ukarofi

12556 Posts
Bichi ta zama abin koyi wajen raba tallafin Naira 50,000 ga mata ƙarƙashin shirin gwamnan Kano

Bichi ta zama abin koyi wajen raba tallafin Naira 50,000 ga mata ƙarƙashin shirin gwamnan Kano

Ƙaramar hukumar Bichi ta samu yabo daga kwamitin kula da ingancin ayyukan gwamnati (CRC) na jihar Kano bisa yadda ta gudanar da rabon tallafin jarin naira dubu 50 ga mata a yankin kamar yadda jami'ar yaɗa labarai Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar.Shirin na daga cikin manufofin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na ƙarfafa tattalin arzikin mata a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano. Yabon ya fito ne daga bakin sakataren tsare-tsare na kwamitin, Malam Tijjani Ali Bichi, wanda ya wakilci shugaban CRC na jiha, Alhaji Usman A. Gezawa, bayan kammala rabon tallafin ga mata 80 a yankin a…
Read More
IGP Disu ya gargadi jama’a kan ɗaukar bidiyon ‘yan sanda a bakin aiki don soshiyal midiya

IGP Disu ya gargadi jama’a kan ɗaukar bidiyon ‘yan sanda a bakin aiki don soshiyal midiya

Daga USMAN KAROFI Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya gargadi jama'a da masu ƙirƙirar kafafen sada zumunta da su guji ɗaukar bidiyon jami'an 'yan sanda yayin da suke bakin aiki. Ya bayyana cewa amfani da irin waɗannan bidiyoyi ba tare da kulawa ba na iya rage ƙwarin gwiwar jami'ai tare da kawo cikas ga ayyukan tsaro. Da yake jawabi a wata ganawa da mambobin Crime Correspondents Association of Nigeria a Abuja, Disu ya jaddada ƙudirin rundunar 'yan sanda na tabbatar da gaskiya, rikon amana, ƙwarewa da mutunta haƙƙin ɗan Adam. Sai dai ya ce akwai buƙatar a…
Read More
Kisan ɗalibar jinya Wendy Achumba ya janyo cece-kuce kan cin zarafin mata

Kisan ɗalibar jinya Wendy Achumba ya janyo cece-kuce kan cin zarafin mata

Daga USMAN KAROFI Mutuwar Wendy Achumba mai shekaru 21, ɗalibar makarantar koyon aikin jinya ta Our Lady Nursing School da ke Umulogho a ƙaramar hukumar Obowo ta jihar Imo, ta haifar da fushi da alhini a tsakanin al'umma. Rahotanni sun nuna cewa an kashe ta ne bayan ta ki amincewa da soyayyar wani matashi da ake zargi da aikata laifin tare da wani abokinsa. An ce Wendy, wadda ke karatun zama ungozoma, tana zaune ita kadai a gidansu a lokacin da lamarin ya faru, bayan abokan zamanta sun tafi aikin horaswa a asibitoci. Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin…
Read More
Gwamna Ahmed Aliyu ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar MD na ZBCC a Zuru

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar MD na ZBCC a Zuru

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Zuru, Sanusi Muhammad Mika'ilu, bisa rasuwar Hajiya Hajara Hussaini, wadda aka fi sani da Innar Manir, mahaifiyar manajan daraktan kamfanin Zuru Building and Construction Company (ZBCC), Alhaji Adamu Hussaini. Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyali da kuma al'ummar Jihar Kebbi baki ɗaya. A yayin ziyarar, Gwamna Aliyu ya yi addu'ar Allah Ya jikanta da rahama, ya sanya ta aljannatul firdausi, tare da bai wa iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi. Ya tunatar da mahalarta cewa mutuwa hakki ce ga kowane rai, don…
Read More
Majalisar Dokokin Ghana ta amince da dokar hana auren jinsi

