ukarofi

12663 Posts
An kama malamin addini bisa zargin hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

An kama malamin addini bisa zargin hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana zargin wani fitaccen malamin addinin Muslunci da ke zaune a garin Zariya, Sheikh Sani Khalifa, da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu da wasu sojoji suka yi yunƙuri a kwanakin baya.Kuma yanzu haka ya shafe kusan kwanaki 23 a tsare a hannun jami’an tsaro.Majiyoyi da dama da suke da masaniya kan lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa, an kama Sheikh Khalifa ne jim kaɗan bayan tasowarsa daga Zariya zuwa Abuja domin neman ba’asin rufe masa asusun bankin da aka yi. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Nijeriya ta musanta yunƙurin…
Read More
Ababen da suka faru a satin bankwana da shekarar 2025 a masana’antun fina-finai na duniya

Ababen da suka faru a satin bankwana da shekarar 2025 a masana’antun fina-finai na duniya

Daga AISHA ASAS  A daidai lokacin da duniya ke bidirin shirye-shiryen karɓar sabuwar shekara, tare da bankwana da shekarar 2025, shafin Taurari ya yi duba da ababen da suka faru a satin ƙarshe na bankwana da shekarar 2025 da zumar taya makaranta masu bibiyar shafin namu murnan sabuwar shekara, tare da fatan Allah Ya sa ta zo mana da tarin alkhairai da kuma silar kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke adabar ƙasarmu. HOLLYWOOD: Avatar: 'Fire and Ash' ya sake girgiza duniya, tare da dawo da mulkin Cameron Masana’antar shirya fina-finai ta Hollywood ta shiga ƙarshen shekara da gagarumar nasara, yayin…
Read More
Yadda ƙaruwar kuɗaɗen Asusun Tarayya ya taimaka wa jihohi rage dogaro da rancen banki

Yadda ƙaruwar kuɗaɗen Asusun Tarayya ya taimaka wa jihohi rage dogaro da rancen banki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihohi da ƙananan hukumomi a Nijeriya sun samu gagarumin sauƙi a nauyin bashin bankuna, bayan sun biya kusan Naira Biliyan 547.5 cikin shekara guda, sakamakon ƙaruwar kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Tarayya (FAAC).  Wannan ci gaban na nuni da wani sabon salo a tafiyar kuɗin gwamnatocin ƙananan matakai, inda aka fara fifita rage bashi maimakon dogaro da tsadar rance daga bankuna. Bayanai daga sabon rahoton ƙididdigar Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa jimillar bashin da bankuna ke bin jihohi da ƙananan hukumomi ya ragu daga naira tiriliyan 2.68 a watan Yunin 2024 zuwa naira…
Read More
’Yan Nijeriya sun yi amfani da terabayit miliyan 1.236 na data a Nuwambar 2025 – NCC

’Yan Nijeriya sun yi amfani da terabayit miliyan 1.236 na data a Nuwambar 2025 – NCC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Amfani da data a Nijeriya ya kai sabon matsayi mafi girma a tarihin ƙasar a watan Nuwamba na shekarar 2025, inda mutane suka kashe kusan terabayt miliyan 1.236 na data, wato kusan petabayt 1.24, a cewar alƙaluman Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC). Wannan shi ne adadin wata guda mafi girma da aka taɓa samu tun bayan fara tattara irin waɗannan bayanai. Rahotanni sun nuna cewa wannan adadi ya ɗan zarce na watan Oktoba, wanda aka kiyasta ya kai terabayt miliyan 1.235, alamar da ke nuna ci gaba mai ƙarfi duk da matsin tattalin arziki da aka…
Read More
Otedola ya sayar da hannun jarinsa a Geregu Power kan Naira tiriliyan 1.1

Otedola ya sayar da hannun jarinsa a Geregu Power kan Naira tiriliyan 1.1

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Attajirin ɗan kasuwa, Femi Otedola, ya sayar da mafi rinjayen hannun jarinsa a kamfanin Geregu Power Plc a wata babbar yarjejeniya da ta kai kimanin Naira Tiriliyan 1.088, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 750. Wannan ciniki na daga cikin manyan muhimman sauye-sauye da aka samu a fannin lantarki a Nijeriya cikin ‘yan shekarun nan. Yarjejeniyar, wadda wasu bankuna ƙaraashin jagorancin Bankin Zenith suka ɗauki nauyin kuɗinta, ta shafi sayar da kaso kashi 95 cikin 100 na Otedola a kamfanin Amperion Power Distribution Company Limited, wanda shi ne babban mai riƙe da hannun jari a Geregu Power. Kamfanin…
Read More
NNPC zai sayar da hannun jarinsa a kadarorin mai domin jawo masu zuba jari

