05
Jun
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani Bafulatani da ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane ya bayyana cewa, yawancin masu aikata garkuwa da mutane a Nijeriya ba Fulani ne ’yan asalin ƙasar ba, sai dai wasu daga ƙasashen maƙwabta, musamman daga yankin ƙasar Chadi. A cikin rahoton da aka samu daga jaridar IntelRegion, mutumin ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da labarin irin azabar da ya sha a hannun masu garkuwa da shi, inda ya ce ya kwashe watanni a tsare kafin daga bisani a sake shi. Ya ce, a duk lokacin da yake tsare, ya lura cewa…
