ukarofi

12556 Posts
Gwamna Uba Sani ya raba wa alhazan Kaduna Riyal 300 a Makkah

Gwamna Uba Sani ya raba wa alhazan Kaduna Riyal 300 a Makkah

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bai wa kowane mahajjacin jihar kyautar Riyal 300 na Saudiyya yayin da ya kai musu ziyara a sansanoninsu da ke Mina a daren Alhamis. A cewar sanarwar da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Malam Ibraheem Musa, ya fitar, kowanne mahajjaci zai karɓi kusan Naira 114,000 bisa farashin canjin kuɗi na yanzu. Gwamnan ya yaba da ɗabi’a da jajircewar alhazan Kaduna tare da jinjinawa hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Kaduna bisa nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. Haka kuma ya yaba wa kwamitin tawagar Hajji na jihar ƙarƙashin jagorancin…
Read More
Liverpool ta sallami Arne Slot

Liverpool ta sallami Arne Slot

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Liverpool ta sallami kocinta, Arne Slot, bayan ya shafe shekaru biyu yana jagorantar ƙungiyar. Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne sakamakon rashin kyakkyawan sakamako a kakarsa ta biyu, duk da cewa ya lashe gasar firimiya a shekararsa ta farko. Arne Slot, mai shekaru 47, ya jagoranci Liverpool zuwa lashe kofin gasar lig na 20 a kakarsa ta farko, abin da ya ƙara masa suna a cikin kwallon kafa ta Ingila. Sai dai a kakarsa ta biyu, ƙungiyar ta fuskanci matsaloli da suka kai ta kammala kakar a mataki na biyar a…
Read More
Tsagin Turaki na PDP ya bayyana Jonathan a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2027

Tsagin Turaki na PDP ya bayyana Jonathan a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2027

Daga USMAN KAROFI Wata ɓangare na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa bai halarci taron ba. An amince da takarar Jonathan ne a wani babban taro na musamman da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin ɓangaren Kabiru Turaki. Rahotanni sun bayyana cewa an miƙa takardar tabbatar da takararsa ga ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Fred Agbedi, wanda ya karɓe a madadin Jonathan. Wannan mataki ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke ci gaba da raba jam’iyyar zuwa ɓangarori daban-daban,…
Read More
An kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a Ogun

An kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a Ogun

Daga USMAN KAROFI Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da masu garkuwa da mutane bayan kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren satar mutane da suka addabi yankuna daban-daban na jihar. Binciken da jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane suka gudanar ya kai ga kama Muhammadu Abdullai mai shekaru 67, wanda ke riƙe da sarautar Seriki Fulani na Ijebu-Ode. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gano wata jaka da aka yi amfani da ita wajen kai kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane a cikin harabar gidan iyalan wanda ake…
Read More
An naɗa alƙalin da zai saurari ƙarar ADC tsakanin David Mark da Nafi’u Bala

An naɗa alƙalin da zai saurari ƙarar ADC tsakanin David Mark da Nafi’u Bala

Daga USMAN KAROFI Babban alƙalin kotun tarayya ya sake tura ƙarar da ke ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC zuwa hannun wani sabon alƙali domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙarar dai Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ne ya shigar yana ƙalubalantar halaccin shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark. An mayar da shari’ar ga Mai Shari’a Peter Lifu bayan tsohon alƙalin da ke saurarar ƙarar, Emeka Nwite, ya kasance cikin alƙalan da majalisar kula da harkokin shari’a ta ƙasa (NJC) ta ba da shawarar a naɗa su a matsayin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara. Nafiu Bala na neman…
Read More
Cire tallafin mai ya ceto Nijeriya daga talaucewa – Tinubu

Cire tallafin mai ya ceto Nijeriya daga talaucewa – Tinubu

Daga USMAN KAROFI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi ya ceci Najeriya daga faɗawa cikin matsanancin taɓarɓarewar tattalin arziki. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jihohi da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah da kuma cika shekaru uku da hawansa mulki. Shugaban ya amince cewa matakin cire tallafin ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalu a farko, amma ya ce hakan ya zama dole domin daƙile durƙushewar tattalin arzikin ƙasar. A cewarsa, an shafe shekaru ana kashe makudan kuɗaɗe wajen biyan tallafin da…
Read More
An samu raguwar masu kamuwa da cutar Lassa – NCDC

An samu raguwar masu kamuwa da cutar Lassa – NCDC

Daga USMAN KAROFI Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar Lassa a mako na 19 na shekarar 2026. A cewar rahoton hukumar, adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya ragu daga mutum 22 a makon da ya gabata zuwa mutum 17, inda aka samu sabbin masu ɗauke da cutar a jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Kogi, Taraba da Nasarawa. Sai dai duk da wannan raguwar, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 204 tun daga farkon shekarar 2026. Hukumar ta bayyana cewa kaso…
Read More
Rikicin PDP: ‘Yan sanda sun rufe hanyar shiga wurin taron ƙaddamar da takarar Jonathan

Rikicin PDP: ‘Yan sanda sun rufe hanyar shiga wurin taron ƙaddamar da takarar Jonathan

Daga USMAN KAROFI Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya sake ɗaukar wani sabon salo bayan da jami’an ‘yan sanda suka tare hanyar shiga dandalin taron da ɓangaren jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya shirya a Abuja domin amincewa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027. Rikicin PDP ya samo asali ne tun bayan shan kayen da jam’iyyar ta yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda saɓani kan shugabanci da ikon tafiyar da harkokin jam’iyyar ya haifar da ɓangarori masu adawa da juna. Wani ɓangare na samun goyon…
Read More
NOA ta fara yaƙin wayar da kai kan ambaliyar ruwa a Jigawa

NOA ta fara yaƙin wayar da kai kan ambaliyar ruwa a Jigawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da damina ke ƙaratowa, hasashen Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) sun nuna cewa za a fuskanci ruwan sama mai ƙarfi a jihohi 33 da fiye da yankuna 14,000 a faɗin ƙasar nan, ciki har da Jihar Jigawa, Hukumar Wayar da Kai ta ƙasa (NOA) a jihar ta sanar da fara gangamin wayar da kai domin rage illar ambaliya da kuma shirye-shiryen ko-ta-kwana. Daraktan Hukumar NOA na Jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Dutse…
Read More
Mazaunin Borno ya zargi gwamnati da bai wa tubabbun ’yan Boko Haram miliyoyin Naira

Mazaunin Borno ya zargi gwamnati da bai wa tubabbun ’yan Boko Haram miliyoyin Naira

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗan asalin jihar Borno mai suna Enoch Yohanna ya tayar da ƙura bayan ya zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da bai wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram da suka tuba kuɗaɗe har Naira miliyan uku bayan kammala shirin gyaran hali. Yohanna ya yi wannan zargi ne yayin wani taron jama’a, inda ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira amfani da kuɗin harajin jama’a wajen tallafa wa mutanen da ake zargi da hannu a kashe-kashe da sace-sacen jama’a a yankin Arewa maso Gabas. A cewarsa, “Abin da ke ƙona min rai shi ne mutanen da suka kashe…
Read More