12
Sep
Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi sun kama wani ma'aikacin gidan gyaran hali, Ibrahim Abubakar Ka'oje bisa ga zargin hannu a cikin wata sata da aka yi a gidan Hajiya Rabi da ke garin Ka'oje a ƙaramar Hukumar Bagudo a jihar Kebbi. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sufurtanda Nafi'u Abubakar ya bayyana cewa an samu nasarar kama wannan jami'in ne bayan da Hajiya Rabi ta kai rahoton waɗansu mutane sun haura ta gidan ta a garin Ka'oje inda su kuma 'yan sandan ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka kamo shi, bayan bincika mai…
