ukarofi

12661 Posts
Kotun ɗaukaka ƙara ta cika shekaru 50 da sauraron ƙararraki 360 cikin mako guda

Kotun ɗaukaka ƙara ta cika shekaru 50 da sauraron ƙararraki 360 cikin mako guda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara ta cika shekaru 50 da fara sauraron ƙararraki 360 cikin mako guda a Legas. Shugabar Kotun ɗaukaka ƙara, Mai Shari'a Monica Bolna'an Dongban-Mensem, ce ta jagoranci wannan shari'a, wacce ta ayyana matakin a matsayin martani mai ƙarfi da gangan ga ƙaruwar cunkoson da ake samu a kotunan, musamman a Legas, babban birnin kasuwanci na Nijeriya da kuma wuraren da ake shari'a. Da take bayyana Legas a matsayin bugun daga kai sai mai tsaron gida, Mai Shari'a Dongban-Mensem ta ce zaman na musamman ya dace kuma ya zama dole, tana mai lura…
Read More
Tsaro: Gwamnan Bauchi ya nemi haɗin kan sarakuna da al’umma wajen tattara bayanan sirri

Tsaro: Gwamnan Bauchi ya nemi haɗin kan sarakuna da al’umma wajen tattara bayanan sirri

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi kira ga jami’an tsaro a jihar kan su yi riƙo da adalci da sa ido da wajen gudanar da ayyukansu yana mai ba su tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta ci dunduniyar gwamnatin tarayya ba musamman kan abin da ya shafi tsaro duk da kasancewarsa a jam’iyyar adawa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin kwamitin tsaro a ranar Litinin wanda aka yi a fadar gwamnatin jihar da ke Bauchi. “Mun yarda da dunƙulalliyar ƙasa. Mun yarda matsayin gwamnatin tarayya ba tare da la’akari da matsayimu k-o…
Read More
Abba ya bai wa mutumin da aka kashe wa iyali kyautar kujerar hajji, gida da kuɗi

Abba ya bai wa mutumin da aka kashe wa iyali kyautar kujerar hajji, gida da kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa mutumin da aka kashe wa mata da yara shida a unguwar Chiranci ɗorayi, kyautar kuɗi, gida da kuma kujerar hajji. Tallafin ya haɗa da ɗaukar nauyin aikin Hajji da Umrah, samar masa da sabon gida, da kuma kulawar gwamnati. Gwamnan ya kuma umarci Babban Lauyan Jihar Kano, da ya tabbatar an hanzarta gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifin. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, bayan gwamnan ya…
Read More
Wani bawan Allah ya bayar da Naira milliyan shida don ɗaukar nauyin karatun marayu a Kebbi 

Wani bawan Allah ya bayar da Naira milliyan shida don ɗaukar nauyin karatun marayu a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Wani bawan Allah da bai so a bayyana sunan shi ba ya ware Naira milliyan shoda (6,000.000:00) domin daukar nnauyin karatun marayu da ke ƙarƙashin kulawar gidauniyar marayun ƙungiyar Mar'atusaliha Widows And Orphans Initiatiɓe da ke garin Argungu a jihar Kebbi. Shugabar ƙungiyar Mar'atusaliha a Masarautar Kabin Argungu Hajiya Mariya Muhammad Mera ce ta bayyana haka a yayin da ta ke zantawa da wakilin Blueprint Manhaja a garin Argungu. Ta bayyana cewa mutumin ya bayyana cewa ya kawo wannan tallafin ne saboda Allah don taimakawa marayun da ke ƙarƙashin kulawar wannan ƙungiyar a matsayin sadaka…
Read More
Gwamnatin Kebbi ta ja kunnen ‘yan kwangila kan bikin kamun kifi na Argungu 

Gwamnatin Kebbi ta ja kunnen ‘yan kwangila kan bikin kamun kifi na Argungu 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kira ga waɗanda aka bai wa kwangilar gyare-gyaren wuraren da za a gudanar da bikin al'adu da kamun kifi na Argungu da su hanzarta su kammala ayyukansu cikin lokaci. Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ne ya yi wannan kira a wani rangadin gani da ido a wuraren da za a gudanar da bukukuwan a garin Argungu. Sanata Umar Abubakar ya ce ya kamata 'yan kwangilar su yi aiki tuƙuru ba dare ba rana tare da tabbatar da sun yi aiki mai inganci bisa la'akari da ƙurarren…
Read More
Gobara ta ƙone ajijuwa 34 a makarantar kiwon lafiyar dabbobi ta Kano

