ukarofi

12663 Posts
Kungiyar ’Yan Tifa ta buƙaci Gwamnatin Kano ta kawo mata ɗauki

Kungiyar ’Yan Tifa ta buƙaci Gwamnatin Kano ta kawo mata ɗauki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD Hadaddiyar ƙungiyar ’Yan Tifa da dangoginta na ƙasa, reshen jihar Kano ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kano ta taimakawa yan ƙungiyar ta ba su motocin Tifa bashi a cikin sauwin kuɗi da za su riƙa biya a hankali hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkokinsu da samawa matasa aiki.  Shugaban ƙungiyar na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Shafi'i Zainawa ya bayyana hakan da yake zantawa da ’yan jarida a wajen taron ranar ma'aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata. Ya yi nuni da cewa idan aka yi la'akari da…
Read More
Sojoji sun cafke mai kitsa hare-haren boma-bomai da wasu a Borno

Sojoji sun cafke mai kitsa hare-haren boma-bomai da wasu a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun rundunar sojoji ƙarƙashin jagorancin atisayen Haɗin Kai (OPHK), sun yi nasarar kama Shariff Umar da ake kira da Yusuf, wanda ake ganin shi ne mai alhakin shirya hare-haren tayar da boma-bomai da ƙulla makirce-makirce a Borno da wasu jihohin Arewa ta Gabas. Jami'in yaɗa labaran jami'an haɗaka na atisayen a yankin, Laftanal Kanal Sani Uba ne ya sanar da haka a wata takarda ranar Asabar a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno. A cewarsa, bincike ya nuna cewa Umar na taka muhimmiyar rawa wajen ɗauka, bada horo da aika 'yan ƙunar baƙin-wake. Haka kuma…
Read More
Ministan Labarai ya yi jimamin ‘yan jarida bakwai da suka rasu a Gombe sakamakon hatsari

Ministan Labarai ya yi jimamin ‘yan jarida bakwai da suka rasu a Gombe sakamakon hatsari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa da alhini akan rasuwar wasu ‘yan jarida guda bakwai a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a yankin Gombe ta Kudu da ke Jihar Gombe, a ranar Litinin da ta gabata. Al'amarin ya faru ne da yammacin Litinin yayin da ‘yan jaridar suke dawowa daga bikin auren wani abokin aikinsu da aka yi Ƙaramar Hukumar Kaltungo, wanda ma'aikatacin gidan talbijin na NTA ne. A cewar bayanan farko daga Kwamandan Sashen Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) a Jihar Gombe,…
Read More
Gwamnan Gombe ya ba iyalan ‘yan jarida bakwai da suka rasu a hatsarin mota miliyan N14

Gwamnan Gombe ya ba iyalan ‘yan jarida bakwai da suka rasu a hatsarin mota miliyan N14

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Gombe ta gabatar da Naira miliyan 14 ga iyalan 'yan jaridar nan guda bakwai da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan jaridar sun rasu ne a ranar Litinin yayin komawa gida daga bikin wani abokin aikinsu da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kaltungo da ke jihar. Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatinsa, Farfesa Abubakar Njodi ne ya gabatar da tallafin miliyan N2 ga kowane iyalan da iftila'in ya shafa a Gombe, ranar Juma'a. Njodi ya bayyana cewa,…
Read More
INEC ta musanta fitar da jaddawalin zaɓen 2027

INEC ta musanta fitar da jaddawalin zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa ta fitar da jaddawali da tsarin ayyukan babban zaɓen 2027. A sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Juma'a ta hannun Sakataren labarai kuma mai ba Shugaban INEC shawara akan lamuran yaɗa labarai, Adedayo Oketola, hukumar ta ce rahoton ba gaskiya ba ne kuma abu ne aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a. Inevitable ta jaddada cewa, ba ta fitar da kowane jaddawali ko tsarin ayyuka dangane da babban zaben 2027 ba zuwa yanzu. Ta ce, tana…
Read More
Majalisar Dokoki ta fitar da bayanan sabuwar dokar haraji ga jama’a don nazari

