ukarofi

12661 Posts
An gargaɗi masu sarautar gargajiya da su zauna lafiya da al’ummarsu

An gargaɗi masu sarautar gargajiya da su zauna lafiya da al’ummarsu

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Danmakwayon Kano kuma Sakataren Masarautar Kano, Hakimin Dawakin Kudu, Alhaji Yusuf Kabir, ya gargaɗi masu riƙe da sarautar gargajiya da su rungumi ɗabi’ar zaman lafiya da al’ummarsu domin samar da cigaba mai ɗorewa a yankunansu. Ya yi wannan gargaɗi ne a lokacin da yake naɗa wasu sabbin masu sarautar gargajiya da wani mai unguwa a fadarsa da ke Dawakin Kudu, a ranar Lahadin da ta gabata.  Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Yunusa Magaji a matsayin Sarkin Askar Dawakin Kudu, Idris Aminu a matsayin Sarkin Noman Dawakin Kudu, da Hamza Ado Abdullahi a matsayin…
Read More
Dalibai 160 sun kammala haddar Alƙur’ani a Tsangayar Sheikh Bala Lau a Jalingo

Dalibai 160 sun kammala haddar Alƙur’ani a Tsangayar Sheikh Bala Lau a Jalingo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dalibai 160 ne suka kammala haddar Alƙur’ani Mai Tsarki a Tsangayar Haddar Alƙur’ani ta Sheikh Bala Lau da ke birnin Jalingo na Jihar Taraba. An gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a harabar babbar cibiyar ƙungiyar Musulunci ta Jihar Taraba a ranar Lahadin da ta gabata, inda manyan malaman addinin Musulunci daga ciki da wajen jihar suka halarta. A jawabin da ya gabatar, Sheikh Bala Lau, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Izalatul Bid’ah Wa Iƙamatus Sunnah mai hedkwata a Kaduna, ya jaddada muhimmancin bai wa matasa ilimin addini haɗi da na zamani, yana cewa…
Read More
Shugaban NAHCON ya kammala ziyarar shirye-shiryen aikin Hajjin bana a Saudiyya 

Shugaban NAHCON ya kammala ziyarar shirye-shiryen aikin Hajjin bana a Saudiyya 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya kammala ziyara ta biyu ta shirye-shiryen aikin Hajjin bana. Ziyarar ta gudana daga 4 zuwa 19 ga Janairu, 2026, inda aka mayar da hankali kan ƙarfafa tsare-tsaren aiki, da inganta haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya, tare da daidaita masu ba da hidima daga Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki domin su dace da ƙa’idoji da jadawalin Saudiyya. A sanarwar da Ahmad Muazu, mataimaki na musamman ga shugaban NAHCON kan yaɗa labarai ya fitar a ranar Talata,  yayin ziyarar, tawagar NAHCON ta gana…
Read More
An gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa

An gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar Operation Haɗin Kai ta Sojin Nijeriya ta sanar da gano wani wuri da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ke ɓoye man fetur, magunguna da sauran kayayyakin aikinsu a ƙarƙashin ƙasa. Samun wannan nasarar na zuwa ne bayan jerin samamen da dakarun rundunar Operation Desert Sanity suka kai a yankunan Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno. Bayanai sun nuna cewa an kai samamen ne bayan hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka kai a ranar Lahadi a Chilaria, Garin Faruk da Abirma, inda dakarun suka yi nasarar daƙile hare-haren, ciki har da waɗanda aka kai da…
Read More
‘Zinariyar Arewa’ ta biya wa mutumin da aka kashe wa iyalai bakwai a Kano aikin Hajji

‘Zinariyar Arewa’ ta biya wa mutumin da aka kashe wa iyalai bakwai a Kano aikin Hajji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata attajira kuma ’yar gwagwarmaya, Hajiya Bilkisu Sulaiman Fema, ta biya wa Malam Haruna Bashir, magidancin nan da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida a Kano kujerar Aikin Hajjin bana. Fitaccen lauyan nan ɗan asalin jihar Kano kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Barista Abba Hikima Fagge, ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata. Ya ce, “Haj. Bilkisu Suleiman Fema wadda aka fi sani da Zinariyar Arewa, ta biya wa Mal. Haruna Bashir kujerar aikin Hajji, ta aika min da N200K a…
Read More
Ranar ‘yan mazan jiya: Tsofaffin sojoji sun koka, sun nemi ƙarin tallafi a Kano

