ukarofi

12550 Posts
Ana iya fuskantar tashin hankali a zaɓen 2027 — Manazarta Taurari

Ana iya fuskantar tashin hankali a zaɓen 2027 — Manazarta Taurari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Malam Falaki Network of Africa (FNA), wadda ta haɗa masu nazarin taurari da wasu malaman addini, ta yi hasashen cewa babban zaɓen Nijeriya na shekarar 2027 na iya fuskantar tashe-tashen hankali, yaɗuwar bayanan ƙarya da rikice-rikicen siyasa. Shugaban ƙungiyar, Imam Habib Abdulkarim Assufiyyu, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Talata. A cewarsa, nazarin da ƙungiyar ta gudanar ya nuna akwai buƙatar a dage da addu’o’i da neman taimakon Allah kafin da lokacin gudanar da zaɓukan da aka tsara yi a shekarar 2027. Ya ce…
Read More
An kama matar auren da ta kitsa garkuwa da kanta a Delta

An kama matar auren da ta kitsa garkuwa da kanta a Delta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  An kama wata matar aure mai suna Oluchi, wadda ta kitsa garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa a wurin ’yan uwanta. Manhaja ta ruwaito cewa an dai gano matar ce tare da wani mutum da ake zargin saurayinta ne a ɗakin wani otel da ke Jihar Delta. Wannan dai na zuwa ne bayan da ’yan uwa da abokan arziki suka fara tara gudunmawar kuɗin fansa domin ceto ta, yayin da ta bayyana a gare su cewa waɗanda suka yi garkuwa da ita suna nema a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin…
Read More
An ga wani babban jami’in kwastom a mace a Jihar Bauchi

An ga wani babban jami’in kwastom a mace a Jihar Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani babban jami’in hukumar kwastom ta Nijeriya, Mista Lumi Elisha Gwamis, ya rasu, lamarin da ya jefa al’ummar gundumar Boi da ke ƙaramar Hukumar Bogoro a jihar Bauchi cikin jimami. Marigayin, wanda shi ne babban ɗan tsohon shugaban karamar hukumar Bogoro, Alhaji Elisha Tula Gwamis, ya rasu yana da shekara 44 a duniya. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun ce marigayin ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya da damuwa kafin rasuwarsa. Sai dai har yanzu babu wata hukuma da ta tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar tasa. Yayin…
Read More
Rasuwar Audu Manaja babban rashi ne ga Arewa da Nijeriya — Sulaiman Hussain

Rasuwar Audu Manaja babban rashi ne ga Arewa da Nijeriya — Sulaiman Hussain

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Janar Manajan Kamfanin Audu Manaja, Alhaji Sulaiman Hussain, ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin mai harkar man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad (Audu Manaja), a matsayin babban rashi ga al’ummar Arewa da Nijeriya baki ɗaya. Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Sulaiman Hussain ya ce marigayin mutum ne mai nagarta, gaskiya da riƙon amana, wanda ya yi fice wajen kyakkyawar mu’amala da jama’a a harkokin kasuwanci da zamantakewa. Ya ce marigayin ya kasance mutum mai cika alƙawari da yafiya, yana kuma kula da ma’aikatansa kamar ’ya’yansa na jini. “Duk wanda ya san Audu…
Read More
Ranar Dimukraɗiyya: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya ta kowa da kowa – Idris

Ranar Dimukraɗiyya: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya ta kowa da kowa – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar gina Nijeriya mai ƙwari, wadda ta haɗa kowa da kowa, kuma mai wadata, inji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris. Ya faɗi haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron manema labarai da aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026. Idris ya ce, “Bikin Ranar Dimokiraɗiyya na wannan shekarar yana da muhimmanci ta musamman domin ya zo daidai da cikar shekara uku na gwamnatin Sabunta Fata. Wannan dama ce ta yin bitar irin cigaban da ƙasa ta…
Read More
Kotu ta haramta wa Majalisr Dokokin Nijeriya kashe biliyan N110 na sayen motocin SUV