Majalisar Dokoki ta fitar da bayanan sabuwar dokar haraji ga jama’a don nazari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da sabuwar dokar haraji a Nijeriya, Majalisar Dokoki ta fitar da kwafin bayanan da dokokin suka ƙunsa don amfanin masu buƙata acikin al'umma da ɓangarorin haɗaka. A ranar Alhamis ne Akawon majalisar, Barista Kamoru Ogunlana ya sanar da haka ta wata takarda da Daraktan yaɗa labarai, Bullah Audu Bi-Allah ya fitar. Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon kiraye-kirayen wasu daga cikin ƴan Nijeriya da ke neman yadda za a tantance sahihancin saƙonnin da ake yaɗawa game da sabuwar dokar harajin. Ogunlana ya ce, hakan zai…
Read More
Wasu jihohin na shirin karɓar bashin tiriliyoyin Naira don cike kasafin 2026

Wasu jihohin na shirin karɓar bashin tiriliyoyin Naira don cike kasafin 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla jihohi goma a Nujeriya na shirin tara kimanin naira tiriliyan 4.287 ta hanyar karɓar bashin banki, fitar da takardun bashi, tallafi, kuɗaɗen shiga na musamman da kuma haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, domin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Wannan na nuna ƙaruwar matsin lambar kuɗi da ke fuskantar gwamnatocin jihohi. Rahoton News Point Nigeria ya nuna cewa jihohin Legas, Abia, Ogun, Enugu, Osun, Delta, Sakkwato, Edo, Bayelsa da Gombe sun gabatar da jimillar kasafin kuɗi naira tiriliyan 14.174 ga majalisun dokokinsu, kamar yadda nazarin takardun…
Read More
NDLEA ta kama tsohon fursuna da hodar iblis cikin ledar sitaci

NDLEA ta kama tsohon fursuna da hodar iblis cikin ledar sitaci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wani tsohon fursuna mai suna Nwobodo Chidiebere Basil tare da wasu jami’an dakon kaya uku, bisa zargin yunƙurin fitar da hodar iblis zuwa ƙasar Birtaniya ta hanyar ɓoye ta a cikin kwalayen sitacin ruwa. NDLEA ta bayyana cewa an gano leda 75 na hodar iblis masu nauyin kilogiram 1.50, da aka ɓoye a cikin jakunkunan sitaci da aka rufe su daga masana’anta, a wajen fitar da kaya na Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed, Ikeja a Jihar Legas. A wata…
Read More
Ba za a tsawaita wa’adin sake gina jarin kamfanonin inshora ba – NAICOM

Ba za a tsawaita wa’adin sake gina jarin kamfanonin inshora ba – NAICOM

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Harkokin Inshora ta ƙasa (NAICOM) ta jaddada matsayinta na cewa ba za ta tsawaita wa’adin sake gina jarin kamfanonin inshora ba, tana mai cewa duk wani kamfani mai tsananin niyya da muhimmanci a harkar, ya kamata ya iya cika sharuɗɗan kafin ranar da aka ƙayyade. Babban Kwamishinan Inshora na ƙasa, Olusegun Ayo Omosehin, ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida kan inshora a Abuja. Ya ce wa’adin sake gina jarin, wanda aka sanya zuwa ranar 30 ga Yuli, 2026, ya samo asali ne kai tsaye daga Dokar Gyaran Masana’antar…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta yafe wa NNPC bashin tiriliyan N7.58

Gwamnatin Tinubu ta yafe wa NNPC bashin tiriliyan N7.58

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da soke wani gagarumin kaso na bashin da Asusun Tarayya ke bin Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), matakin da ya zo bayan kammala tantance bayanai da daidaita alƙalumma tsakanin ɓangarorin biyu. Matakin ya soke bashin da ya kai kimanin dala biliyan 1.42, daidai da Naira tiriliyan 2.059, tare da wani ƙarin bashin Naira tiriliyan 5.57, wanda gaba ɗaya ya kai Naira tiriliyan 7.58. Wannan na nuni da babban sauyi a kan nauyin bashin da NNPC ke ɗauke da shi ga baitul-malin ƙasa. Rahotanni sun bayyana…
Read More