Ranar ‘yan mazan jiya: Tsofaffin sojoji sun koka, sun nemi ƙarin tallafi a Kano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Ranar 15 ga watan Janairu na kowacce shekara rana ce da aka ware domin tunawa da tsofaffin sojoji, wato ‘Yan Mazan Jiya, waɗ anda suka fafata a Yaƙ in Duniya na Farko da na Biyu, Yaƙin Basasar Nijeriya, da kuma waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a fannonin tsaro domin kare martabar ƙasa. Tun da fari, ana gudanar da wannan biki ne a ranar 11 ga watan Nuwamba, wadda aka fi sani da Poppy Day (11-11), musamman a ƙasashen Turai. Sai dai sakamakon tarihi da kuma kawo ƙarshen yaƙin Basasar Nijeriya a ranar 15 ga…
Read More
Dabi’un Marigayi Malam Kabiru Na’ibi abubuwan koyi ne – Salisu Muƙaddas

Dabi’un Marigayi Malam Kabiru Na’ibi abubuwan koyi ne – Salisu Muƙaddas

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An bayyana kyawawan ɗabi’u da halayen marigayi tsohon Na’ibin Limamin Dawakin Kudu, Ustaz Malam Kabiru Yahaya, a matsayin abin koyi ga al’umma, musamman matasa masu tasowa. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Alhaji Salisu Abdullahi Dawakin Kudu, Mukaddamin Hakimin Gundumar Darmanawa, a sakon ta’aziyyarsa bayan rasuwar malamin, wadda ta faru a ranar Juma’a da ta gabata bayan doguwar jinya. Alhaji Salisu ya bayyana rasuwar Malam Kabiru a matsayin babban rashi ga garin Dawakin Kudu, yana mai cewa gudunmawar da marigayin ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da tarbiyyar al’umma ba za a taɓa…
Read More
Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, ya cika shekaru 25 a kan mulki

Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, ya cika shekaru 25 a kan mulki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An gudanar da bikin cika shekaru ashirin da biyar da naɗa Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, a kan mulki, a fadarsa da ke garin Gama, ƙaramar hukumar Nasarawa, a ranar Lahadi. Dagacin Gama ya bayyana godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa ba shi damar kai wannan matsayi na shekaru 25 yana jagorantar al’ummarsa. Ya ce wannan nasara babbar ni’ima ce da ke nuna rahamar Allah da goyon bayan al’umma. Alhaji Rabiu Isyaku ya bayyana farin cikinsa bisa yadda ake zaman lafiya da jituwa a yankin Gama duk da kasancewar al’umma masu kabilu daban-daban. Ya ce…
Read More
Gwamnatin Kano za ta ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyi

Gwamnatin Kano za ta ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyi

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU aKano Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa da duk wata kungiya da ke da manufar bunƙ asa rayuwar al’umma a faɗin jihar.  Darakta Janar ta Hukumar Bincike da Adana Bayanai ta jihar, Dr. Asma’u Jibrin, ce ta bayyana hakan yayin da take karɓar lambar girmamawa daga ƙungiyar Kwankwasiyya Media Production, tare da wasu masu bai wa Gwamnan Jihar shawara, a Ma’aikatar Yaƙi da Talauci da Jinƙan Al’umma, a ranar Litinin da ta gabata. Dr. Asma’u Jibrin ta bayyana cewa ƙungiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma,…
Read More
’Yan Nijeriya sun sha barasar tiriliyan N1.54 a wata tara

’Yan Nijeriya sun sha barasar tiriliyan N1.54 a wata tara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Manyan kamfanonin giya a Nijeriya sun samar da jimillar kuɗaɗen shiga sama da tiriliyan N1.54 daga sayar da giya da sauran abin sha marasa giya cikin watanni tara na farkon shekarar 2025. Alƙaluman dai na nuna adadin kuɗin da ’yan Nijeriya suka kashe wajen sayen kayayyakin giya a wannan lokaci. A cewar bayanan kuɗi da ba a tantance ba na kamfanonin giya na Nigerian Breweries, International Breweries, da Champion Breweries Plc na watanni tara da suka ƙare a ranar 30 ga watan Satumba, 2025, kamfanonin sun samu babban ci gaba ta sayar da giya.…
Read More