ukarofi

12715 Posts
Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sarki Sanusi II

Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sarki Sanusi II

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya bai dace gwamnatin Shugaban ƙasa Bola tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Talata, a taron Oɗford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da wani littafi, Sanusi ya ce cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na gwamnati. Sanusi ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai bayyana matakan a matsayin “masu raɗaɗi amma na…
Read More
Kamfanin simintin Dangote na Gboko ya ƙaddamar da mako na ɗorewar cigaba na 2025

Kamfanin simintin Dangote na Gboko ya ƙaddamar da mako na ɗorewar cigaba na 2025

Daga RABIU SANUSI a Kano Kamfanin Dangote Cement Plc, Gboko Plant, ya fara gudanar da Makon ɗorewar Cigaba na 2025, wani shiri na shekara-shekara da ke nuni da jajircewar kamfanin wajen kare muhalli, kula da al’umma, da kuma haɓaka tattalin arziki. A jawabinsa yayin ƙaddamar da shirin, Daraktan Kamfanin, Injiniya Abhijit Dutta, ya bayyana cewa ɗorewar cigaba na nufin “cika buƙatun yau ba tare da tauye damar al’umman gaba wajen cika nasu buƙatun ba.” Ya ce, a ɓangaren ƙera siminti, ɗorewar cigaba yana nufin kiyaye daidaito tsakanin mutane, muhalli da riba. Taken makon ɗorewar cigaba na bana ya mayar da…
Read More
Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu mazauna Jihar Legas – Sarkin Hausawan Imota

Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu mazauna Jihar Legas – Sarkin Hausawan Imota

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin Hausawan karamar hukumar Imota da ke yankin Ikorodu a jihar Legas, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana cewa al’ummar Hausawa mazauna yankin Imota da sauran ƙabilun Arewacin Nijeriya suna zaune lafiya da sauran kabilu mazauna Legas da kewaye. Alhaji Ibrahim Haruna, wanda asalinsa daga karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano ne, ya bayyana haka ne a hirarsa da Jaridar Blueprint Manhaja a Legas, inda ya ce tun shekaru da dama da suka gabata ake samun zaman lafiya da jituwa tsakaninsu da sauran al’ummomin jihar. Ya ce tun bayan rikicin da aka taba samu tsakanin Hausawa…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta nanata ƙudirin farfaɗo da sashen ma’adanai domin rage dogaro da man fetur

Gwamnatin Tarayya ta nanata ƙudirin farfaɗo da sashen ma’adanai domin rage dogaro da man fetur

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Tarayya ta sake tabbatar da aniyarta ta bunkasa sashen ma’adanan kasa a matsayin wani ɓangare na yunƙurin rage dogaro da kuɗaɗen man fetur, da kuma ƙara ƙarfin tattalin arzikin ƙasa tare da samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa. Wannan jawabi ya fito ne a yayin taron wayar da kai kan aiwatar da sabon tsarin bayanan ma’adanan ƙasa na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya gudana a Kano, ranar Litinin. A jawabinsa, Kwamishinan Tarayya mai wakiltar Jihar Kano a Hukumar Raba Kuɗin Shiga ta ƙasa (RMAFC), Alhaji Adamu Fanda, ya bayyana cewa Allah Ya…
Read More
Makarantar Tanwirul Azhar ta yi taron saukar Alƙur’ani da mauludin Annabi

Makarantar Tanwirul Azhar ta yi taron saukar Alƙur’ani da mauludin Annabi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An gudanar da taron saukar karatun Alƙur'ani Karo na biyar na makarantar Tanwilur Azhar li tahafizil ƙur'an a ranar Lahadi. Taron ya samu halartar iyayen ɗalibai maza da mata da iyayen ƙasa da manyan gwanayen Alƙur'ani. Da yake zantawa da 'yan jarida a taron saukar wanda ya assasa makarantar Malam Muhammadul Hadi da ake wa laƙabi da Malam Bala, ya ce an assasa makarantar ne kusan shekaru 13 kenan da manufar sunan ta na "kore duk wani abu na rashin sani a ƙwaƙwalwa a cusa masa Alƙur'ani da tarbiyya" sun fara ne  da ɗalibai  daga …
Read More
NECO ta buɗe cibiyar jarrabawa a Birtaniya 

NECO ta buɗe cibiyar jarrabawa a Birtaniya 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Jarabawa ta ƙasa, NECO, ta buɗe cibiyar zana Jarabawar Kammala Makarantar Sakandare (SSCE) a birnin London, da ke ƙasar Biritaniya. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin Daraktan Yada labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Azeez Sani, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja. Sani ya ce wannan shiri na da nufin samar da damar yin jarabawa mai inganci da sauƙi ga ‘yan Nijeriya da ke zaune  ƙasashen waje, musamman waɗanda ba su samu damar kammala karatun sakandare ba ko kuma samun takardar da ta yi daidai da hakan.…
Read More
Kasuwar Mile-12 ta zarce sa’o’inta na ƙasashen Afrika – Bala Gozaki

Kasuwar Mile-12 ta zarce sa’o’inta na ƙasashen Afrika – Bala Gozaki

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban sashen kasuwancin dankalin turawa na kasuwar Mile 12 International Market da ke Legas, Alhaji Bala Magaji Gozaki, ya bayyana cewa kasuwar Mile 12 ta zama babbar kasuwa a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya, bisa yawan al’ummar ƙasashen waje da ke gudanar da cinikayya a cikinta. Alhaji Bala Magaji, wanda asalinsa daga karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ne, ya ce kasuwar ta kai matsayin da za a iya cewa “kasuwa ta ƙasa da ƙasa” saboda irin ci gaba da haɓakar da take samu a kowanne bangare, musamman wajen jawo ‘yan kasuwa daga ƙasashen…
Read More
’Yan bindiga sun sa harajin miliyan N15 kan al’ummar mazaɓar Sanata Tambuwal 

’Yan bindiga sun sa harajin miliyan N15 kan al’ummar mazaɓar Sanata Tambuwal 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mazauna ƙauyukan Bazar da makwabtansu a Karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato, sun koka cewa ’yan bindiga sun kakaba musu harajin Naira miliyan 15 tare da barazanar kai sabbin hare-hare idan ba a biya ba. Wadannan ƙauyuka suna yankin Mazabar Sanatan Kudu ta Kudu, inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ke wakilta. Wani mazaunin yankin, Dauda Umar, ya shaida wa manema labarai, cewa “abin yana da matuƙar tsanani” kuma yana buƙatar gaggawar kulawar gwamnati. “Ina tabbatar muku cewa ’yan bindiga sun nemi Naira miliyan 15 daga gare mu, suka yi barazanar aikata…
Read More
Ƙaramar Hukumar Ɓagwai ta yi fice wajen noma da kiwo – Hon. Belllo Gadanya 

Ƙaramar Hukumar Ɓagwai ta yi fice wajen noma da kiwo – Hon. Belllo Gadanya 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Ɓagwai, Hon. Bello Abdullahi Gadanya ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam bisa shirya taron kalankuwa na nuna al'adu na gargajiya da sana'oi da ake tun kaka da kakanni. Ya bayyana haka ne da yake zantawa da 'yan jarida a rumfar ƙaramar hukumar Bagwai da suka bajekolin kayayyaki da suke nomawa. Ya ce sun kawo abinda suke nomawa a  yankin da ke da tasiri a noma da abinda suke da su na gargajiya sun bajekolinsu jama'a sun gani. Shugaban na ƙaramar hukumar na Ɓagwai…
Read More
Riƙo da al’adun gargajiya zai ƙara mana mutunci a idon duniya – Hon. Tukur Wada 

Riƙo da al’adun gargajiya zai ƙara mana mutunci a idon duniya – Hon. Tukur Wada 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana farfaɗo da al'adun mu na gargajiya da ware ranaku na musamman a jihar Kano aka yi biki a kai wani muhimmin abu ne mai kyau da Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta yi na kyakkyawan tunani abin alfahari da farin ciki da isar da muhimmin saƙo na al'adunmu ga duniya. Shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon.Tukur Muhammad Wada ne ya bayyana hakan a yayin taron da aka yi a harakar filin kasuwar bajekoli ta Kano ya ƙara da cewa kamar a masarautar su ta Rano suna da kyakkyawan tarihi na sarauta…
Read More