Gobara ta ƙone ajijuwa 34 a makarantar kiwon lafiyar dabbobi ta Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata gobara da ta tashi ta ƙone ajijuwa 34 a Makarantar Kiwon Lafiyar Dabbobi da ke ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano. A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:53 na ranar Litinin. Jami’in ya ce ofishin kula da gobara ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Jamilu Abubakar, wanda ya bayar da rahoton tashin gobarar a cikin makarantar. Ya ce nan da nan aka tura ma’aikatan kashe gobara daga ofishinsu na Rijiyar Zaki zuwa wurin.…
Read More
Tallafin Amurka ga Nijeriya: Yaƙi da ta’addanci ya wuce amfani da makamai

Tallafin Amurka ga Nijeriya: Yaƙi da ta’addanci ya wuce amfani da makamai

Daga ƙarshen watan Disamba na shekarar 2025 zuwa makonnin farko na Janairu 2026, alamu sun fara bayyana na yiwuwar samun sauƙi a matsalar tsaro da ta addabi Nijeriya tsawon lokaci. Tsawon kusan shekaru biyu, ƙasar ta rayu cikin yanayi mai cike da fargaba da rashin tabbas, tamkar yadda masanin falsafa Thomas Hobbes ya siffanta rayuwar da ba ta da tsari da kariya. Yau dai, ana iya cewa haske ya fara bayyana, ko da yake har yanzu akwai sauran rina a kaba. Bayan harin sama da sojojin Amurka suka kai a daren Kirsimeti, wanda ya lalata wasu sansanonin ’yan ta’adda a…
Read More
Ranar Marubuta 2025: Wacce wainar aka toya tsakanin marubuta da manazarta?

Ranar Marubuta 2025: Wacce wainar aka toya tsakanin marubuta da manazarta?

"Jihar Katsina ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin taron Ranar Marubuta wanda za a yi na gaba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A karo na uku, marubuta da manazarta adabin Hausa daga sassan nahiyar Afirka da Nijeriya sun yi haɗuwar yaushe rabo, a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a ranar 31 ga watan Disamba, 2025, domin ƙarfafa zumunci da tattauna hanyoyin inganta rubutun Hausa, don a duba yadda za a samar da haɗin gwiwa tsakanin marubuta da mahukunta, da nufin gano bakin zaren warware matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da suke addabar wasu jihohin Arewa. An zaɓi a…
Read More
Patrice Lumumba: Gwarzon ’yancin ƙasar Congo

Patrice Lumumba: Gwarzon ’yancin ƙasar Congo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Patrice Emery Lumumba na daga cikin fitattun jaruman Afirka da suka yi gwagwarmaya wajen kwato ’yanci daga Turawan mulkin mallaka. Sunansa ya shiga tarihi a matsayin Firaminista na farko na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan samun ’yanci daga Belgium a shekarar 1960. Lumumba ya shahara wajen tsayuwa tsayin daka, kishin ƙasa da kuma adawa da danniya da cin zarafin Afirka. An haifi Patrice Lumumba a ranar 2 ga Yuli, 1925, a ƙauyen Onalua, cikin yankin Katanga na wancan lokaci a Belgian Congo (wanda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo). Ya fito ne daga ƙabilar Tetela. Tun yana…
Read More
Fahimtar juna ko soyayya: Wanne ginin aure ne ya fi ƙarko?

Fahimtar juna ko soyayya: Wanne ginin aure ne ya fi ƙarko?

Tare da BILKISU YUSUF ALI Gabatarwa Auren zamani na fuskantar barazana iri-iri. Sau da yawa muna jin "sun yi shekara biyu da aure, amma sun rabu" ko "aure ya tashi saboda rashin jituwa. “ta kasha mijinta alhali ita ta kawo shi ta ce “ta ji ta gani" “Satinmu biyu da aure amma ya fara faɗamin maganganu marassa daɗin ji” da sauran halaye da ma’aurata kan fuskanta kafin auren ya ci talata da laraba. Waɗannan lamura sun sa mutane da dama tambaya. Shin aure ya fi dorewa ne idan an fara da soyayya mai zafi, ko idan an gina shi bisa…
Read More