ukarofi

12661 Posts
Cutar Lassa a Nijeriya

Cutar Lassa a Nijeriya

Daga USMAN KAROFI A shekarar da ga gabata, hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa aƙalla mutane 215 suka rasa rayukansu a sanadin zazzaɓin cutar Lassa. Ga wanda ya ke bibiyar alƙaluman da kuma yanayi na yaɗuwar cutar zai san cewa wannan adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu dole hankali ya tashi. Alƙaluman da suka fito sun nuna cewa an samu waɗanda ake zargi da cutar aƙalla mutum 9389 wanda a cikinsu kuma a tabbatar da mutum 1148 sun kamu da cutar kuma a cikinsu a ka samu mutane 215 da suka rasu wanda…
Read More
An kammala ginin cibiyar Musulunci a Katsina

An kammala ginin cibiyar Musulunci a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Cibiyar musulunci da gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation ta gina a Unguwar Kadarko Estate cikin garin Katsina na ɗauke da katafaren masallacin Juma'a, makaranta da gidan liman. Shugaban ƙungiyar izalatul bidi'a wa iqamatul sunnah Sheikh Yakubu Musa Hassan ya sanar da cewa ana shirye shiryen buɗewa nan ba da jimawa ba. Sheikh Yakubu Musa wanda har ila yau shine shugaban gidauniyar Sauttus sunnah ya nuna gamsuwa da yadda akai ingantaccen aiki. Yayi kira ga al'ummar musulmi da su tashi tsaye wajen aikin Allah ta hanyar aiwatar da irin wannan aiki. Sheikh Yakubu Musa Hassan yayi…
Read More
Wani matashi ya halaka matar aure a Zamfara

Wani matashi ya halaka matar aure a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Wani matashi mai suna Hassan Ɗan Chanji, ya halaka wata matar aure mai suna Rakiyaya matar Malam Maikuddi a Garin Dambo dake ƙaramar hukumar Bakura a Jihar Zamfara. Wani mazaunin yankin Malam Tukur Dambo ya shaidawa wakilin mu ta wayar tarho a zantawar sa da Blueprint Manhaja cikin daren nan. Malam Tukur Dambo ya shaidawa wakilin mu cewar labarin ya faru ne da yammacin yau Laraba bayan da wanda ake zargin da matar da ya halaka su kayi sa'insa na cacar baki a tsakanin su. "A yayin sa'insar ne, sai ya shiga gida ya ɗauko…
Read More
Mutane sun gaji da gwamnatin APC – Dr Ibrahim Trader

Mutane sun gaji da gwamnatin APC – Dr Ibrahim Trader

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam'iyar adawa ta ADC Dr Junaidu Lawal Trader ya faɗawa manema labarai haka a wajan taron jam'iyar a Katsina. Ya ce matsalolin rashin tsaro, tabbatarwan ilimi ya lalace, harkar noma da tattalin arziki suka sanya mutane ke ruwa zuwa jam'iyar su ta ADC. "Kowa naji a jikin sa kan haka ne mutane ke neman makoma da ingancin rayuwa a jam'iyar mu ta ADC,"inji Junaidu Trader. Dr Junaidu ya bayyana cewa ganin irin mashahurai kuma adalan mutanen da suka shiga cikin jam'iyar su yana da tabbacin samun nasara…
Read More
Gwamnati ta bayyana gamsuwarta kan ingancin tagwayen hanyar Zaria-Funtua-Gusau-Sokoto

Gwamnati ta bayyana gamsuwarta kan ingancin tagwayen hanyar Zaria-Funtua-Gusau-Sokoto

Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau Gwamnatin tarayya ta nuna gamsuwarta kan ingancin ayyukan tagwayen hanyar da ta tashi daga Zaria zuwa Funtua, Gusau har zuwa Jihar Sokoto. Ministan ayyuka, Cif David Umahi ya yi wannan tsokaci da yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar gani da ido a ranar Talata, inda ya bayyana cewa an bayar da ayyukan ne a shekarar 2023. Ministan wanda babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan ayyukan al'umma a Arewa maso Yamma, Abdullahi Tanko Yakasai ya wakilta a lokacin rangadin, ya bayyana cewa za a samar da isasshen tsaro ga dukkan kamfanonin dake gudanar…
Read More
Dikko Raɗɗa ya tallafa wa mata 14,000 da kayan sana’o’i

