ukarofi

12663 Posts
Kotu ta ƙi dakatar da ƙaramin Ministan Man Fetur daga raba rijiyoyin mai

Kotu ta ƙi dakatar da ƙaramin Ministan Man Fetur daga raba rijiyoyin mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da aka shigar domin hana ƙaramin Ministan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur (ɓangaren Mai), Heineken Lokpobiri, da wasu hukumomi raba wasu rijiyoyin mai da filayensa, inda kotun ta umurci waɗanda ake ƙara da su fito su bayyana dalilin da ya sa ba za a amince da buƙatar ba. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke wannan hukunci yayin sauraron buƙatar gaggawa da kamfanonin mai na Hi-Reɓ da Hi-Reɓ Eɗploration and Production suka shigar, ta hannun lauyansu Ambrose Unaeze. A maimakon bayar da umarnin dakatarwa, kotun ta umurci…
Read More
’Yan jarida bakwai sun rasu a hatsarin mota a Gombe

’Yan jarida bakwai sun rasu a hatsarin mota a Gombe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni sun tabbatar da mutuwar ’yan jarida bakwai sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Jihar Gombe. Hatsarin ya rutsa da wata mota ƙirar bas ta ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), wacce ta ke ɗauke da ’yan jaridar, yayin da suke dawowa daga bikin auren wani abokin aikinsu da aka yi a ƙaramar Hukumar Kaltungo ta Jihar Jigawa. Bayan kammala bikin cikin nasara, motar ta NUJ ta samu matsala a kan hanya a kusa da garin Kumo da ke ƙaramar Hukumar Akko, inda tayar motar ta fashe a lokacin da suke dawowa.  Lamarin…
Read More
NUJ ta karrama tsofaffin shugabanni da gogaggun ’yan jarida a Kano

NUJ ta karrama tsofaffin shugabanni da gogaggun ’yan jarida a Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen Wakilan Jaridu na Jihar Kano, ta gudanar da taron bayar da lambobin yabo na shekarar 2025 a ranar Lahadi, inda ta karrama tsofaffin shugabanninta, gaogaggun mambobi da kuma abokan ƙungiyar da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga aikin jarida da hidimar al'umma. An gudanar da taron cikin dandali mai armashi a Tahir Guests Palace da ke Nasarawa GRA, Kano, inda ‘yan jarida, jami’an gwamnati, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar suka halarta. Rahotanni sun nuna cewa taron ya zama wata dama ta…
Read More
Jigawa: Mutane 11 sun rasu bayan mota ta yi karo da bishiya

Jigawa: Mutane 11 sun rasu bayan mota ta yi karo da bishiya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu tara suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis, 25 ga Disamba, 2025, a ƙauyen Bagewu da ke ƙaramar Hukumar Ringim ta jihar. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin ya shafi wata jajayen mota ƙirar ɓolkswagen Golf 3 mai lambar rajista LNG 983 ɗA daga Jos.…
Read More
Lauyoyi 28 suka tsallake gwajin nagarta yayin naɗa alƙalan Kotun Tarayya

Lauyoyi 28 suka tsallake gwajin nagarta yayin naɗa alƙalan Kotun Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla lauyoyi 28 ne daga cikin 62 waɗanda aka tsayar domin naɗa su a matsayin alƙalan Kotun Tarayya ta Nijeriya suka tsallake gwajin mutunci da Hukumar Kula da Shari’a ta ƙasa (NJC) ta kafa, yayin da wasu 34 suka faɗi gwajin sakamakon koke-koken da aka shigar kansu, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar. Rahotanni sun nuna cewa lauyoyi 62 ne gaba ɗaya suka shiga jarrabawar kwamfuta (CBT) da Kotun Tarayya ta gudanar, kuma aka tura sunayensu zuwa Hukumar Ayyukan Shari’a ta Tarayya (FJSC). Sai dai bisa sabon tsari da NJC ta amince da shi a ƙarƙashin Babbar…
Read More
2027: Shiga APC ba zai sa samun tikitin tazarce a 2027 ba – Wike

