ukarofi

12556 Posts
Yadda Masarautar Sarkin Sha-sha ta gudanar da taron addu’o’in neman ƙarin zaman lafiya

Yadda Masarautar Sarkin Sha-sha ta gudanar da taron addu’o’in neman ƙarin zaman lafiya

Daga DAUDA USMAN e Legas A ranar Lahadin da ta gabata ne Masarautar Mai Martaba Sarkin Al’ummar Hausawa mazauna garin Sha-Sha da ke ƙaramar hukumar Alimosho a cikin birnin Ikko, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Hausawan Sha-Sha, Dakta Alhaji Iliyasu Isa Kira, ɗan asalin ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina kuma mazaunin Legas, wanda kuma shi ne Wamban Jikamshi na jihar Katsina, ta gudanar da babban taron walimar addu’o’i na musamman domin neman Allah Ubangiji Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya. Haka kuma, taron ya zo daidai da bikin cika shekaru goma sha biyu cif na…
Read More
KDIN ta gudanar da taron horaswa domin bunƙasa kasuwanci na fasaha a Kano

KDIN ta gudanar da taron horaswa domin bunƙasa kasuwanci na fasaha a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Cibiyar Kano Digital Innovation Network (KDIN) ta shirya wani taron horaswa na kwanaki biyu domin ƙarfafa sabbin kamfanonin fasaha (startups) da ƙanana da matsakaitan sana’o’i ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, ingantacciyar tsari da bunƙasa harkokin kasuwanci mai ɗorewa. Taron mai taken “Bita, Haɗin Kai da Tsare-tsaren Aiki Domin Samar da ƙirƙire-ƙirƙire da ya Haɗa Kowa,” ya haɗa da masu kafa sabbin kamfanoni, cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a fannin domin tattauna ƙalubalen da ke addabar harkokin kasuwanci tare da samar da mafita masu amfani. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban KDIN, Abdulsalam…
Read More
AFAN ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin kayan aikin noma

AFAN ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin kayan aikin noma

Daga WAKILINMU Kungiyar Manoma ta ƙasa, wato AFAN, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙoƙarin rage kuɗin kayan aikin gona domin manoman ƙasar nan su samu damar bunƙasa sana’ar noma cikin nasara. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Magaji Gettado, shi ne ya yi wannan roƙo yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa idan aka samar da rangwamen kayan aikin gona kamar taki da iri da kuma magungunan feshi, babu shakka noma zai kara bunƙasa a Nijeriya. Ya ce idan kayan aikin gona sun zama masu sauki, manoma za su ƙara ƙarfin gwiwar faɗaɗa ayyukansu na noma,…
Read More
Tsarin tattalin arzikin Tinubu ya ceto Nijeriya daga almubazzaranci – IMPI

Tsarin tattalin arzikin Tinubu ya ceto Nijeriya daga almubazzaranci – IMPI

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kafofin Yaɗa Labarai Masu Zaman Kansu da Shirye-Shiryen Manufofi (IMPI) ta bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo gagarumin sauyi a tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar aiwatar da manufofin ci gaba na tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen fitar da ƙasar daga dogon zamani na almubazzaranci da rashin tsari. A cikin wata sanarwar manufofi da Shugaban ƙungiyar, Dakta Omoniyi Akinsiju, ya rattaba hannu a kai, IMPI ta jaddada cewa wannan salo na gyaran tattalin arziki shi ne mafi dacewa wajen warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye tsarin kuɗi da tafiyar da harkokin…
Read More
PSG ta kare kambun gasar zakarun Turai bayan doke Arsenal

PSG ta kare kambun gasar zakarun Turai bayan doke Arsenal

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain (PSG) ta sake lashe kofin gasar zakarun Turai ta UEFA bayan ta doke Arsenal a wasan ƙarshe da aka buga cikin tsananin fafatawa. Wasan ya ƙare da ci 1-1 bayan ƙarin lokaci, kafin PSG ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida domin kare kambunta. Arsenal ce ta fara zura ƙwallo tun a minti na shida ta hannun Kai Havertz, lamarin da ya ba ta damar mamaye wasu sassan wasan. Sai dai PSG ta nuna jajircewa tare da dawowa cikin wasan, inda gwarzon ɗan wasanta Ousmane Dembélé ya…
Read More
Dalilin da ya sa Tinubu ya ɓoye shirin cire tallafin mai daga jawabin rantsuwarsa – Shettima