Dikko Raɗɗa ya tallafa wa mata 14,000 da kayan sana’o’i

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina “Mata Sune ƙashin bayan al’umma. Inganta Rayuwarsu daidai yake da inganta rayuwar al’umma”Inji Raɗɗa Gwamna ya bayyana hakanne yayin ƙaddamar da babban shirin tallafa wa mata ’yan kasuwa guda 14,450 a Jihar Katsina. A wani muhimmin mataki na bunƙasa tattalin arzikin jihar Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin tallafa wa mata ’yan kasuwa 14,450 a faɗin jihar don dogaro da kansu. An tsara shirin ne domin tallafa wa mata da ke gudanar da sana’o’i daban-daban kamar sana’ar hannu, kasuwanci, noma, ɗinki, rini, sarrafa abinci da sauransu, waɗanda da dama daga cikinsu su ne…
Read More
Shaye-shaye: Wuta ce da ke cin ginin al’umma cikin sirri

Shaye-shaye: Wuta ce da ke cin ginin al’umma cikin sirri

Daga AISHA ASAS  'Idan ba ka koya wa yaro bin hanya ba, sai ka biyo shi da kuka a bayan titi.' Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A wannan mako, za mu yi dubiya ne kan ɗabi'a ta shaye-shaye wadda a can da ana mata kallon ɗabi’a ta 'yan iska, ko waɗanda ba su da mafaɗi. Saidai a yanzu ta zama ruwan dare, game gari, domin za ka iya samun ta har a wurin ɗalibai masu hazaƙa a ƙoƙarin ganin ba su faɗi jarrabawa ba su afka shaye-shaye da sunan maganin hana…
Read More
Ciwon haƙora da yadda za a magance shi

Ciwon haƙora da yadda za a magance shi

Daga AISHA ASAS  (Ci gaba daga makon jiya) A wasu lokuta rashin hasken haƙora kan zama matsala ga mai tare da shi, saboda sau da yawa idan aka kalli haƙoran sai a yi wa mai su kallon ƙazami, duk da cewa, yana wanke su yadda ya kamata.  Sau da dama akan bazama neman man wanke baki da ya dace da haƙoran, a namu tunanin rashin dace da man baki na ƙwarai ne ya janyo hakan. Sai dai abinda ba mu sani ba, wannan matsala ce da ke buƙatar a magance ta kamar kowacce, kafin a ga haƙoran a yanayin da…
Read More
Zuwa gare ku ma’abota haƙuri

Zuwa gare ku ma’abota haƙuri

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Zuwa gare ku, ya ma’abota haƙuri, ku da kuka zaɓi ku tsaya daram a kan gaskiya duk da tsanani, ku da kuka rungumi haƙuri a lokacin jarrabawa, ku da kuka yi imani cewa duk wani raɗaɗi da zubar hawaye ba zai tafi a banza ba a wajen Allah Maɗaukaki. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne domin girmama ku, domin tunatar da ku darajar haƙuri a Musulunci, da kuma ƙarfafa zuciyarku da kalaman Alƙur’ani da hadisai, waɗanda suka nuna cewa haƙuri ita ce hanya zuwa ga nasara ta gaskiya. Haƙuri ba kawai jurewa ba ne.…
Read More
Ikon Allah sai kallo

Ikon Allah sai kallo

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Cikin Suratul Waqi'a sai Allah ya tambaye mu cewa; Q56:58-59 "Shin kun ga abinda kuke fitarwa na maniyyi? Shin ku kuke halitta shi ko mu ne masu halittawa.” Wato Allah ya ja hankalinmu da mu yi nazarin maniyyi domin gano asalin yadda mu ka faro da kuma gwanintar halittarsa. Da farko dai idan bayan namiji ya sadu da mace ya dura mata maniyyinsa, to a cikin maniyyin akwai kwayoyin Mani kimanin miliyan 75 a duk yawan Mani da zai kai cikin cokali guda, wato 5 milliliters kenan. Kowane daya cikin wadannan kwayoyin maniyyi idan ya sami…
Read More