansila

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Tsohon Kansilan unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano, Hon. Chief Fredrick Ilele, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ba ya nuna ƙabilanci ko wariya wajen tafiyar da mulkinsa. Ilele ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce salon shugabancin gwamnan ya sa jama'a daga kabilu daban-daban ke ci gaba da ba shi goyon baya. Ya ce irin wannan tsarin shugabanci ya kuma taimaka wajen ƙara karɓuwa da bunƙasar jam'iyyar a ƙaramar hukumar Fagge da sauran sassan jihar. Tsohon kansilan ya bayyana ƙwarin…
Read More
Kotu ta tabbatar da shugabancin David Mark a ADC

Kotu ta tabbatar da shugabancin David Mark a ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC tare da yin watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, da ya ƙalubalanci naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar na ƙasa. Mai shari'a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam'iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam'iyyar ba kafin ya garzaya kotu. Kotun…
Read More
Gidauniyar Gidan Alheri ta cire mutum huɗu daga kurkuku a Gombe

Gidauniyar Gidan Alheri ta cire mutum huɗu daga kurkuku a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe ƙungiyar jin ƙai ta Gidan Alheri/Dangin Juna Afirka ta taimaka wajen fitar da mutum huɗu daga Gidan Gyaran Hali na Jihar Gombe bayan ta biya musu tarar kuɗi da diyya da kotu ta ɗora a kansu. Waɗanda aka taimaka wa sun haɗa da matasa uku da mace ɗaya, waɗanda suka ci gaba da zama a gidan gyaran hali duk da hukuncin da aka yanke musu, sakamakon rashin ikon biyan tarar da diyya. An gudanar da wannan aiki ne yayin wata ziyara da tawagar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Sagir A.A. Haruna, ta kai Gidan…
Read More
Dole Nijeriya ta kauce wa sake faɗa wa yaƙin basasa – Obasanjo

Dole Nijeriya ta kauce wa sake faɗa wa yaƙin basasa – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce wajibi ne Nijeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kauce wa sake faɗawa yaƙin basasa, yana mai gargaɗin cewa ƙasar ba za ta iya jure wani irin rikici makamancin na 1967 zuwa 1970 ba. Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abeokuta yayin ƙaddamar da wani littafi da Chuck Nduka-Eze ya rubuta kan kisan gillar Asaba da abubuwan da suka shafi yaƙin basasa. Ya ce har yanzu wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa yaƙin basasa suna nan, don haka dole ne a koyi darasi daga tarihi tare…
Read More