ukarofi

12661 Posts
Yadda aka yi kisan kai biyu cikin kwanaki uku a Kebbi 

Yadda aka yi kisan kai biyu cikin kwanaki uku a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta samu nasarar damƙe wani magidanci mai suna Suleiman Mamuda ɗan kimanin shekaru 30 ɗan asalin garin Bayawa da ke ƙaramar hukumar Augie yayin da yake kan hanyarsa ta tserewa bayan ya kashe matarsa mai suna Umaima Maidawa. Bayanin da wakilin Blueprint Manhaja ya tattara sun nuna cewa kisan ya biyo bayan barazanar da Umaima ke yi masa ne na cewa ita fa yanzu ta gaji da zama da shi saboda ba shi da kuɗi kamar yadda ya ke a baya saboda haka tana so ta kashe auren don ta…
Read More
Kotu ta ba da umarnin kamo waɗanda ake zargin na alaƙa da Bello Turji

Kotu ta ba da umarnin kamo waɗanda ake zargin na alaƙa da Bello Turji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin kamo wasu mutum biyar da ake zargin na alaƙa da ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji. Mai shari’a Emeka Nwite ne, ya bayar da umarnin a ranar Laraba bayan waɗanda ake tuhumar sun gaza halartar kotu domin fara shari’arsu. Lauyan Gwamnatin Tarayya ya nemi kotu ta bayar da takardar izinin kama su saboda rashin halartar su kotu. Mutanen sun haɗa da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da Doctor), Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma. Lauyansu ya…
Read More
Fitattun kisan da suka tada hankali a Arewa

Fitattun kisan da suka tada hankali a Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ‘yan shekarun nan, ana yawan samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya inda akasari kisan ke tayar da hankalin jama’a. Duk da cewa a faɗin Nijeriya ana samun rahotannin kisan kai akai-akai, amma irin waɗanda ake samu a Kano na jan hankali saboda abubuwan da ke tattare da kisan musamman na ban al’ajabi ko tsananin tausayi ko kuma wani abu da hankali bai cika ɗauka ba. Dangane da irin waɗannan abubuwa, Blueprint Manhaja ta yi nazari dangane da kisan-gilla biyar da suka yi matuƙar tayar da hankali a Kano. Kisan…
Read More
Bikin kamun kifin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa – Gwamnatin Tarayya

Bikin kamun kifin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa – Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta bayyana Bikin Kamun Kifi da Bajekolin Al’adu na Duniya na Argungu a matsayin wata babbar alama ta haɗin kan Nijeriya, gadon al’adu, da kuma karɓuwar al’adun ƙasar nan a idon duniya, yayin da ta jaddada muhimmancin sa wajen bunƙasa tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar buɗe taron bikin Argungu karo na 61, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 21 ga Janairu, 2026, a dandalin hedikwatar Hukumar Talbijin na ƙasa (NTA) da ke Abuja. Daraktan…
Read More
Alƙalin alƙalan Ribas ya ƙi fara bincikar Fubara da mataimakiyarsa

Alƙalin alƙalan Ribas ya ƙi fara bincikar Fubara da mataimakiyarsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Alƙalin Jihar Ribas, Mai Shari’a Simeon C. Amadi, ya ƙi amincewa da buƙatar majalisar dokokin jihar na kafa kwamitin bincike mai mambobi bakwai domin binciken zargin aikata manyan laifuka da ake yi wa gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma-Odu. Babban alƙalin ya bayyana cewa akwai umarnin kotu da har yanzu ke aiki, tare da ƙarar da ke gaban kotu ta ɗaukaka ƙara. Matsayar mai shari’a Amadi na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa ta hukuma da ya aikawa kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, inda ya tabbatar da karɓar buƙatu guda biyu daga Majalisar da…
Read More
Kaduna: ’Yan bindiga sun nemi miliyan N28.9 kafin fara tattaunawa

Kaduna: ’Yan bindiga sun nemi miliyan N28.9 kafin fara tattaunawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga da suka sace ɗaruruwan ’yan coci a ƙaramar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna sun buƙaci a biya su kuɗin babura da suka ce sun ɓata kafin su fara tattaunawar sakin mutanen da suke hannunsu. Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yi iƙirarin cewa babura 17 nasu ne suka ɓace a lokacin wani farmaki da jami’an tsaro suka kai a yankin, inda suka ce kowanne babur na da darajar Naira miliyan N1.7, wanda ya haɗa jimillar kuɗin da suka nema zuwa Naira miliyan N28.9. Sun ce dole ne a biya wannan kuɗi gaba…
Read More
Trump ya dakatar da shirin ƙaƙaba wa Turai haraji

Trump ya dakatar da shirin ƙaƙaba wa Turai haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Amurka Donald Trump ya ja baya daga barazanar ƙaƙaba wa ƙasashen Turai haraji tare da bayyana cewa ba zai yi amfani da ƙarfin soja wajen karɓar Greenland ba, yankin da ke ƙarƙashin ikon Denmark amma ke da ikon cin gashin kai a wasu fannoni. Wannan mataki ya zo ne bayan ganawarsa da Sakatare Janar na NATO, Mark Rutte, a gefen taron Dandalin Tattalin Arzikin Duniya da aka gudanar a Daɓos, Switzerland. A cewar Trump, sun cimma wani tsari na haɗin gwiwa kan makomar Greenland da yankin Arctic, wanda ya ce idan aka kammala shi zai…
Read More
Zargin ɗaukar nauyin ta’addanci: Ba a samu makamai a gidana ba — Malami

Zargin ɗaukar nauyin ta’addanci: Ba a samu makamai a gidana ba — Malami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke cewa an gano makamai a wasu gidaje da ake zargin mallakinsa ne. A cikin wata sanarwa da hadiminsa kan yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce labaran ba gaskiya ba ne. Ya ce: “Muna musanta iƙirarin da ke cewa an gano makamai ko harsasai a dukkanin wani gida da ake alaƙanta da Abubakar Malami, SAN.” Ya ce babu wata hukuma da ta sanar da shi, iyalansa ko lauyoyinsa cewa an samu makamai a…
Read More
ADC ta dakatar da shugabanta a Nasarawa

ADC ta dakatar da shugabanta a Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar ADC a Jihar Nasarawa, ta dakatar da shugabanta na jihar, Godwin Alaku Williams, bisa zargin aikata wasu abubuwa da suka saɓa wa dokokin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Idris Ojoko, ya ce an ɗauki matakin ne bayan samun wata takarda ƙorafi da ke zargin Alaku da ayyukan da ke barazana ga haɗin kai da cigaban jam’iyyar. Zarge-zargen sun haɗa da ƙin amincewa da shugabancin jam’iyyar na ƙasa, ƙin haɗa kai don yin haɗaka, da kuma kai rahoton shugabannin jam’iyyar ga hukumomin tsaro. An ce an dakatar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya, ƙwararru, cibiyoyi, da kamfanoni masu zaman kan su da su ɗauki nauyin ginawa tare da kare martabar ƙasar nan a idon duniya, ta hanyar sadarwa ta gaskiya da kuma nuna cigaban da ake samu. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wurin taron bitar martabar Nijeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja. Yayin da yake jawabi a taron, Ministan ya bayyana ƙaddamar da ma’aunin fahimtar martabar Nijeriya na farko da…
Read More