ukarofi

12715 Posts
Legas: Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin mambobi

Legas: Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin mambobi

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban ƙungiyar ’Yan Arewa na ƙaramar Hukumar Epe a Jihar Legas, Alhaji Ummaru Gwamna Epe, ya shawarci shugabanni da mambobin kungiyar a faɗin jihar da su ƙara haɗa kai da zaman tafiya a tsari ɗaya domin ƙarfafa martabar al’ummar Arewa a Legas. Alhaji Gwamna Epe ya yi wannan kira ne a garin Epe yayin wani taron tattaunawa da ya gudanar tare da wasu jiga-jigan ƙungiyar, wanda yake kanana shugabanci ke gudanarwa a ƙarshen kowane mako domin nazari kan matsaloli da kuma ɗaukar matakan magance su. Ya bayyana cewa, hadin kai da kyakkyawar fahimta ita ce…
Read More
Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al'ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmanci yin zaɓe, cusa ɗa'a, nuna kishin ƙasa da kyautata tarbiyya mai suna 'Adɓocacy for Integrity and Rule of Law Initiatiɓe' (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya musamman mazauna yankunan Arewa da su shiga cikin harkokin zaɓe ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaɓen shugabanni nagari. Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ya yi wannan kiran ne a yayin bikin ƙaddamar da ko’odinetocin jiha da ƙananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House,…
Read More
An buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta saka matasa cikin masu aikin sa-kai

An buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta saka matasa cikin masu aikin sa-kai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Matasa kan Tattaunawa da wayar da kan Jama’a, ya buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) da ta taimaka wajen kafa ’yan sa-kai ‘Road Marshals’ wanda ya ƙunshi matasa a kowace jiha ta ƙasar nan. Darakta Janar na kwamitin, Cif Obinna Nwaka ne ya yi wannan roƙo yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa rundunar Corps Marshal Dauda Ali-Biu a ranar Laraba a Abuja. Ya ce baya ga jawo hankalin matasa domin su zama masu hazaƙa, ƙoƙarin da ake yi zai kai ga samar da hanyoyin da za a samar da tsaro a…
Read More
Sulhu da ’yan bindiga babu ajiye makamai gazawa ce – Gwamna Lawal

Sulhu da ’yan bindiga babu ajiye makamai gazawa ce – Gwamna Lawal

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargaɗi shugabanni da hukumomin tsaro da su guji tattaunawa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai idan har za a bar su da makaman nasu, yana mai cewa irin wannan salon sulhu ba ya kawo zaman lafiya, sai dai ya ƙara tashin hankali tare da raunana ikon gwamnati. Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban baƙo mai gabatar da lacca ga mahalarta taron Eɗecutive Intelligence Management Course (EIMC) na 18 a Cibiyar Nazarin Tsaro ta ƙasa (NISS) da ke Abuja, ranar Laraba. A cewar wata sanarwa da mai magana…
Read More
Sanata Natasha za ta fuskanci shari’a, inji Ma’aikatar Shari’a

Sanata Natasha za ta fuskanci shari’a, inji Ma’aikatar Shari’a

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya tana da shari’a a gabanta, bisa tuhumar ɓatanci da laifin amfani da yanar gizo wajen yaɗa bayanan ƙarya da ake yi mata a kotunan Abuja biyu. Ofishin Babban Lauyan Gwamnati (AGF) ya ƙaryata iƙirarin Sanatar cewa shari’ar da aka shigar da ita a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da kuma Kotun ƙoli ta Tarayya abin raina doka ne da kuma tsoma bakin siyasa. A cewar ofishin AGF, an shigar da ƙarar ne bayan cikakken bincike da hukumomin tsaro suka gudanar,…
Read More
Kotun ɗa’ar Ma’aikata ta bankaɗo ƙarairayin wasu manyan jami’an gwamnati

