08
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Haɗin gwiwa na rundunar ƙasa da na sama da sojojin sama da ake kira FANSAN YAMMA sun sami nasarar kashe 'yan bindiga 23 da ceto mutane da akayi garkuwa da su 26 a ƙananan hukumomin Ƙanƙara da Matazu. Haka kuma bayanai da yake fitowa daga hedkwatar sojoji ta ƙasa, sojojin sun kama wasu 'yan ta'adda guda 14 a shiyar Arewa maso Gabas da Arewa maso kudu. Wasu mutane huɗu da ake zargi 'yan ƙungiyar jihadi ISWAP daga Arewa maso kudu sun miƙa wuya ga sojojin. Waɗanda sojojin suka ceto sun haɗa da mata 12,yara ƙanana…
