ukarofi

12556 Posts
Kada ki tsaya jiran dama, ki zama dalilin samuwar ta – Marie Curie 

Kada ki tsaya jiran dama, ki zama dalilin samuwar ta – Marie Curie 

“Bai kamata ka kalli abin da aka riga aka yi ba, ka mai da hankali kan abin da za ka iya yi” (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  A cikin wannan shafi mai farin jini na Gimbiya, muna ci gaba da haskaka rayuwar mata jarumai, waɗanda suka tsallake rijiya da baya, suka fuskanci ƙalubalai masu tsanani, amma suka tsaya tsayin daka har suka zama abin koyi ga al’umma. Kamar yadda ku ka sani wannan shafi ba kawai shafin bayar da labaran rayuwar mata ba ne, wuri ne na ilmantarwa da tunatarwa, inda ake fito da rayuwar mata domin…
Read More
NUT a Oyo ta umarci malamai su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

NUT a Oyo ta umarci malamai su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar malaman Nijeriya (NUT) reshen Jihar Oyo ta umarci dukkan malaman makarantun firamare da sakandare na gwamnati su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026. Matakin ya biyo bayan sace malamai da ɗalibai da aka yi a ƙaramar hukumar Orire ta jihar. A cikin wata sanarwa da Shugaban NUT na jihar, Hassan Fatai, da sakatare, Salami Olukayode, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda waɗanda aka sace ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane. Ta ce lamarin ya jefa malamai, ɗalibai da iyayensu…
Read More
Yaƙi ya dawo sabo tsakanin Amurka da Iran bayan sabbin hare-hare

Yaƙi ya dawo sabo tsakanin Amurka da Iran bayan sabbin hare-hare

Daga USMAN KAROFI Yaƙi tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar wani sabon salo bayan Amurka ta kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a ƙarshen mako, yayin da Iran ta mayar da martani da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. Rundunar Amurka ta ce hare-haren nata sun biyo bayan zargin cewa Iran ta harbo jirgin leƙen asirin Amurka mara matuƙi da ke shawagi a sararin samaniyar ƙasa da ƙasa. A cewar CENTCOM, jiragen yaƙin Amurka sun lalata wasu cibiyoyin kariyar sararin samaniyar Iran, cibiyar sarrafa hare-hare da kuma wasu jirage marasa matuƙi da ake…
Read More
Shekaru ukun Uba Sani sun sauya fasalin Kaduna – Sanata Hunƙuyi

Shekaru ukun Uba Sani sun sauya fasalin Kaduna – Sanata Hunƙuyi

Kwamishinan da ke wakiltar shiyyar Arewa maso yamma a hukumar kula da ayyukan majalisar dokoki ta ƙasa (NASC), Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya taya Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, murnar cika shekaru uku a mulki, inda ya bayyana wa’adin gwamnatin a matsayin lokaci na sauyi mai ma’ana da ya sake fasalta jihar Kaduna. A cikin saƙon taya murnar da ya fitar domin bikin cika shekaru uku na gwamnatin Uba Sani, Hunkuyi ya ce gwamnan ya nuna shugabanci mai hangen nesa da mayar da hankali kan buƙatun jama’a, wanda ya haifar da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma. Ya…
Read More
‘Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, Ali Bahago a Zamfara

‘Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, Ali Bahago a Zamfara

Daga USMAN KAROFI Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta sanar da cafke wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga mai suna Ali Bahago Danakulu tare da wasu mutum uku da ake zargi daga dabar sa. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan wasu masu aikata laifuka da ke addabar al’ummomin Kasuwan Daji da kewaye. A cewar rundunar, waɗanda aka kama sun haɗa da Ali Bahago Danakulu, Hassan Dan Kure da Dahiru Lawali. Binciken farko ya nuna cewa suna cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da aikata fashi da makami…
Read More
Jam’iyyar Labour Party a Nasarawa ta sanar da ‘yan takararta na zaɓen 2027

