24
Jan
Daga RABIU SANUSI a Kano Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar Naira biliyan 8.53 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, ilimi, samar da ruwan sha da kuma jin daɗin al’umma a faɗin jihar. An yanke wannan shawara ne a taron Majalisar Zartarwa na 37 da aka gudanar a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2026, a Malam Aminu Kano House, Gidan Gwamna da ke Asokoro, Abuja. Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa…
