ukarofi

12738 Posts
‘Yan sanda a Katsina sun kama wani ɓarawon mota

‘Yan sanda a Katsina sun kama wani ɓarawon mota

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wani mutum Muhammad Abdullahi mazaunin Ƙofar ƙwaya, Katsina da wata mota ƙirar Toyota Corolla wanda ake zargi ya sato daga Abuja. Motar mallakar Mr Sunday Solomon Jiyah mazaunin Abuja,yan sanda sun gano ta a wata maɓoya da ke ƙofar ƙwaya a cikin garin Katsina. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da haka yace jami'an su sun kama wanda ake zargi tare da gano motar. DSP Sadiq Aliyu ya bayyana cewa wanda ake zargi ya faɗawa yan…
Read More
Mujaddadi Ɗanfodiyo sak ‘yan kwangila sam!

Mujaddadi Ɗanfodiyo sak ‘yan kwangila sam!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Na ga ya dace na dora alkalami don jan hankali kan wasu da su ka takarkare sai sun aibanta Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo. Aikin waɗannan mutanen na nan a kafafen sada zumunta inda su ke jefa miyagun sunaye da alaƙanta mummunan tarihi ga Shehun malamin. Waɗanda ke kwangilar nan sun tsara wata loga don samun saukin yaɗa manufofin su inda su ka rubuta “FODIYANCI SAM MUSULUNCI SAK” kuma ba ma lallai mutanen nan Musulmi ba ne don haka ba wani abun da ya haɗa su da Musulunci har ya zama sak a wajen su. Idan har…
Read More
Wane ne miji nagari?

Wane ne miji nagari?

Daga AISHA ASAS Duk macen da hankali ya saukar wa za ta fara roƙon Allah miji nagari kamar yadda ta ji iyayenta na ma ta a kullum. Sai dai abin mamaki da yawa a mata idan ka tambaye su wane ne miji nagari sai ka ga amsar su ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa. Ban ce bai kamata ta yi addu’ar ba, hasali ma ita ce makamin da ya kamata ta riƙe tun balagar ta har sai an kaita ɗakin aure. Kafin in zayyano alamomin miji nagari, zan fara da jan kunne ga mazaje. Annabin rahma (S.A.W) ya ce “Mafifita…
Read More
Alamomin da ke nuna rashin wadatattun ruwa a jiki

Alamomin da ke nuna rashin wadatattun ruwa a jiki

Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Muna godiya da jimirin bibiyar mu da ku ke yi. A wannan makon za mu tattauna ne kan muhimmin abin da jiki ba ya iya rayuwa sai da shi, kuma rashin nasa babbar illa ce da ka iya haddasa wasu cututtuka manya da ƙanane. Ba kuwa komai nake magana kai ba face ruwa. Na san wasu za su yi mamakin jin rashin isasshen ruwa a jiki zai iya haifar da cuta ga jiki, kasancewar ba su ɗauke su a matsayin komai ba face abin kawar da ƙishirwa. To…
Read More
Gwamna Abba ya karɓi rahoton aikin hajji na 2025

Gwamna Abba ya karɓi rahoton aikin hajji na 2025

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Da yake jawabi jim kaɗan bayan da ya karbi rahoton, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati za ta nazarci rahoton tare da ɗaukar matakan da suka dace a duk inda ake da buƙatar gyara domin cigaba da samun nasara aikin hajji na gaba. Ya bayyana jin daɗin sa bisa yadda Jihar Kano ta samu lambobin yabo a matsayin jihar da tayi fice wajen kula da walwala da jin daɗin alhazanta fuskar masauki da ciyarwa da kuma tsarin zirga-zirgar mahajjatanta. Ya godewa hukumar jin daɗin alhazai ta jiha da wakilan kwamitocin aikin Hajjin da aka…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta zamanantar da gidan talabijin na jihar

