ukarofi

12556 Posts
Rasuwar Wasila Isma’il: Tarihin jarumar da ta zama ɗaya daga cikin ginshiƙan Kannywood 

Rasuwar Wasila Isma’il: Tarihin jarumar da ta zama ɗaya daga cikin ginshiƙan Kannywood 

Daga AISHA ASAS  Masana’antar fina-finan Hausa ta shiga cikin yanayi na jimami da alhini bayan rasuwar tsohuwar jaruma Wasila Isma'il, wadda ta kasance cikin taurarin farko da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa tubalin da masana’antar Kannywood ta tsaya a kai a yau. Rasuwarta ba wai mutuwar jaruma kaɗai ba ce, tamkar rufe wani babi ne na tarihin tsohuwar Kannywood da mutane da dama suka taso suna kallo. An bayyana cewa, jarumar ta rasu tana da shekaru 46 bayan fama da jinya, lamarin da ya jefa masoyanta da abokan sana’a cikin jimami. Wacce ce Wasila Isma’il? An haifi Wasila Isma’il…
Read More
’Yan sanda sun jikkata bayan wata mata ta sakar musu ƙudan zuma

’Yan sanda sun jikkata bayan wata mata ta sakar musu ƙudan zuma

A ƙasar Amurka, an shiga ruɗani bayan wata mata mai shekara 59 ta saki tarin ƙudan zuma kan jami’an ’yan sanda da suka je aiwatar da umarnin korar wani tsoho daga gidansa, lamarin da ya jawo jikkatar wasu daga cikin jami’an. Rahotanni daga hukumomin yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an tsaro suka isa gidan domin aiwatar da umarnin kotu na fitar da wani dattijo da ake zargin an ƙwace masa haya ko kuma ya kasa biyan kuɗin zama. Sai dai jim kaɗan bayan jami’an sun fara aiwatar da aikin, matar da ake zargin tana…
Read More
Tsadar gas ta tilasta wa talakawa amfani da itace da gawayi

Tsadar gas ta tilasta wa talakawa amfani da itace da gawayi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Masu Kasuwancin Iskar Gas Ta Nijeriya (NALPGAM), ta bayyana damuwa kan ƙarancin iskar gas ta girki da kuma tashin farashinta a sassa daban-daban na ƙasar nan. ƙungiyar ta ce, farashin gas ɗin ya tashi daga kusan naira 1,300 zuwa fiye da naira 1,500 kan kowanne kilo, gwargwadon yankin da ake saye. A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, ta jawo hankalin Gwamnatin Tarayya, hukumomin gwamnati, masu kula da harkokin makamashi, masu shigo da gas, masu samar da shi, masu ajiyar gas a tankuna da kuma jama’a baki ɗaya kan abin da…
Read More
Arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.89 a farkon 2026, inji NBS

Arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.89 a farkon 2026, inji NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu bunƙasa da kashi 3.89 cikin ɗari a farkon shekarar 2026 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahoton GDP na farkon shekarar 2026 da ta fitar ranar Litinin, 25 ga watan Mayu. A cewar NBS, wannan ci gaba ya zarce kashi 3.13 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2025, sai dai ya yi ƙasa da kashi 4.07 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2025. Hukumar ta ce ɓangaren noma ya samu bunƙasa…
Read More
Nijeriya da Turkiyya sun ƙulla yarjejeniya kan haɓaka harkar ma’adanai

Nijeriya da Turkiyya sun ƙulla yarjejeniya kan haɓaka harkar ma’adanai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatocin Nijeriya da Turkiyya sun rattaba hannu kan wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) domin ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangaren ma’adanai masu ƙarfi, a wani yunƙuri na bunƙasa alaƙar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu. An sanya hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin Ministan Raya Ma’adanai Masu ƙarfi na Nijeriya, Dele Alake, da Ministan Makamashi da Albarkatun ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar, a gefen Taron Albarkatun ƙasa na Istanbul (INRES). A cikin wata sanarwa da Mataimakiyarsa ta Musamman, Lara Owoeye-Wise, ta fitar ranar Litinin, Alake ya bayyana cewa Nijeriya na shirye ta yi amfani da ci gaban fasaha da…
Read More
Farashin abincin mai inganci ya kai N1,513 a kullum – NBS

Farashin abincin mai inganci ya kai N1,513 a kullum – NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin kuɗin da mutum guda zai kashe domin samun ingantaccen abinci mai gina jiki a rana ya kai naira 1,513 a watan Fabrairun 2026. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na “Cost of a Healthy Diet (CoHD)” na watan Fabrairu da aka fitar a Abuja. A cewar NBS, wannan adadi ya nuna ƙarin kashi 3.76 cikin ɗari idan aka kwatanta da naira 1,458 da aka samu a watan Janairun 2026. Hukumar ta bayyana cewa ma’aunin CoHD na nufin mafi ƙarancin haɗin nau’ikan abinci da ake samu a…
Read More
Kotu ta hana Mamuda Beverages samar da Pop Power saboda tambarin Fearless

Kotu ta hana Mamuda Beverages samar da Pop Power saboda tambarin Fearless

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited ci gaba da samar da abin sha mai ƙara kuzari na ‘Pop Power’, bayan da kamfanin Rite Foods ya zargi kamfanin da kwaikwayon tambarin kayansa na ‘Fearless Energy Drink.’ Mai shari’a Justice Binta Nyako ce ta bayar da umarnin na wucin-gadi bayan ta yanke hukuncin cewa tsarin kwalin da tambarin Pop Power ke amfani da shi na da kamanceceniya sosai da na ‘Fearless’. Kotun ta bayar da umarnin dakatar da samar da kayan nan take har sai an kammala sauraron shari’ar…
Read More
Wajibi ne jaddawalin INEC ya yi daidai da tanadin dokar zaɓe – Kotu

Wajibi ne jaddawalin INEC ya yi daidai da tanadin dokar zaɓe – Kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa wajibi ne jadawalin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ke fitarwa ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026. Kotun ta kuma tabbatar da cewa INEC na da ikon tsara jadawalin gudanar da zaɓe da kuma yin gyare-gyare a kansa idan buƙatar hakan ta taso, amma dole ne duk wani jadawalin ya kasance cikin iyakokin da dokar zaɓe ta shimfiɗa. Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin yayin sauraron ƙarar da jam’iyyar SDP ta shigar kan INEC, inda jam’iyyar…
Read More
PDP: Saleh zai ƙalubalanci bai wa Pantami takarar gwamnan Gombe a kotu

PDP: Saleh zai ƙalubalanci bai wa Pantami takarar gwamnan Gombe a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Gombe kuma mai neman tikitin takarar gwamna, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya bayyana aniyarsa ta ƙalubalantar matakin bai wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tikitin takarar gwamna a kotu. Hamma Saleh ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Gombe, inda ya ce ba zai amince da abin da ya kira rashin bin ƙa’ida da tauye haƙƙin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ba. Ya ce shi da sauran masu neman tikitin gwamna sun shafe shekaru suna bautawa jam’iyyar…
Read More
PDP ta tsayar da Sandy Onor takarar shugaban ƙasa a 2027

PDP ta tsayar da Sandy Onor takarar shugaban ƙasa a 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsagin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike da Abdurrahman Mohammed ya ayyana tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Sandy Onor, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a Zaɓen 2027 bayan masalahar da aka gudanar. Tsohon gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani, ya sanar da hakan yayin tattara sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar Talata a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja. Kwamitin zaɓen ya ce an gudanar da zaɓen ne ta hanyar tuntuɓa da kuma masalahar goyon baya daga mambobin jam’iyyar a…
Read More