25
Jan
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ta kama wani mutum mai suna Suleman Mamuda, mai shekaru 30 a duniya bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a ƙauyen Bayawa da ke ƙaramar Hukumar Augie. Rundunar ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da fartanya wajen dukan matarsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta. Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya ce bayan faruwar lamarin mutumin ya tsere, amma daga baya ’yan sanda suka gano inda ya ɓuya biyo bayan wasu bayanan da suka samu. Ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya bayar da umarnin a miƙa…
