25
Jan
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata muhawara mai zafi ta barke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar Manyan Dattawan Arewa (NEF) kan batun wani kamfanin tace zinari da ake zargin ana ginawa a jihar Legas, bayan da ƙungiyar ta zargi gwamnati da karya ƙa’idojin adalci da raba albarkatu a ƙasar. ƙungiyar NEF ta yi wannan zargi ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 18 ga Janairu, 2026, inda ta ce kafa abin da ta kira “Babban Matatar Zinari ta ƙasa” a Legas ba daidai ba ne, ganin cewa mafi yawan ma’adinan zinari da ake haƙowa na Arewa ne.…
