13
Sep
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Asusun Tallafawa Illimi na Majalisar ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen Turai tare da haɗin gwaiwar hukumar illimin bai ɗaya ta Jihar Kano sun gudanar da taron gangamin wayar da kai dangane da shirin mayar da yara makarantu a Jihar Kano, da nufin kawo ƙarshen rashin zuwan yara makaranta mai taken "Education And Youth Empowerment Project in Northern Nigeria. Da take jawabinta yayin buɗe taron wanda aka gudanar a makarantar sakandiren gwamnati dake Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala wakiliyar Asusun tallawa illimin yara na Majalisar ɗinkin Duniya Hajiya Aisha Abdullahi ta bayyana cewa maƙasudin shirin shine…
