ukarofi

12661 Posts
Imam Abdullahi Abubakar: Daga mai sha’awar shiga soja zuwa jarumin ceton al’umma

Imam Abdullahi Abubakar: Daga mai sha’awar shiga soja zuwa jarumin ceton al’umma

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ranar 15 ga watan Janairu na kowacce shekara na kasancewa Ranar Tunawa Da Mazan Jiya a Nijeriya, domin yabawa da gudummawar da dakarun sojojin ƙasar nan suka bayar a fagagen fama daban-daban. Wannan rana harwayau ta kasance baƙar rana da al'ummar Jihar Filato, wacce ba za su taɓa mantawa da ita ba, kasancewar ita ce ranar da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na ƙauyen Yelwan Gindin Akwati, a yankin Nghar da ke ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ya yi bankwana da duniya. Malam Abdullahi ya rasu ne a Asibitin ƙwararru na Jihar Filato bayan ya yi fama…
Read More
‘Yan sanda sun kama shugaban makarantar sakandare a Katsina da zargin sata

‘Yan sanda sun kama shugaban makarantar sakandare a Katsina da zargin sata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a wata takardar sanar wa. Ya ce ofishin 'yan sanda na garin Dutsi a ƙaramar hukumar Dutsi suka sami bayanan sirri gama da fasa wani ɗakin kayan gwaje-gwaje a wata makarantar sakandare da ke yankin. Ko da 'yan sanda suka isa wajen sun tarar da an ɓalle ɗakin kayan tare da sace na'ura mai samar da wutar lantarki (solar) da wasu kayayyaki amma an bar safan hannu. DSP Abubakar Sadiq ya cigaba da cewa bincike da yan sanda…
Read More
Dikko Raɗɗa ne ɗan takarar gwamnan mu a zaɓen 2027 – Nasiru Yahaya Daura

Dikko Raɗɗa ne ɗan takarar gwamnan mu a zaɓen 2027 – Nasiru Yahaya Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya faɗi haka a taron gangamin da jam'iyar APC na ƙaramar hukumar Daura ta shirya. Ya ce duba da ayyukan da gwamna Raɗɗa ya aiwatar a faɗin jihar yasa al'ummar ƙaramar hukumar Daura suka shirya waɗannan taron jaddada goyon bayan sake takarar gwamnan. Kakakin majalisar ya bayyana cewa ɗaukacin al'ummar ƙaramar hukumar Daura da suka haɗa da matasa, 'yan kasuwa,maza da mata sun shaida cewa gwamna Dikko Raɗɗa zasu yi a 2027. "Bamu da wani Ɗan takarar sai Dikko Raɗɗa,bamu da wata jami'ya sai APC…
Read More
A zamantakewar aure an fi ɗora wa mata laifi fiye da maza – Fatima Gwadabe

A zamantakewar aure an fi ɗora wa mata laifi fiye da maza – Fatima Gwadabe

"Rashin sana'ar yi ga mace musamman matar aure ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba" Daga AYSHA ASAS Hajiya Fatima Umma Salisu Gwadabe, mace mai neman na kanta a ɓangaren sana'ar sayar da abinci, wadda ta kafa yara kuma ta koyar da su sana'ar don su ma su dogara da kansu. A wannan makon jaridar Blueprint Manhaja ta samu damar tattaunawa da ita don jin wasu batutuwa da suka shafi irin sana'ar da yadda sana'ar ke da tasiri a rayuwar matan aure. Sannan mun taɓo ɓangaren rayuwarta. Kuma za ku ji irin shawarwarin da ta ba wa mata…
Read More
Za a kammala aikin tagwayen hanyar Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zaria a shekarar 2028 – Goronyo

Za a kammala aikin tagwayen hanyar Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zaria a shekarar 2028 – Goronyo

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin tarayya ta ce, za a kammala aikin tagwayen hanyar Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zariya a shekarar 2028. Karamin Ministan ayyuka, Bello Mohammed Goronyo ya yi wannan tsokaci a wata hira da manema labarai a Garin Bungudu hedikwatar ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara a yau Lahadi. A cewar sa, ziyarar gani da ido na gina hanyar ta Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zariya wanda ma'aikatar sa ta yi, ya biyo bayan umarnin ministan ayyuka, David Umahi, da nufin duba ayyukan da 'yan kwangilar da ke kula da aikin ke yi da kuma tabbatar da ayyukan cikin sauri da…
Read More
NUJ a Katsina ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na SWAN/Dikko Raɗɗa Cup

