03
Jun
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ci gaba da tallafa wa iyalan waɗanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa, inda kwamitin rabon tallafin ya kai ziyara a garin Jiƙamshi domin rabon tallafin ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka. Mutane 19 ne suka amfana da tallafin da ya kai jimillar Naira miliyan 2.3. Daga cikin waɗanda suka amfana akwai iyalan mutum tara da aka kashe, inda kowanne su ya karbi Naira N200,000, yayin da mutane 10 da suka samu raunuka suka karbi Naira N50,000 kowannensu. Kwamitin ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya da jaje ga…
