ukarofi

12738 Posts
Dakatar da fitar da ɗanyar kaɗanya hangen nesa ne da zai inganta tattalin arziki – Minista

Dakatar da fitar da ɗanyar kaɗanya hangen nesa ne da zai inganta tattalin arziki – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa dakatarwar wucin-gadi da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na fitar da ɗanyar ƙwarar kaɗanya zuwa ƙasar waje wani muhimmin mataki ne da aka yi cikin hangen nesa domin zai buɗe sababbin damarmaki ga tattalin arzikin Nijeriya. Ministan ya faɗi haka ne a matsayinsa na babban baƙo a Babban Taro na 20 na Yankin Arewa na Akantoci (ICAN) wanda aka yi a Minna, Jihar Neja. Idris dai ɗan Jihar Neja ne, wadda ita ce cibiyar noman ƙwarar kaɗanya a Nijeriya.…
Read More
Al’ummar Zamfara sun roƙi NCC ta dawo musu da ‘network’ da suka rasa na tsawon wata uku

Al’ummar Zamfara sun roƙi NCC ta dawo musu da ‘network’ da suka rasa na tsawon wata uku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Al’ummar shiyyar Zamfara ta Arewa sun nemi hukumar kula da sadarwa ta Nijeriya (NCC) da ta dawo musu da netwok ɗin layukan waya waɗanda aka katse sama da watanni uku da suka wuce. Mai magana da yawun ƙungiyar ƙaura Namoda Focus Forum (KNFF), Abdulrazak Bello, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya aike wa da Blueprint Manhaja. Mr. Bello ya ce, rashin netwok ɗin ya shafi al’ummar ƙananan hukumomin Birnin Magaji, ƙaura Namoda, Shinkafi, da Zurmi waɗanda a jumulla yawansu ya kai miliyan 1.78. Ya ce, kafanonin layi kamar MTN, Airtel…
Read More
Samar da masallacin Juma’a a Jami’ar FUT alkhairi ne babba – Farfesa Ibrahim B/Kudu

Samar da masallacin Juma’a a Jami’ar FUT alkhairi ne babba – Farfesa Ibrahim B/Kudu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Mataimakin Shugaban Jami'ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke ɓaɓura, Farfesa Ibrahim Sabo Birnin Kudu wato Federal University Of Technology Baɓura a Jihar Jigawa ya bayyana cewa samun masallacin Juma'a a wannan jami'a babban alkairi ne kuma babban burinsa da abinda yake so ya gani shi ne a samu ɗaliabai masu hazaƙa, tsoron Allah, ɗa,a da sanin ya kamata daga ɗaukacin al'ummar da ke wannan jami'a tun da kan ɗalibai, ma'aikata da sauran masu ruwa da tsaki na wannan jami'a ta FUT da ke ɓaɓura a Jihar Jigawa Nijeriya.  Farfesa Birnin Kudu ya bayyana haka…
Read More
Karuwar bashin da Nijeriya ke ci abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas 

Karuwar bashin da Nijeriya ke ci abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna damuwa kan yadda bashin Nijeriya ya ƙaru zuwa Tiriliyan 149.39  a farkon 2025, kwatankwacin dala biliyan 97, wanda ya wuce iyakar kashi 40 da doka ta gindaya, inda ya kai kashi 52 na GDP. Abbas ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na ƙungiyar WAAPAC a Abuja, yana mai cewa hauhawar bashin na barazana ga ɗorewar tattalin arziki, tare da gargaɗin cewa rancen da ke tallafa wa cin hanci da ciyar da buƙatu bai kamata a ci gaba da shi ba. Ya ce dole rance ya kasance…
Read More
Hukumar SEPA ta ƙaddamar da ba marasa lafiya magani kyauta a Katsina

Hukumar SEPA ta ƙaddamar da ba marasa lafiya magani kyauta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban hukumar kare muhalli ta Jihar Katsina Alh. Kabir Usman Amoga ya ƙaddamar da shirin duba marasa lafiya tare da basu magani kyauta a ƙaramar hukumar Katsina. Marasa lafiyan maza da mata sama da 500 a firamaren Dutsen Amare dake cikin garin Katsina suka amfana da tallafin magungunan. A jawabin sa shugaban hukumar kare muhalli ta Jihar Katsina Alh. Kabir Usman Amoga ya bayyana cewa" yayi wannan ƙoƙari ne domin tallafama al'umma musamman mabuƙata duba da irin halin da ake ciki. Amoga ya bayyana cewa idan kaje asibiti za kaga al'umma mabuƙata amma kuɗin abin…
Read More
Gwajo-Gwajo yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomi

