31
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu tsoffin sojoji a Nijeriya sun koka kan abin da suka kira gata da alfarma da ake nuna wa manyan hafsoshin sojin ƙasar bayan barin aiki, yayin da ƙananan jami'ai ke ci gaba da fama da rashin kula da kuma rashin biyan haƙƙoƙinsu duk da shekaru da suka kwashe suna hidimtawa ƙasa. Tsoffin sojojin sun yi wannan koken ne bayan bayan sanar da irin abubuwan da za a ba wa Tsohon Babban Hafsan Tsaro da aka sauke, Janar Christopher Musa, tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da Babban Hafsan Sojin…
