ukarofi

12471 Posts
El-Rufai ya nemi diyyar Naira biliyan 10 da neman afuwa daga ministan tsaro

El-Rufai ya nemi diyyar Naira biliyan 10 da neman afuwa daga ministan tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nemi ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya biya shi Naira biliyan 10 tare da neman afuwarsa a bainar jama’a kan kalaman da ya ce sun bata masa suna. Lauyoyin El-Rufai ne su ka gabatar da bukatar a wata wasikar gargadi kafin daukar matakin shari’a da suka aika wa ministan ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026. Bukatar ta biyo bayan bayyanar Musa a shirin Politics Today na Channels Television ranar 3 ga Satumba, inda ya yi magana kan matsalar tsaro a Kaduna tare da yin zarge-zarge…
Read More
Dambarwar riƙe iyali: ’Yar Maroko ba ta tare da Sheikh Gumi — Lauya

Dambarwar riƙe iyali: ’Yar Maroko ba ta tare da Sheikh Gumi — Lauya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Lauyar ’yar ƙasar Maroko, Khadija Diab, ta ce matar ba ta tare da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, kamar yadda mijinta ya yi zargi. Lauyar, Bilkisu Abdulrasheed Chedi, ta ce Khadija ta koma Maroko tun watan Afrilun 2026, kuma tun daga wannan lokacin take zaune tare da iyalanta. Chedi ta ce ƙungiyarta, Women Aware of Rights Initiative, ta taimaka wa Khadija wajen samun takardar tafiyar gaggawa bayan da mijinta, Nasiru Idris Musa, ya riƙe fasfo ɗinta. Lauyar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Sheikh Gumi,…
Read More
Gwamnan Kano ya ba da umarnin binciken kisan Danshagamu

Gwamnan Kano ya ba da umarnin binciken kisan Danshagamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa shahararren mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu. Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta gano tare da kama wadanda ke da hannu a kisan, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin firgitarwa da ba za a amince da shi ba. News Point Nigeria ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kuma bukaci gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gano dukkan wadanda ke…
Read More
Rundunar sojin Nijeriya ta sauya wa manyan kwamandoji wuraren aiki

Rundunar sojin Nijeriya ta sauya wa manyan kwamandoji wuraren aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta sake yin wani gagarumin garambawul a shugabancinta, inda ta sauya wa wasu manyan kwamandojin soji wuraren aiki. A wani ɓangare na sauye-sauyen, an tura Manjo Janar IA Ajose daga Hedikwatar Rundunar Soji domin jagorantar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, wadda ke yaƙi da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a yankin. Ajose ya maye gurbin Manjo Janar AE Abubakar, wanda aka tura Cibiyar Tarihi da Makomar Rundunar Sojin Nijeriya, inda zai zama Shugaban Kwalejin Binciken Ayyukan Soji. Rundunar ta ce sauye-sauyen, waɗanda Babban Hafsan Sojin…
Read More
Ambaliya ta yi awon gaba da ɗalibi ɗan shekara 13 a Abuja

Ambaliya ta yi awon gaba da ɗalibi ɗan shekara 13 a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da wani ɗalibi ɗan shekara 13 mai suna Alhassan Jamil a ƙaramar Hukumar Gwagwalada da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Alhassan ɗalibi ne a ƙaramar makarantar sakandaren Ihyau El-Burhan Academy da ke Phase 3, Gwagwalada. Mahaifin yaron, Jamil Maikasuwa, ya ce yana kan hanyar kai ɗansa makaranta a kan babur lokacin da lamarin ya faru. Ya bayyana cewa yayin da suke ƙoƙarin tsallake wata magudanar ruwa mai ramuka biyu, sai ya lura cewa ruwan yana gudu da ƙarfi. A cewarsa, ya taka birki, amma ɗansa ya firgita, ya…
Read More
Kotu ta ɗaure mutane biyu shekaru tara kowanne kan ba yara abubuwan maye

Kotu ta ɗaure mutane biyu shekaru tara kowanne kan ba yara abubuwan maye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Kotun Majistare da ke Gwammaja a Kano ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin zaman gidan yari na jimillar shekaru tara kowannensu, bayan ta same su da laifin bai wa yara masu rauni maganin roba da wasu abubuwa masu maye. News Point Nigeria ta ruwaito cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin, Kabiru Isa, wanda aka fi sani da Mada, da Usman Hamisu, wanda aka fi sani da Mani, sun samu hukuncin ne daga Mai Shari’a Muhammad Alhaji Sani na Kotun Majistare mai lamba 44 da ke Gwammaja, Kano. An same su da laifin…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta saka tallafin data ga miliyoyin ɗalibai

Gwamnatin Tinubu ta saka tallafin data ga miliyoyin ɗalibai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire kuɗin data ga miliyoyin ɗaliban Nijeriya da ke amfani da wasu manhajoji da kafafen koyarwa da gwamnati ta amince da su, a wani sabon shiri da aka ƙaddamar domin sauƙaƙa wa ɗalibai samun damar karatun zamani ta hanyar intanet. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da Shirin Samar da Damar Samun Kafafen Koyarwa da Abubuwan Ilimi Ta Intanet Ba Tare da Kuɗin Data ba a Nijeriya. Alausa ya ce, shirin, wanda ke ƙarƙashin ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na…
Read More
Gobara ta tashi a tashar jirgin ƙasa ta Idu a Abuja

Gobara ta tashi a tashar jirgin ƙasa ta Idu a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta bayyana cewa, wata ƙaramar gobara ta tashi a tashar jirgin ƙasa ta Idu da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, sakamakon matsalar wutar lantarki. Lamarin ya faru ne a ɗakin tsarin samar da lantarki mai ƙaramin ƙarfi (low-Voltage electrical room) na tashar a yammacin Laraba, inda aka gano gobarar da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Hukumar ta ce, ma’aikatan kula da tashar sun yi gaggawar shawo kan gobarar, inda suka kashe ta cikin ɗan lokaci. A cikin sanarwar da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na…
Read More
Matashin Kano ya yanke yatsarsa kan alƙawarin miliyan N80 na tsafi

Matashin Kano ya yanke yatsarsa kan alƙawarin miliyan N80 na tsafi

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyar, ciki har da wani matashi mai shekaru 27 da ake zargi da yanke yatsarsa da kansa bayan an yi masa alