14
Sep
Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kawo ƙarshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a ranar 3 ga Mayu, 2022 tare da ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso ɓilla. Ya ziyarci waɗanda ta’addanci ya shafa kamar, sansanoni ’yan gudun hijira a Jihar Borno, waɗanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya kora daga muhallan su. Guterres ya bayyana fatansa na cewa, Nijeriya na daf da samun nasara a yaƙin Boko Haram. Ya yabawa gwamnatin Buhari bisa dabarunta da suka ƙarfafawa mayaƙan Boka Haram aƙalla 37,000 kwarin gwiwar miƙa wuya tare da kai su wuraren halin gyaran hali.…