Kotu ta haramta wa Majalisr Dokokin Nijeriya kashe biliyan N110 na sayen motocin SUV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Kotun Tarayya da ke Legas ta bayyana cewa yunƙurin da Majalisar Dokokin Nijeriya ke yi na sayen motocin da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 110 da wasu alawus-alawus ya saɓa wa ƙa’idar sayen kayayyaki na gwamnati da tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da yardar al’umma. A cikin jawabin da cibiyar kare haƙƙin al’umma da tattalin arziƙi da ayyukan gwamanati (SERAP) ta raba wa manema labarai, ta ce, mai shari’a Yellim Bogoro ya bayyana cewa shirin kashe Naira 40 kan sayen motoci 465 ga ‘yan majalisar tarayya da tallafin Naira biliyan 70 a matsayin…
Read More
Gini kan magudanan ruwa na kawo ambaliya – Sarkin Ibo na Hausawan Afirka

Gini kan magudanan ruwa na kawo ambaliya – Sarkin Ibo na Hausawan Afirka

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Sarkin Ibo na Hausawan Afirka, Ambasada (Dakta) David N. Onwere, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya da su guji gina gine-gine akan magudanan ruwa, yana mai cewa,  yin hakan na haddasa matsalolin muhalli da kuma ambaliyar ruwa. Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan karɓar gaisuwar Babbar Sallah daga al’ummar Musulmi a fadarsa da ke unguwar Nomansland a Kano. Sarkin ya kuma buƙaci jama’a su rika tsaftace magudanan ruwa tare da guje wa zubar da shara a cikinsu domin rage hadarin ambaliya da kare muhalli. Ya…
Read More
Gyaran tsarin shari’a: NBA Gombe ta fara makon lauyoyi da addu’o’i na musamman

Gyaran tsarin shari’a: NBA Gombe ta fara makon lauyoyi da addu’o’i na musamman

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta fara gudanar da makon lauyoyi na shekarar 2026 da addu'o'in na musamman, inda ta buƙaci a ƙara inganta tsarin shari'a domin tabbatar da cewa adalci ya isa ga kowane ɗan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba. An fara shirye-shiryen makon ne da addu'ar Musulmi da aka gudanar a masallacin Juma'a na Modibbo Bubayero da ke Gombe, inda lauyoyi, alƙalai da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara domin neman taimako da shiriyar Allah wajen samun nasarar shirye-shiryen da aka tanada. Da yake jawabi bayan addu'ar,…
Read More
Zargin muzanta marasa ƙarfi a ɓangaren shari’a ya girgiza al’ummar Kano

Zargin muzanta marasa ƙarfi a ɓangaren shari’a ya girgiza al’ummar Kano

Daga MUSA AHMAD Ƙorafin tsare yarinya ta hanyar nuna ɓangaranci sa shirin jefa alƙalin hisba cikin tsaka mai wuya KANO – Zarge-zargen rashin adalci da nuna son rai sun mamaye al’umma bayan ɓullar ƙorafe-ƙorafen da ke alaƙanta wani alƙalin hukumar Hisba, Sani Tanimu, da abin da masu ƙorafi suka bayyana a matsayin tauye haƙƙin wata yarinya marar gata. Lamarin ya janyo cece-kuce, inda jama’a ke kira ga mahukunta su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru. Rahotanni sun nuna cewa tunda farko rikici ne ya ɓarke tsakanin wasu mata biyu, lamarin da ya kai ga shigar da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bada aikin fidda magudanan ruwa a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya bada aikin fidda magudanan ruwa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina cikin gaggawa ya amshi ƙorafin al'ummar Barhim, har ya bada umarnin fidda magudanan ruwa a bisa sabon aikin tagwayen hanyoyi daga Barhim zuwa sabuwar hanyar "Estern Bye Pass". Bayan ganin ƙorafin al'ummar Barhim da ke cikin ƙaramar hukumar Batagarawaa Jihar Katsina, na ambaliyar ruwa sanadiyar rashin magudanan ruwa akan aikin tagwayen hanyoyi da tsara unguwar Barhim. Cikin gaggawa gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi umarnin fidda magudanan ruwa akan aikin tagwayen hanyoyin domin kare al'ummar Barhim daga ibtala'in ambaliyar ruwa duba da yanayin damina da aka shiga. Ruwan sama…
Read More