NUJ a Katsina ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na SWAN/Dikko Raɗɗa Cup

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wasan wanda NUJ ta samu nasarar zura ƙwallo 1-0 akan abokiyar karawarta ta ƙungiyar malaman lafiya MHWUN ya basu damar lashe kofin. Kwamishinan harkokin wasanni da cigaban matasa Eng Surajo Yazid Abukur ya miƙa kofin ga ƙungiyar da ta samu nasara. Da yake jawabi a lokacin taron, kwamishinan ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Katsina na ƙoƙari wajen ganin an samar ma matasa abun yi ta ɓangaren wasanni domin su dogara da kansu a faɗin jihar. Yayi addu’a da fatan alheri ga dukkanin mahalarta musamman ƙungiyar NUJ da suka samu nasara. Gadan cin wannan kofi shine…
Read More
Jami’ar Alƙalam ta karrama Aminu Bello Masari da digirin girmamawa

Jami’ar Alƙalam ta karrama Aminu Bello Masari da digirin girmamawa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'ar da ta gudanar da bikin yaye ɗailabai guda 1109 ta kuma karrama mataimakin shugaban Jamaatul Nasarul Islam JNI jihar Imo, Malam Ezeh Abdulfatah Chimeaze Emetumah III shima da digirin girmamawa. A ranar Asabar 24 ga Janairun 2026, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD, ya halarci taron yaye ɗaliban Jami’ar Al-Qalam Katsina, karo na 17, inda makarantar ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, da kuma Ezeh Abdulfatah Chimaeze Emetumah na III da digirin digirgir na girmamawa. A jawabin da ya gabatar a wajen taron, gwamna Raɗɗa ya fara…
Read More
Gwamnan Kano ya yi kira ga masu amfani da kafafen sadarwa na zamani da su gudanar da aikin su cikin tsafta

Gwamnan Kano ya yi kira ga masu amfani da kafafen sadarwa na zamani da su gudanar da aikin su cikin tsafta

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga masu tasiri a kafafen sada zumunta musamman magoya bayan gwamnatin da ke kan mulki da su tabbatar cewa abubuwan da suke wallafawa na kasancewa cikin alhaki, girmamawa da mutunci, domin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban al’umma. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar. Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Yusuf ya yi wannan kira ne yayin Shirin tallafa wa masu tasiri a kafafen sadarwa ta hanyar raba…
Read More
Gwamna Yusuf ya gargaɗi masu tasiri a kafafen sada zumunta kan cin zarafin Sanata Kwankwaso

Gwamna Yusuf ya gargaɗi masu tasiri a kafafen sada zumunta kan cin zarafin Sanata Kwankwaso

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya gargaɗi masu tasiri a kafafen sada zumunta da masu sharhin siyasa da su guji yin kalamai na raini ko tayar da zaune tsaye kan Jagoran Tafiyar Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Gwamnan ya yi wannan gargadi ne a ranar Juma’a yayin raba babura 600 ga masu tasiri a kafafen sada zumunta, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Kano. Gwamna Yusuf ya bayyana Sanata Kwankwaso a matsayin jagora da gudummawarsa ga cigaban siyasa da tattalin arziƙin Jihar Kano ke da matuƙar girma, tare da jaddada cewa…
Read More
Matashi ya yi facaka da kuɗi a kwana guda bayan banki ya yi kuskuren tura masa biliyan N1.3

Matashi ya yi facaka da kuɗi a kwana guda bayan banki ya yi kuskuren tura masa biliyan N1.3

Abin da ya faru da Ojo Kingsley ya yi kama da labarin fim mai cike da al’ajabi. A rana guda, kuskuren tsarin banki ya sauya rayuwarsa gaba ɗaya, inda First Bank ta tura masa sama da naira biliyan 1.3 bisa kuskure. Maimakon ya sanar da bankin ko ya mayar da kuɗin, Kingsley ya ɗauki matakin da ya jefa shi cikin mummunar masifa. Bayan samun kuɗin, nan take ya rarraba wani kaso mai yawa zuwa asusun mahaifiyarsa, Itohan Ojo, da kuma ‘yar uwarsa, Edith Okoro Osaretin. Bai tsaya nan ba, ya kuma kashe wani ɓangare wajen kammala ginin gidansa, sannan ya…
Read More