2027: Shiga APC ba zai sa samun tikitin tazarce a 2027 ba – Wike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gargaɗi 'yan siyasa cewa shiga APC ko nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu ba ya nufin tabbacin samun tikitin wa’adi na biyu kai tsaye. Wike ya yi wannan gargaɗin ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ƙaramar Hukumar Emohua da ke jihar Ribas, a wani bangare na ziyarce-ziyarcensa na tuntuɓar jama'a a faɗin jihar. Ministan, ya samu tarbar Shugaban ƙaramar Hukumar Emohua, Chidi Lloyd, tare da sarkin gargajiya Sergeant Awuse da sauran shugabannin jam’iyya. A cewarsa, dole ne ƙabilar Ikwerre ta ci gaba da kasancewa mai…
Read More
NUT ta karrama shugabannin ƙananan hukumomi da na sashen ilimi a Dawakin Kudu

NUT ta karrama shugabannin ƙananan hukumomi da na sashen ilimi a Dawakin Kudu

Daga SUULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Kungiyar Malaman Makarantu ta ƙasa (NUT) reshen ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta karrama Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai-Rago, da Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, tare da Shugaban Sashen Ilimi na Dawakin Kudu, Musa Sani Yankatsare, Shugaban NUT na Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, da wasu malamai bisa nuna hazaka, jajircewa da kulawa ga harkar ilimi. Da yake jawabi a yayin bikin karramawar, Shugaban NUT na Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya ce ya zama wajibi ga ƙungiyar su karrama waɗannan shugabanni la’akari da irin gudunmawar…
Read More
’Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar Ogun a masallaci

’Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar Ogun a masallaci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ƙaramar Hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata. Musa, wanda ya taɓa zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ƙarfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa. Shugaban ƙaramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a…
Read More
Kano ce kan gaba wajen ƙirƙire-ƙirƙiren injinan sarrafa kayan amfanin gona a Nijeriya — Dakta Tukur Minjibir

Kano ce kan gaba wajen ƙirƙire-ƙirƙiren injinan sarrafa kayan amfanin gona a Nijeriya — Dakta Tukur Minjibir

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Mai ba Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shawara kan harkokin noma, Dakta Tukur ɗayyabu Minjibir, ya bayyana cewa Jihar Kano ce ke kan gaba a Nijeriya  wajen ƙirƙire-ƙirƙire da samar da injinan sarrafa kayan amfanin gona na zamani. Dakta Minjibir ya bayyana hakan ne yayin taron noma da fasahar sarrafa amfanin gona na NAMIS’25, wanda ƙungiyar Connection of Stakeholders in Agricultural Mechanization (CONESAM) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Mista Teddy Eragbai. Taron, wanda Kano ta karɓi baƙuncinsa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna ƙima da darajar Kano a fannin noma da…
Read More
Kaunar talaka da cikakken adalci ne sirrin farin jinin Sarkin Gumel — Umar Danwasha

Kaunar talaka da cikakken adalci ne sirrin farin jinin Sarkin Gumel — Umar Danwasha

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban ƙungiyar Masarautar Gumel kuma ma’ajin ƙungiyar a Jihar Jigawa, Malam Jafar Umar ɗan Washa, ya bayyana cewa ƙaunar talakawa da cikakken adalci su ne manyan dalilan da suka sa Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani Mailautai, ke da farin jini da karɓuwa a tsakanin al’ummarsa da ma Nijeriya  baki ɗaya. Ya ce tun bayan da marigayi tsohon Gwamnan Kano, Alhaji Abubakar Rimi, ya naɗa Sarkin Gumel a shekarar 1985, masarautar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda bai taɓa jin ƙorafi ko bore daga talakawa ba, sai dai nuna ƙauna da biyayya. Malam…
Read More