Jam’iyyar Labour Party a Nasarawa ta sanar da ‘yan takararta na zaɓen 2027

Daga JOHN D WADA a Lafia Jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Nasarawa ta fitar da sakamakon zaɓen fidda gwaninta na ‘yan takaran kujerar gwamna da sanata da majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar. Shugaban kwamitin zaɓen a jihar Dr. Kalu Ekeh ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Lafia babban birnin jihar inda ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana da gaskiya. Ya sanar cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Karu/Keffi/Kokona wato Hon. Jonathan Gaza ya fito takar gwamnan jihar a ƙarƙashin LP ɗin inda aka kuma tabbatar da shi ba tare da hamayya ba bisa dokar…
Read More
Gombe 2027: Ma’aikatan KEDCO sun tara wa Jamilu Gwamna Naira miliyan 23

Gombe 2027: Ma’aikatan KEDCO sun tara wa Jamilu Gwamna Naira miliyan 23

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) sun tara sama da naira miliyan 23 domin tallafa wa kamfen ɗin takarar gwamna na Dokta Jamilu Isyaku Gwamna, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Gombe. An bayyana hakan ne a wani taron karramawa da ma’aikatan kamfanin suka shirya masa, inda suka ce gudummawar ta samo asali ne daga godiyar da suke yi masa bisa damar aikin yi da ya samar wa mutane da dama lokacin da yake jagorantar kamfanin a matsayin Manajan Darakta. Shugaban kwamitin shirya taron, Sa’idu Sambo, ya ce ma’aikatan sun tara…
Read More
Katsina United ce za ta lashe gasar NPFI a kakar wasanni mai zuwa – Sarajo Abukur

Katsina United ce za ta lashe gasar NPFI a kakar wasanni mai zuwa – Sarajo Abukur

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma’aikatar wasanni ta Jihar Katsina ta lashi takonin ganin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta lashe gasar (NPFL) da samun tikitin gasar nahiyar Afirka. A lokacin taron masu ruwa da tsaki da ma'aikatan wasanni ta shirya tayi nazarin kakar wasannin da ta gabata da shirye-shiryen kakar wasa mai zuwa. Kamar yadda sashin yaɗa labarai na ma’aikatar,ta umarci mahukuntan ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Katsina United da su tabbatar sun kawo kofin gasar firimiya ta Najeriya wato (NPFL) ko samo tikitin shiga gasar nahiyar Afirka a kakar wasa mai zuwa. Kwamishinan wasannin jihar,Injiniya Surajo Yazeed Abukur,…
Read More
Kebbi ta tattara malamai 100 wurin addu’ar nasarar zaɓen 2027

Kebbi ta tattara malamai 100 wurin addu’ar nasarar zaɓen 2027

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi. Malamai guda 100 mabiya ɗariqatul tijjaniyya da masu aƙiidar Izala daga ulama na Jihar Kebbi suka hallara a ɗakin taron masaukin shugaban ƙasa dake Birnin Kebbi, ranar Jumu'a da ta wuce, suka nuna yabo ga Allah na cika shekara uku akan karagar mulkin na gwamnatin Kwamred, Dakta Nasir Idris, a matsayin gwamnar Jihar Kebbi mai cikakken iko. Gwamnatin Jiharce ta kira taron domin gudanar da addu'oi masu zurfi, na samun nasarar zaɓen 2027, da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a Kebbi da kuma ƙasa baki ɗaya. Da yake share fage, babban sakatare a…
Read More
Obi ya zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimaki a zaɓen 2027

Obi ya zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimaki a zaɓen 2027

Daga USMAN KAROFI Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaɓen 2027 mai zuwa. An bayyana hakan ne a ranar Asabar jim kaɗan bayan jam’iyyar NDC ta tabbatar da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a taronta na musamman da aka gudanar a Abuja. Wannan mataki ya tabbatar da jita-jitar da ta daɗe tana yawo kan yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu. Obi ya fito ne a matsayin dan takara ɗaya tilo a jam’iyyar, sannan…
Read More