Gwajo-Gwajo yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An yabawa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina bisa ba ƙananan hukumomin jihar damar cin gashin kansu wanda ke ba su damar gudanar da ayyukan raya ƙasa don inganta walwala da jin daɗin al'ummarsu musamman mutanen karkara. Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina. Sanarwar ta bayyana cewa a baya-bayan nan ƙananan hukumomin sun gudanar da ayyuka daban daban na kawar da zaizayar ƙasa da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ɗakunan shan magani…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa da Sanata Barau Jibrin ku ceto rayuwar Hon. Nasiru Dayi

Gwamna Dikko Raɗɗa da Sanata Barau Jibrin ku ceto rayuwar Hon. Nasiru Dayi

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Ranar 14 ga Augusta,2025, da magariba, wasu yan bindiga da aka ƙiyasta sama da 60 ɗauke da muggan makamai sun far wa garin Dayi inda su ka wuce kai tsaye zuwa gidan Hon. Nasiru Dayi da ke tsakiyar garin kuma su ka kama shi su ka tafi da shi, shi kaɗai, duk da ƙoƙarin tirjiya da ya yi musu, kuma ance sun ja shi a ƙasa yadda su ka yi masa raunuka a kafaɗunsa da bayansa. Bai fi yan kwanaki ba mun yi waya da shi ya ke ce min zai shigo Kano zai ga CMD…
Read More
Barace-baracen ƙananan yara a tituna abin dubawa ne

Barace-baracen ƙananan yara a tituna abin dubawa ne

Ga duk mai dubi zuwa ga yadda aka jefa ƙananan yara cikin harkar barace- barace, musamman a biranen ƙasar nan zai ga cewa akwai sosar zuciya mutaƙa, musamman ganin yadda yaran ke fama da wahala, sannan ga ɓata sunan Hausawa da abin ke jawowa. Akwai abubuwa da dama, waɗanda idan mutum ya yi dubi zuwa garesu za su dagula masa rayuwa ya ma rasa abin da ke masa daɗi, musamman idan aka duba yadda wasu abubuwa ke jawo wa rayuwar al’ummar da abin ya shafa. Wasu daga cikin waɗannan abubuwa, waɗanda kuma za mu iya cewa babu wani mai farin…
Read More
Gwamnati na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bunƙasa harkar noma – Injiniya Rabi’u Bichi

Gwamnati na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bunƙasa harkar noma – Injiniya Rabi’u Bichi

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na kashe maƙudan kuɗaɗe don ganin ta bunƙasa harkar noma da nufin magance matsalar abinci a faɗin ƙasar nan.  Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Gudanarwar Raya Kogunan Haɗeja/Jama'are Inginiya Rabiu Suleiman Bichi yayin buɗe wasiƙun 'yan kwangila don neman kwangilar gudanar da wasu manyan ayyuka a ɗakin taro na hukumar dake kan titin Maiguri, Hotoro a Jihar Kano.  Bichi ya jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na ganin abinci ya wadata a ƙasar nan wanda hakan ya sa shugaban ƙasa yake sahalewa hukumomin da…
Read More
Ba za a bar Kano baya ba wajen yin rijistar zaɓe – Sheikh Tijjani Auwalu

Ba za a bar Kano baya ba wajen yin rijistar zaɓe – Sheikh Tijjani Auwalu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Yawan malamai da masana da yawan al'umma da Ubangiji ya albarkaci Kano da shi da kuma wayewar siyasa da sauran al'amura da kowa ya san Kano tana da wannan baiwar na cewa mutanen Kano wayayyayu ne ba za su yarda a barsu a baya ba na yawan katin zaɓe da hukumar zaɓe ta fara yi a yanzu haka, da ake ganin kamar za a bar Kano a baya, Kanawa ba za su yarda da wannan haƙƙi ba, kuma nasan halinsu za su tashi tsaye su je su yi rijista fiye da yadda ake tunani musamman…
Read More