12
Jun
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwarta kan ci gaba da hare-hare, cin zarafi da tsoratar da ’yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu ke fuskanta, tana mai bayyana cewa tana nazarin yiwuwar ɗaukar matakan martani kan lamarin. Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin da take ganawa da wakilan kafafen yaɗa labarai a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. Ta ce duk da cewa gwamnatin na duba yiwuwar ɗaukar matakan ramuwar gayya, duk wata matsaya ta ƙarshe za ta buƙaci tattaunawa da amincewa daga manyan hukumomin gwamnati, ciki har da…