Dalilin da ya sa Tinubu ya ɓoye shirin cire tallafin mai daga jawabin rantsuwarsa – Shettima

Daga USMAN KAROFI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɓoye aniyarsa ta cire tallafin man fetur daga jawabin rantsuwar kama aiki domin kauce wa matsin lamba daga masu adawa da matakin. Ya ce an ɗauki wannan shawara tun kafin Tinubu ya hau mulki, kuma ba mataki ne da aka ɗauka cikin gaggawa ba. Shettima ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da gwamnoni a Legas a yayin bukukuwan babbar sallah da cikar gwamnatin Tinubu shekaru uku a kan karagar mulki. A cewarsa, shugaban ƙasar ya san cewa idan ya bayyana shirin cire tallafin…
Read More
Tawagar ‘yan majalisar tarayya ta yaba da yadda aka gudanar da aikin hajjin 2026

Tawagar ‘yan majalisar tarayya ta yaba da yadda aka gudanar da aikin hajjin 2026

Daga SHAFII SANI MOHAMMED Wata tawaga daga Majalisar Tarayya wadda ke da alhakin sa ido kan hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta gudanar da ziyarar duba tantunan maniyatan Najeriya a Mina, a matsayin wani ɓangare na tantance yadda aikin Hajjin shekarar 2026 ke gudana. Wannan ziyarar sa ido ta kasance cikin hurumin doka na majalisar domin sa ido kan yadda ake tafiyar da aikin Hajji tare da tabbatar da cewa maniyatan Najeriya na samun ingantaccen kulawa da ayyuka masu inganci a tsawon zamansu a ƙasar Saudiyya. A yayin ziyarar, tawagar ta duba wasu tantuna na jihohin Najeriya inda ta gana…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a ƙauyen Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a ƙauyen Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga sun kashe mutane 16 a wani mummunan hari da suka kai a ƙauyen Kiliya da ke a garin Bagagadi a ƙaramar hukumar Dutsinma. Harin da yabar wasu da dama ɗauke da raunuka ya faru ranar juma'a a lokacin da mutanen ƙauyen ke cigaba da bukuuwan sallah. Kamar yadda wasu mutanen ƙauyen da suka nemi a ɓoye sunan su,sun faɗa cewa 'yan bindigan sun fara shigowa ƙauyen a kan babura guda biyu da ganin haka mutanen ƙauyen suka fara gujewa ƙauyen. Sai dai majiyar mu ta shaida cewa nan take 'yan bindigan suka hana…
Read More
Mutane uku sun rasu sakamakon faɗawa cikin rijiya a Kano

Mutane uku sun rasu sakamakon faɗawa cikin rijiya a Kano

Daga USMAN KAROFI Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon faɗawa cikin rijiyoyi daban-daban a lokuta daban a ranar Juma’a. Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce an samu kiran gaggawa da safiyar ranar, inda aka garzaya domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su. A cewar hukumar, an fara samun rahoton mutuwar wani namiji da ba a san ko wane ne ba a unguwar Semegu da ke ƙaramar hukumar Kumbotso. An ce jami’an ceto sun ciro gawarsa daga cikin rijiya tare da mika ta ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kan musabbabin…
Read More
Gwamnoni sun buƙaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa ₦100,000

Gwamnoni sun buƙaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa ₦100,000

Daga USMAN KAROFI Gwamnonin Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar Nigeria Governors’ Forum (NGF) sun yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi la’akari da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa N100,000. Sun ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta yi, musamman cire tallafin mai, sun ƙara yawan kuɗaɗen da jihohi ke samu, wanda ke ba su damar biyan basussuka da gudanar da ayyuka. Shugaban NGF kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce jihohi da dama a baya sun dogara ne da rance da kuma sayen bashi domin tafiyar da harkokinsu, amma yanzu yanayin ya sauya. Ya bayyana…
Read More