03
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya fi duk wani shugaban ƙasar da ya gabata aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a yankin Arewa, yana mai cewa manyan zuba jari a fannonin ababen more rayuwa, noma da lafiya sun tabbatar da ƙudirin gwamnatin wajen bunƙasa yankin. Gwamnan ya kuma yi watsi da ra'ayin da ke cewa Arewa ba za ta goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2027 ba, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasar zai samu ƙuri'u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen shugaban…