Majalisar Dokokin Ghana ta amince da dokar hana auren jinsi

Daga USMAN KAROFI Majalisar Dokokin ƙasar Ghana ta amince da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce wadda ke haramta ayyukan auren jinsi (LGBTQ+) tare da ƙara tsaurara hukunci kan masu alaƙa da irin waɗannan halaye. Dokar ta tanadi ɗaurin shekaru har uku a gidan yari ga mutanen da aka bayyana a matsayin masu alaƙa da LGBTQ+, sannan ta wajabta wa jama'a kai rahoton irin waɗannan ayyuka ga hukumomin tsaro. A cewar masu goyon bayan dokar, matakin yana da nufin kare al'adu da kimar iyali ta al'ummar Ghana. Sun bayyana cewa dokar za ta ƙarfafa aiwatar da dokokin da ake da…
Read More
‘Yan bindiga sun sace Janar Rabe Abubakar da matarsa rana-tsaka a Katsina

‘Yan bindiga sun sace Janar Rabe Abubakar da matarsa rana-tsaka a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga sun sace tare da garkuwa da tsohon daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin Najeriya Manjo Janaral Rabe Abubakar da mai ɗakin sa a garin Matazu bisa kan hanyar na zuwa Katsina. Sai dai direban sa ya tsira da rauni a jikin sa bayan harbin bindida daga maharan, kamar yadda Birgediya Janaral Sagir Musa mai Ritaya ya fitar da sanarwa cewa yanzu haka motar shi Janaral Rabe ƙirar Peugeot 504 mai kalan ja na nan ajiye a ofishin 'yan sanda na garin Matazu. Janaral Rabe Abubakar ɗan asalin ƙaramar hukumar Batsari na kan hanyar…
Read More
An karrama ministan tsaro da lambar girma ta Kudancin Kaduna

An karrama ministan tsaro da lambar girma ta Kudancin Kaduna

Daga USMAN KAROFI Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama ministan tsaro na Najeriya, Christopher Gwabin Musa, da lambar yabo ta Grand Commander of Southern Kaduna (GCSK) bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa. An gudanar da bikin karramawar ne tare da halartar sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, wakilan al’umma, ƙungiyoyin matasa da na addinai, da sauran jama’ar Kudancin Kaduna. Yayin karɓar lambar yabon, Janar Musa ya gode wa al’ummar yankin bisa wannan girmamawa, yana mai bayyana Kudancin Kaduna a matsayin yanki mai albarka da ɗimbin damar ci gaba. Ministan ya sadaukar da lambar yabon…
Read More
Nijeriya ta sake lashe Unity Cup bayan doke Jamaica da ci uku da nema

Nijeriya ta sake lashe Unity Cup bayan doke Jamaica da ci uku da nema

Daga USMAN KAROFI Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta samu nasarar kare kambunta na Unity Cup bayan da ta lallasa Jamaica National Football Team da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na The Valley Stadium. Najeriya ta fara wasan cikin ƙarfi, inda ɗan wasan tsakiya Alhassan Yusuf ya zura ƙwallon farko tun a minti na uku da fara wasa. Ƙwallon ta bai wa Super Eagles damar mamaye wasan tun daga farkonsa tare da nuna ƙwarewa da tsari a ƙarƙashin jagorancin mai horarwa Eric Chelle. A karo na biyu na wasan, kyaftin ɗin tawagar kuma ɗan…
Read More
Obi ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na NDC

Obi ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na NDC

Daga USMAN KAROFI Ɗan siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓen shekarar 2027. Yayin karɓar tutar takarar a Abuja, Obi ya bayyana cewa Najeriya ba ta da wani dalili na kasancewa cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa a duniya, yana mai jaddada cewa “Sabuwar Najeriya mai kyau mai yuwa ce.” Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, samar da ayyukan yi, magance matsalar tsaro da kuma bunƙasa harkokin noma domin kawo ƙarshen yunwa. Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za…
Read More
Amaechi da Hayatudeen sun yi watsi da sakamakon zaɓen ADC

Amaechi da Hayatudeen sun yi watsi da sakamakon zaɓen ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan takarar neman shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC, Mohammed Hayatudeen da Rotimi Amaechi, sun bayyana rashin amincewarsu da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda suka yi zargin cewa an tafka maguɗi da kura-kurai a kusan duka sassan ƙasar. Korafin nasu na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar domin tantance wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a babban zaɓen 2027. Mohammed Hayatudeen, shi ne ya fara bayyana rashin amincewarsa da yadda aka gudanar da zaɓen. A wata…
Read More