NNPC zai sayar da hannun jarinsa a kadarorin mai domin jawo masu zuba jari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC), ya fara ɗaukar matakan sayar da wani kaso na hannun jarinsa a wasu kadarorin mai da gas, a wani yunƙuri na sake tsara harkokinsa tare da jawo sabbin masu zuba jari zuwa ɓangaren mai na Nijeriya.  Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da NNPC ke fuskantar manyan ƙalubale na aiki, raguwa a zuba jari, da kuma ƙaruwar buƙatar jari domin ƙara yawan haƙo mai da gas. Masana na ganin wannan shiri na daga cikin manyan dabarun da kamfanin ke bi domin sauya salo daga tsohuwar hanyar gudanarwa zuwa tsarin kasuwanci…
Read More
Yadda shirin komawar Abba Gida-gida Jam’iyyar APC ya yamutsa hazon siyasar Kano 

Yadda shirin komawar Abba Gida-gida Jam’iyyar APC ya yamutsa hazon siyasar Kano 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC ya jefa tafiyar Kwankwasiyya, wadda uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yake jagoranta, cikin ruɗani. Majiyoyi da dama sun ce, babu gudu, babu ja da baya kan hukuncin da gwamnan ya yanke, ko da kuwa hakan zai kawo cikas tsakaninsa da Kwankwaso. Sanata Kwankwaso shi ne wanda ya kafa tafiyar Kwankwasiyya kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Abba a zaɓen gwamna a 2023. Sauya sheƙar Abba da ke tafe ta sake tayar da tsoffin taƙaddama a siyasar…
Read More
’Yan majalisar Ribas sun ƙi karɓar kyautar Naira 100,000 da Fubara ya ba su

’Yan majalisar Ribas sun ƙi karɓar kyautar Naira 100,000 da Fubara ya ba su

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas sun ƙi karbar kyautar Naira 100,000 da aka tura wa kowannensu a matsayin kyautar Kirsimeti bisa umarnin Gwamna Siminalayi Fubara. A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa ba ta nemi gwamnati ta tura mata wannan kuɗi ba kuma bai samu sahalewar masu yin doka a jihar ba. ’Yan majalisar sun kuma jaddada cewa, dole ne Gwamna Fubara ya kiyaye tsaro na doka da neman amincewar majalisa kafin ya kashe duk wani kuɗi na gwamnati. Yayin da ma'aikatan gwamnatin jihar ke cikin murna sakamakon samun wannan…
Read More
Kungiyar Izala ta shirya gasar karatun Alƙur’ani karo na 16 a Legas

Kungiyar Izala ta shirya gasar karatun Alƙur’ani karo na 16 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah ta ƙasa, reshen Jihar Legas, ta gudanar da taron walimar gasar karatun Alƙur’ani Mai Tsarki karo na goma sha shida, domin ƙara zaburar da yara ɗalibai wajen himmatuwa da koyon karatun Alƙur’ani da tarbiyyar Musulunci. An gudanar da taron ne a ranar Lahadi da ta gabata a harabar Babban Masallacin Juma’a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan Anfo, a cikin birnin Legas, inda dubban al’ummar Musulmi maza da mata suka hallara domin shaida taron. Gasar ta gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban Kungiyar Izala na Jihar Legas, Sheikh Imam…
Read More
Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al'ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmanci yin zaɓe, cusa ɗa'a, nuna kishin ƙasa da kyautata tarbiyya mai suna 'Adɓocacy for Integrity and Rule of Law Initiatiɓe' (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya musamman mazauna yankunan Arewa da su shiga cikin harkokin zaɓe ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaɓen shugabanni nagari. Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ya yi wannan kiran ne a yayin bikin ƙaddamar da ko’odinetocin jiha da ƙananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House,…
Read More