ukarofi

12554 Posts
Mu kula da yanayin mata domin rashin fahimtarsu na jawo mutuwar aure

Mu kula da yanayin mata domin rashin fahimtarsu na jawo mutuwar aure

Assalamu alaikum, barka da warhaka, Edita. Da fatan kowa yana lafiya. A lokuta da yawa aure yakan mutu saboda rashin sani ko ƙarancin ilimin maza game da yanayin mata a lokacin da za su fara al’ada (menstruation), ko suke yi; ko lokacin da suke ɗauke da ƙaramin ciki, wato lokacin laulayi da lokacin da cikin ya kai wata bakwai zuwa lokacin da za su haife shi. Kwana 5 ko 8 kafin su fara al’ada suna zama kwanakin haƙuri ga duk magidancin da ya gane haka. Duk da yake cewa ba a cika tattauna irin waɗannan abubuwa a nan ƙasar Hausa…
Read More
2027 zaɓe ne tsakanin masu hankali da masu ƙarancin tunani

2027 zaɓe ne tsakanin masu hankali da masu ƙarancin tunani

Daga UNCLE LARABI Ina mamakin yadda kuke kasa amfani da tunaninku wajen gane cewar, da Tinubu da Peter Obi duk abu ɗaya ne, kawai shi Tinubu ya yaudare ku da Musulunci ne. Sannan shi Atiku ko ya ci kujerar Shugaban ƙasa babu abin da zai canja daga irin mulkinsu Tinubu ɗin. Shi Tinubu ana so a kawar da shi a kawo wani sabo ne, don a koya wa duk wani shugaba darasi. Da a ce a 2019 ba a sake zaɓen Buhari ba, an kifar da shi da ko waye ya hau bayansa, sai ya shiga taitayinsa, amma sai ’yan Arewa…
Read More
Sabuwar Nijeriya daga 1 ga Oktoba, 2026?

Sabuwar Nijeriya daga 1 ga Oktoba, 2026?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Tun bayan shigowar gwamnatin Tinubu ake ta rade-radin cewa akwai yunkuri na maida Najeriya kan tsohon tsarin mulki na shiyyoyi (Regions) wanda aka gwada a shekarun 1960 lokacin su Sardauna, Zik da Awolowo. A halin da ake ciki kuwa an gano wata shawara (proposal) ta sauya fasalin Najeriya (Geo-political zone bill) da ke ta kara-kaina a majalisa wadda Dr Akin Fapohunda ya dau nauyi. Wannan doka da ake son ganin ta sami karbuwa a majalisa, nan da zuwa 1st ga watan October, ranar da Najeriya ke cika shekaru 66, ake son ta kama aiki. Ana son…
Read More
Nana Bin Fodio ta ciri tutar alheri

Nana Bin Fodio ta ciri tutar alheri

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa har dai mutum zai dubu tarihin haziƙan mata a yankin Arewacin Nijeriya da kewaye, sai ya Ambato sunan haziƙa kuma malama Nana Asma’u ‘yan Shehu Usman Mujaddadi. Abin farin ciki game da Nana shi ne kwarewarta wajen rubutun darussan addinin Musulunci musamman cikin wake. Haƙiƙa mu na da mata a yankin nan da su ka shahara wajen sarauta, jarumtakar yaƙi har kuma a sabon zamani wajen siyasa, tattalin arziki da sauran su, amma ita Nana a kan koyarwar addinin musulunci ta shahara kuma shekaru aru-aru bayan komawarta ga Allah, sunanta ya na nan a raye…
Read More
Sauyin Jam’iyya: Mene ne makomar dimukraɗiyyar Nijeriya?