Kotun ɗa’ar Ma’aikata ta bankaɗo ƙarairayin wasu manyan jami’an gwamnati

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ɗa'ar Ma'aikata (CCB) ta bayyana cewa ta gano wasu bambance-bambance da ake zargi da rashin daidaito a cikin takardun bayyana kadarori na ministoci, manyan sakatarori da wasu manyan jami’an gwamnati. A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na hukumar, Moses Atolagbe, ya fitar a madadin shugaban CCB, Abdullahi Bello, hukumar ta ce sabon sashen bincike da ta kafa — Financial Investigation and Fraud Analysis Unit (FIFAU) — ya tantance sama da takardun bayyanar dukiya 500. A cewar Bello, binciken ya riga ya tabbatar da bayanan kadarorin: Ministoci 9, Manyan Sakatarori 43 da Daraktoci na Tarayya…
Read More
Miyetti Allah ta yi allawadai da kisan Fulani 43 a Kebbi 

Miyetti Allah ta yi allawadai da kisan Fulani 43 a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN), ta yi allawadai da kisan Fulani makiyaya 43 a daga yankunan jihohin Kebbi da Neja.  Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar na ƙasa Alhaji Bello Aliyu Gotomo ya fitar a Hedikwatar ƙungiyar dake Abuja ranar Alhamis ɗin da ta gabata. Takardar ta ce ƙungiyar ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN) ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai ba tare da wani dalili ba, da kuma kisan mutane 43 daga cikin makiyaya masu zaman lafiya da ‘yan…
Read More
Nijeriya ta ƙara kuɗin tsaro ga jiragen ƙetare

Nijeriya ta ƙara kuɗin tsaro ga jiragen ƙetare

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da ƙarin kuɗin tsaro ga fasinjojin jiragen ƙetare da ke shiga ko fita daga ƙasar, wanda zai fara aiki daga 1 ga Disamba, 2025. Wannan sabon kuɗi zai ƙara Dala 11.5 a kowace tikitin jirgi, yana mai ɗaga jimillar kuɗin tsaro zuwa Dala 31.50 ga kowane fasinja. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasa (NCAA) ta bayyana cewa wannan kuɗin zai riƙa shiga ne kai tsaye cikin tikiti tun daga ranar da tsarin ya fara aiki. Sabon kuɗin na cikin tsarin Advance Passenger Information System (APIS), tsarin bayanan fasinjoji tun…
Read More
Cocin ERCC Graceland sun gudanar da taron ranar al’adun gargajiya na 2025

Cocin ERCC Graceland sun gudanar da taron ranar al’adun gargajiya na 2025

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Cocin Evangelical Reformed Church of Christ da a ka fi sani da ERCC Graceland dake Lafiya a jihar Nasarawa ya gudanar da wani babban taron ranar baje-kolin al'adun gargajiya ga mambobin cocin na jiha da ƙasa baki ɗaya. Taron wadda aka gudanar a cikin cocin ya samu halartar mambobin masu yare da al'adu dabandaban a jihar dama saura jihohin ƙasar nan daban daban. Da yake ganawa da wakilin mu a jihar John D. Wada bayan an kammala taron, babban Rabaran da ke kula da cocin wato Rabaran Moses A. Kudu JP ya bayyana muhimmancin…
Read More
2027: Jam’iyyar APC ta Zamfara ta amince da Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

2027: Jam’iyyar APC ta Zamfara ta amince da Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jami'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. An amince da wannan zaɓen ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan Sanata Abdulaziz Yari a yau Asabar. An yanke wannan shawara ne bayan wani ƙudiri daSanata Sahabi Ya'u mai wakiltar yankin Zamfara ta Arewa ya gabatar, kuma ɗan majalisar wakilai na tarayya Hon. Abdul Malik Zubairu mai wakiltar Maru da Bungudu ya goyi bayansa a lokacin taron. Da yake jawabi, Sanata Abdulaziz Yari ya yaba da…
Read More