ukarofi

12553 Posts
Kaduna: Shugaban Capacity Movement ya yi kira ga Yusuf Zailani da ya kwantar da hankali kan rikicin APC 

Kaduna: Shugaban Capacity Movement ya yi kira ga Yusuf Zailani da ya kwantar da hankali kan rikicin APC 

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Shugaban ƙungiyar Capacity Movement ta ƙasa, Shehu Sani Sado, ya buƙaci tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna kuma tsohon ɗan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Rt. hon. Yusuf Ibrahim Zailani, da ya kwantar da hankali tare da bai wa zaman lafiya da haɗin kai fifiko dangane da rikicin da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam'iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a Jihar Kaduna. Alhaji Shehu Sani Sado ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a ƙaramar Hukumar Igabi, inda ya jaddada muhimmancin kauce wa kalamai…
Read More
EBOLA: Rigakafi ya fi magani

EBOLA: Rigakafi ya fi magani

Yayin da cutar Ebola (EVD) ke sake ɓulla a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) tare da tabbatar da samun wani mutum da ya shigo da cutar a maƙwabciyar ƙasar Uganda, duniya ta sake shiga yanayin fargaba da taka-tsantsan.  Wannan lamari ya sake tunatar da al’ummar duniya cewa cututtuka masu yaɗuwa ba sa mutunta iyakokin ƙasashe, kuma sa ido da shiri tun kafin matsala ta auku su ne manyan makaman kariya daga annoba. Da take fahimtar girman barazanar da lamarin ke haifarwa, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ɓarkewar cutar a matsayin Gaggawar Lafiyar Jama’a Ta Duniya (PHEIC). Ko da yake…
Read More
Cutar Ebola: Me ya kamata mu sani

Cutar Ebola: Me ya kamata mu sani

Daga USMAN KAROFI Ebola Virus Disease (EVD)cuta ce mai tsanani da ƙwayar cuta ta Ebola ke haifarwa. Tana daga cikin cututtukan da idan aka kamu da ita, mafi yawa ana rasa rai, inda tsakanin kashi 25% zuwa 90% na masu kamuwa da ita kan rasa rayukansu idan ba a gano ta da wuri ba. Masana sun yi imanin cewa jemagu masu cin 'ya'yan itatuwa (fruit bats) su ne manyan ma'ajiyar wannan ƙwayar cuta. Yadda Ebola ke yaɗuwa Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar hulɗa da jemagu ko wasu dabbobin da suka kamu da ita kamar birrai, ɓeraye da sauransu.…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya taya gwamnan Bayelsa, Douye Diri murnar cika shekaru 67 da haihuwa

Gwamna Raɗɗa ya taya gwamnan Bayelsa, Douye Diri murnar cika shekaru 67 da haihuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya aike da saƙon taya murna ga gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, bisa cika shekaru 67 da haihuwa. Gwamna Raɗɗa ya yaba da nagartaccen jagoranci da kuma gagarumin ci gaban da Gwamna Diri ya samar a Jihar Bayelsa tun bayan hawansa mulki. Ya bayyana cewa gwamnatin Diri ta nuna cikakken jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar Bayelsa ta hanyar zuba jari a muhimman fannoni da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, gine-ginen more rayuwa da kuma bunƙasa tattalin arziki. A cewar Gwamna Raɗɗa: “Mulkin ka ya tabbatar da cewa…
Read More
ADC ta ƙaryata jita-jitar janyewar Mahdi Aliyu daga takarar gwamnan Zamfara a 2027

ADC ta ƙaryata jita-jitar janyewar Mahdi Aliyu daga takarar gwamnan Zamfara a 2027

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar ADC, a Jihar Zamfara ta yi watsi da rahotannin ƙarya da na ɓatanci da ke yawo a shafukan sada zumunta suna iƙirarin cewa ɗan takarar gwamna a 2027, Barr. Mahdi Aliyu Muhammad, ya janye daga takarar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar ta bayyana rahoton da ke yawo a yanar gizo a matsayin, ƙirƙirarre, kuma aikin wasu 'yan siyasa ne da nufin ɓatar da jama'a da kuma haifar da ruɗani kafin zaɓen 2027. Sanarwar da Salisu Mohammed Mada, sakataren yaɗa labarai/mai magana da yawun Barista Mahdi Aliyu Muhammad ta sanya wa hannu,…
Read More
Kwamitin kula da gandun daji ya jaddada kiyaye dokoki a Katsina

