30
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da damina ke ƙaratowa, hasashen Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) sun nuna cewa za a fuskanci ruwan sama mai ƙarfi a jihohi 33 da fiye da yankuna 14,000 a faɗin ƙasar nan, ciki har da Jihar Jigawa, Hukumar Wayar da Kai ta ƙasa (NOA) a jihar ta sanar da fara gangamin wayar da kai domin rage illar ambaliya da kuma shirye-shiryen ko-ta-kwana. Daraktan Hukumar NOA na Jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Dutse…