Gwamnatin Katsina za ta zamanantar da gidan talabijin na jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD Majalisar zartaswa a zaman ta karo na 13 ƙarƙashin shugabancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da inganta gidan talabijin na jihar zuwa tsari na dijital. Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu Dr Bala Salisu Zango ya sanar da haka bayan kammala taron majalisar zartaswa karo na 13. Kwamishinan ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin na shirin shigar da na'urar watsa shirye-shirye mai ƙarfin 5KW da wata mai karfin 2.2KW a matsayin madadi. Haka kuma Dr Bala ya ƙara da cewa za a sanya na'urar amfani da hasken rana (solar) domin tabbatar da ɗorewar wutar lantarki. Kwamishinan ya ce…
Read More
Yadda ‘yan bindiga ke kare al’umma bayan an yi sulhu da su a Katsina

Yadda ‘yan bindiga ke kare al’umma bayan an yi sulhu da su a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Bayan sulhu da aka cimma a ƙaramar hukumar Jibiya ta Jihar Katsina, 'yan bindigar da ke addabar al’ummomin yankin yanzu sun koma kare su daga hare-haren ɓarayin daji dake riƙe da makamai. Wani mazaunin ƙauyen Magama, Abubakar Mohammed, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai ya nuna godiya bisa samun zaman lafiya da aka yi a yankin. Yayin da yake bayani kan yadda zaman lafiya ya dawo, Mohammad ya tuna cewa kusan watanni shida da suka gabata aka cimma yarjejeniyar sulhu da ƴan bindigan. Ya ce tun daga lokacin ba a sake…
Read More
Ƙungiyar mabiya Ahlulbaiti reshen Kano ta yi kira ga mabiyanta su fito su karɓi katin zaɓe

Ƙungiyar mabiya Ahlulbaiti reshen Kano ta yi kira ga mabiyanta su fito su karɓi katin zaɓe

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Duba da yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ke ci gaba yi wa 'yan ƙasa rajistar katin jefa ƙuri'a, ƙungiyar musulmi ta mabiya Shi'a a Nijeriya, wato 'Ahlul Baiti Nijeriya ta yi kira ga 'ya'yan ƙungiyar da ba su da katin zaɓe, cewa da su hanzarta yin haka, kasantuwar wajibcin katin a harkokin su na siyasa. Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar ƙungiyar ta mabiya da masoyan Ahlul Bait (as) ta ƙasa reshen jihar Kano, Hon. Adamu Kabiru (Auduwa) a yayin ganawa da manema labarai a Kano. Honourable Adamu Kabiru ya ƙara…
Read More
NSCDC a Katsina ta daƙile ƙoƙarin karkatar da gidan sauro a Matazu

NSCDC a Katsina ta daƙile ƙoƙarin karkatar da gidan sauro a Matazu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Maganin sauron da ke haɗe da maganin zazzaɓin cizon sauro, hukumar kula da kiyon lafiya a matakin farko ta samar kyauta domin rabawa al'ummar jihar. A zirga zirga da take yi na tabbatar da tsaro jami'an tsaron na farin kaya suka ci tare haya buɗaɗɗa ɗauke da buhu 35 na gidan sauro. Kowane buhu yana ɗauke da gidan sauro 50 da motar ta ɗauko daga garin Matazu akan hanyar ta na zuwa Kano. Nan take suka kama direban motar zuwa hedkwatar hukumar a Katsina. A yayin gudanar da bincike kamar yadda hukumar ta sanar direban…
Read More
Gwamnan Raɗɗa ya cika shekara 56 da haihuwa

Gwamnan Raɗɗa ya cika shekara 56 da haihuwa

MATSAYI NA TARIHI: Rayuwar Gwamna Raɗɗa ta hidima ga al'ummar katsina. “Gwamnati wata hukuma ce da ke hana zalunci, sai dai irin wanda ita kanta ta aikata,” a cewar babban malamin Larabawa, Ibn Khaldun, tun ƙarni da dama da suka wuce. Amma a cikin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, Katsina ta samu jagora wanda ya tabbatar cewa mulki na iya zama kayan adalci maimakon cikas gare shi. Tafiyar Raɗɗa daga aikin koyarwa a Raɗɗa Day Secondary School zuwa zama gwamna na jihar ta kasance shaida ta ƙarfin hidima mai ma’ana. Kamar yadda muka sani, wasu shugabanni suna bayyana zuwansu da hayaniya,…
Read More