ukarofi

12550 Posts
HJRBDA, Bichi da cikar shekaru uku na manhajar Sabon Fata ta Tinubu kan tsaron abinci

HJRBDA, Bichi da cikar shekaru uku na manhajar Sabon Fata ta Tinubu kan tsaron abinci

Daga: SHEHU MUSTAPHA CHAJI Hukumar raya kogunan Hadejia Jama'are (HJRBDA) ƙarƙashin jagorancin Injiniya Dakta Rabiu Suleiman Bichi tana da mafi girman tsarin ban-ruwa mai aiki a cikin hukumomin raya koguna 12 na Najeriya. Tun bayan hawansa mulki tare da manyan jami'ansa irin su Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, Daraktan Kuɗi da Gudanarwa, Bichi ya sha bayyana cewa sauye-sauyen da yake yi a HJRBDA sun yi daidai da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope Agenda, musamman a fannin tsaron abinci. Yayin da 'yan Nijeriya ke bikin cikar shekaru 3 na gyare-gyare ƙarƙashin Renewed Hope Agenda, HJRBDA ƙarƙashin Rabiu Suleiman Bichi…
Read More
Gwamnatin Nasarawa ta ƙaryata zargin Maku kan shirin maguɗin zaɓe

Gwamnatin Nasarawa ta ƙaryata zargin Maku kan shirin maguɗin zaɓe

Daga JOHN D WADA a Lafia Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana zargin da ɗan takarar kujerar sanata a Nasarawa ta Arewa a jam’iyyar Labour Party Labaran Maku ya yi kan shirin jam'iyya mai ci a jihar na tafka maguɗin zaɓe a matsayin mara tushe. Babban mataimakin gwamnan kan harkokin jama’a Hon. Peter Ahemba ne ya faɗi haka yau Juma’a a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar NUJ dake Lafia babban birnin jihar. Idan za a iya tunawa Labaran Maku wanda tsohon mataimakin gwamna ne kuma tsohon ministan yaɗa labarai ya bayyana a ranar Laraba a Akpata na ƙaramar…
Read More
Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Raɗɗa ya yaba wa jajurtattun dimokuraɗiyya

Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Raɗɗa ya yaba wa jajurtattun dimokuraɗiyya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al'ummar Jihar Katsina da ɗaukacin 'yan Najeriya murnar cika shekaru 27 da ranar dimokuraɗiyya ta ƙasa. Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa ranar 12 ga Yuni rana ce mai muhimmanci da ke nuna ƙudurin al'ummar Najeriya na zaɓar 'yanci, adalci da mulkin dimokuraɗiyya fiye da komai. Ya ce ranar tana tunatar da mu irin sadaukarwar da aka yi domin Najeriya ta tsaya a kan ginshiƙin dimokuraɗiyya da take morewa a yau. Gwamnan ya yi gagarumar karramawa ga fitattun 'ya'yan Jihar Katsina waɗanda gudummawar da suka bayar a…
Read More
Hanyoyin Gwamnatin Tarayya a Katsina sun yi mummunar lalacewa – Kwamred Suleiman

Hanyoyin Gwamnatin Tarayya a Katsina sun yi mummunar lalacewa – Kwamred Suleiman

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua Kwamred Mannir Suleiman ya koka a kan yadda hanyoyi mallakar gwamnatin tarayya su kayi mummunar lalacewa a jihar katsina. A hira da yayi da manema labarai a katsina Kwamred Suleiman ya ce idan har gwamnatin tarayya ba ta kammala wasu aikin hanyoyi a jihar ba ta zirga zirga tsakanin jihar katsina da makwabtan ta zai tsaya cik. Ya bada misali da hanyar Katsina zuwa Kano da Gidan Mutum Ɗaya zuwa Katsina da aka bada aikin hanyar a shekarun baya amma har ya zuwa yanzu babu wani bayani game da cigaban aikin…
Read More

