13
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Aikin da zai ci kuɗi Naira biliyan 18.9bn yana da tsawon kilomita 27, sai dai dalilin ƙalubalen tsaro aikin ya tsaya. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da suka addabi ƙaramar hukumar sabuwa ne, babban dalilin da ya jinkirta fara aikin titin. Aikin titin, wanda aka bayar da kwangilarsa kan kuɗi ₦18.9bn, an tsara shi ne domin haɗa Sabuwa da Tashar Bawa. Ya ce aikin hanyar na ɗaya daga cikin alƙawarin yaƙin neman zaɓe ne da ya yi wa al’ummar Sabuwa. Malam Dikko Raɗɗa ya fadi haka ne a…