Sauyin Jam’iyya: Mene ne makomar dimukraɗiyyar Nijeriya?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  ’Yan Nijeriya da sauran manazarta harkokin siyasa na ganin yadda ’yan siyasar ƙasar nan musamman gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisu, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa ke tururuwar canjin sheƙa daga jam’iyyun da aka zaɓe su akai zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ko wasu manyan jam’iyyun adawa, alamu ne dake nuna cewa Nijeriya ta doshi zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya, a wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar Babban Zaɓen shekarar 2027. A halin yanzu, ana ganin tsarin dimukraɗiyyar Nijeriya na fuskantar sauyi mafi girma, inda jam’iyyu da dama ke rasa ƙarfinsu, wanda hakan ke haifar da tambayoyi…
Read More
NCDC: Najeriya na da kashi 59% kacal wajen shirin tunkarar Ebola

NCDC: Najeriya na da kashi 59% kacal wajen shirin tunkarar Ebola

Daga USMAN KAROFI Babban daraktan hukumar kula dake kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (Nigeria Centre for Disease Control and Prevention), Dakta Jide Idris, ya bayyana cewa Najeriya na da shirin kashi 59 cikin 100 ne kawai wajen fuskantar yiwuwar ɓullar cutar Ebola. Ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin sa ido da daƙile cututtuka, har yanzu akwai manyan giɓi musamman a filayen jiragen sama da iyakokin ƙasa masu sauƙin shiga. Da yake magana a wata hira da aka yi da shi, Dakta Idris ya ce NCDC ta gudanar da bincike domin auna matakin shirin…
Read More
Tun daga Kaduna mu ke bin Manjo Janar Rabe — Ɗan bindiga Kachalla

Tun daga Kaduna mu ke bin Manjo Janar Rabe — Ɗan bindiga Kachalla

Daga UMAR GARBA a Katsina Kachalla Muhammadu, shugaban dabar ’yan bindiga da ake zargin suna tsare da Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, ya bayyana yadda suka riƙa bibiyar tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya kafin su kama shi. A cikin wani saƙon murya da majiyar Blueprint Manhaja ta Katsina Times ta samu ya an ji Kachalla Muhammadu na cewa lallai Janar ɗin yana hannunsu tsare a maɓoyarsu. Majiyar ta ce a cikin saƙon muryar, Kachalla Muhammadu ya tabbatar da cewa Janar Rabe na cikin ƙoshin lafiya a inda suke tsare da shi. A cewarsa, tun daga birnin Kaduna suke samun…
Read More
Ba mu yarda da danniya a APC ta Gombe ba – Buba Kwacam

Ba mu yarda da danniya a APC ta Gombe ba – Buba Kwacam

Daga AISHA ASAS A cikin wannan kaka ta siyasa da ke ƙara ɗaukar zafi a fagen siyasar Najeriya, an samu wasu takun-saƙa da suka fi jan hankalin jama’a, musamman a ɓangaren siyasar Jihar Adamawa. Daga cikin batutuwan da suka mamaye tattaunawar siyasa akwai takarar kujerar majalisar dattawa da ke haɗa sunan Hon. Abdurrahman Buba Kwacam da kuma gwamna mai ci a yanzu, Ahmadu Umaru Fintiri. Lamarin ya soma ɗaukar hankali ne tun bayan da ake zargin gwamnan ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. Wannan mataki ya haifar da rashin jituwa a tsakanin wasu…
Read More
Kada ki tsaya jiran dama, ki zama dalilin samuwar ta – Marie Curie 

Kada ki tsaya jiran dama, ki zama dalilin samuwar ta – Marie Curie 

“Bai kamata ka kalli abin da aka riga aka yi ba, ka mai da hankali kan abin da za ka iya yi” (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  A cikin wannan shafi mai farin jini na Gimbiya, muna ci gaba da haskaka rayuwar mata jarumai, waɗanda suka tsallake rijiya da baya, suka fuskanci ƙalubalai masu tsanani, amma suka tsaya tsayin daka har suka zama abin koyi ga al’umma. Kamar yadda ku ka sani wannan shafi ba kawai shafin bayar da labaran rayuwar mata ba ne, wuri ne na ilmantarwa da tunatarwa, inda ake fito da rayuwar mata domin…
Read More
NUT a Oyo ta umarci malamai su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

NUT a Oyo ta umarci malamai su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar malaman Nijeriya (NUT) reshen Jihar Oyo ta umarci dukkan malaman makarantun firamare da sakandare na gwamnati su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026. Matakin ya biyo bayan sace malamai da ɗalibai da aka yi a ƙaramar hukumar Orire ta jihar. A cikin wata sanarwa da Shugaban NUT na jihar, Hassan Fatai, da sakatare, Salami Olukayode, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda waɗanda aka sace ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane. Ta ce lamarin ya jefa malamai, ɗalibai da iyayensu…
Read More