02
Jul
Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya sha alwashin yi wa Fulanin da aikin hanya ya taɓa burtalin su adalci kamar yadda doka ta tanada.Ya yi wannan bayanin ne ranar Larabar nan bayan da waɗansu fulani suka yi ƙorafi a kan wani aikin hanya da ta haɗa ƙauyen Gidan-koni da babbar hanyar da ta haɗa ƙaramar hukumar mulki ta Augie zuwa jihar Sokoto ya taɓa burtalin su. Honarabul Yahaya Augie ya nemi Fulanin da su kwantar da hankalin su ba za a bari wani ƙaramin abu ya zo ya ɓata daɗaɗɗiyar dangantakar da…