Kwamitin kula da gandun daji ya jaddada kiyaye dokoki a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamitin kula da gandun daji (Task Force Committee on Forest Reserve) ya gudanar da taron wayar da kai tare da sauraron ƙorafe-ƙorafen da ƙalubalen da jami’an kula da gandun daji ke fuskanta a Jihar Katsina. Taron ya gudana ne a sakatariyar ƙaramar hukumar Kankiya inda ya haɗa jami’an kula da gandun daji daga ƙananan hukumomin Kankia, Kusada, Ingawa, Musawa, Matazu, Danmusa, Dutsin-Ma, Kurfi, Safana da Batsari. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin, Alhaji Khalil Bako, ya bayyana cewa manufar taron ita ce duba yadda ayyukan kula da gandun daji ke gudana, sauraron ƙalubalen…
Read More
Nasarawa 2027: Sanata Wadada ya yi kira a yi sulhu bayan nasarar zaɓen fidda gwanin APC

Nasarawa 2027: Sanata Wadada ya yi kira a yi sulhu bayan nasarar zaɓen fidda gwanin APC

Daga JOHN D WADA a Lafia Sanata Ahmed Aliyu Wadada mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta tarayya ya amince da zaɓin da magoya bayan jam'iyyar APC suka yi masa a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027 da ke tafe. Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Lafia babban birnin jihar tare da shugabannin jam’iyyar Wadada yace zaɓen fidda gwani na APC din bai samar da “mai nasara ba, kuma babu wanda ya sha kaye” yayi kira da haɗin kai a cikin jam’iyyar. “Na amince da wannan amanar da ‘yan jam’iyyar mu suka…
Read More
Ba ni da masaniya a kan takarar Abba – Ɗahiru Mangal

Ba ni da masaniya a kan takarar Abba – Ɗahiru Mangal

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina‎Ko alama bani da masaniya alkan wannan takararta Abba, hasalima bana ra'ayin wani daga cikin ahalina ya shiga siyasa, kawai dai babu yadda za kayi idan Allah yayi tsarinsa Waɗannan kalamai sun fito daga bakin hamshaƙin ɗan kasuwa kuma jigo a jam'iyar APC, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal da yake tsokaci akan takarar ɗaya daga cikin ɗan sa Barista Abba Ɗahiru Mangal.‎‎Yace "Allah ne ya ƙaddara wannan yaro shine za'a bawa tikitin takarar nan to ni babu abinda zanice face ince masa sai dai Allah ya yi masa jagora,"‎‎Mangal yayi fatan idan Allah ya bashi kujerar Allah…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Zaki ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Bala Muhammad

Shugaban ƙaramar hukumar Zaki ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Bala Muhammad

Daga GAMBO ISA Shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Dakta Adamu Yakubu Sakwa, ya yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, bisa irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ci gaba da kyautata rayuwar al’ummar jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Sakwa ya bayyana cewa gwamnatin Bala Muhammad ta samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, noma, tsaro da samar da ababen more rayuwa. Ya ce daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar akwai gina da gyaran sakatariyoyin gwamnati na zamani, samar da fitilun hasken rana a yankuna daban-daban,…
Read More
Matasa ‘yan Katsina za su buga tamola a ƙasashen waje – Joɓe

Matasa ‘yan Katsina za su buga tamola a ƙasashen waje – Joɓe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina tasha alwashin cigaba da haɗa hannu da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bai wa matasan Jihar Katsina damar ganin sun cimma burin su na buga ƙwallon ƙafa a ƙasashen waje. Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Faruq Lawal Joɓe ya bayyana haka a lokacin da ya amshi baƙuncin tawagar wakilan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Torpedo Belaz Zhodino da ke ƙasar Belarus waɗanda suka zo Jihar domin gudanar da shirin baje kolin 'yan wasan ƙwallon ƙafa da Katsina football academy ta ɗauki nauyi. 'Yan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Torpedo…
Read More