Ranar Dimukraɗiyya: Inuwa ya ce cigaban Gombe shaida ce ta ribar dimukraɗiyya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce gagarumin ci gaban da aka samu a jihar cikin shekaru da suka gabata shaida ce ta ribar dimokuraɗiyya da kuma amfanin shugabanci mai ɗaukar al'umma a matsayin ginshiƙi tare da riƙon amana. A saƙonsa na taya murnar ranar dimokuraɗiyya da ya fitar a ranar Juma'a, gwamnan wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF), ya taya shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗaukacin 'yan Najeriya murnar cika shekaru 27 ana gudanar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da tangarɗa ba. Ya bayyana dimokuraɗiyya a matsayin hanya…
Read More
Atiku shi ne mafitar ƙasar nan — Hajiya Humaira Kano

Atiku shi ne mafitar ƙasar nan — Hajiya Humaira Kano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar (Turakin Adamawa), a matsayin wanda kaɗai zai iya fitar da Nijeriya daga halin da take ciki a yanzu. Shugabar matan jam’iyyar ADC a Jihar Kano kuma shugabar ƙungiyar Atiku Network Initiatives, Hajiya Aisha Ibrahim Hassan, wadda aka fi sani da Humairan Kano, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a taron gangamin haɗin kan ‘yan jam’iyyar ADC da ta shirya, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Gidauniyar Kano a ranar Asabar da ta gabata. Ta ce ta shirya taron…
Read More
Tsangwama: An dawo da ’yan Nijeriya 270 gida daga Afirka ta Kudu

Tsangwama: An dawo da ’yan Nijeriya 270 gida daga Afirka ta Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta karɓi ’yan Nijeriya 270 da suka dawo daga Afirka ta Kudu. Waɗanda suka dawo sun shiga shirin komawa gida da kansu. NEMA ta ce sun yi rajista tare da kammala dukkanin gwaje-gwaje da ake buƙata kafin su dawo. Sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Alhamis. Jami’an NEMA, sauran hukumomin gwamnati sun tarbi waɗanda suka dawo, tare da taimaka musu wajen komawa cikin al’umma. Gwamnati ta kuma shirya motocin da za su kai su zuwa wuraren…
Read More
Tinubu ya yi alƙawarin mai da Abuja katafaren birni daidai da manyan birane na duniya

Tinubu ya yi alƙawarin mai da Abuja katafaren birni daidai da manyan birane na duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Tinubu ya ce zai buƙasa Babban Birnin Tarayya (FCT) ta yadda zai zama babban birni mai yawan al’umma da tattalin arziki da ɗaga martabar ƙasa nan bakiɗaya. Shugaba Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin ƙaddamar da aikin Titin Arterial Road N5 (Obafemi Awolowo Way), daga mahaɗar Life Camp zuwa Ring Road III da ke yankin Dape. Ya ce inganta hanyoyin sufuri a Abuja zai rage kuɗaɗen jigilar kayayyaki da ƙara jawo masu zuba jari tare da samar da guraben ayyukan…
Read More
‘Yan sanda sun ceto matafiya biyar da aka sace a Zamfara

‘Yan sanda sun ceto matafiya biyar da aka sace a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce ta ceto matafiya biyar da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da su a kan hanyar Anka zuwa Bukkuyum. Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce jami’an Sashen Yaki da Manyan Laifuka ne suka kai dauki cikin gaggawa bayan faruwar lamarin. A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar 10 ga watan Yuni, lokacin da wasu dauke da makamai suka tare hanyar tare…
Read More
Rasuwar Marigayi Dandama Yabo ta girgiza al’ummar Legas

Rasuwar Marigayi Dandama Yabo ta girgiza al’ummar Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas, Alhaji Mohammed Dandamma Yabo, ta jefa al’umma cikin jimami da alhini. Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadin makon da ya gabata a mahaifarsa ta Jihar Sakkwato bayan fama da jinya. Kafin rasuwarsa, Alhaji Mohammed ɗandamma Yabo shi ne babban shugaban kasuwar sayar da doya ta Mile 12 da ke Legas. Haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar al’ummar Arewa (Northern Community) a Jihar Legas. Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, ya bar mata biyu, ’ya’ya takwas, maza biyar…
Read More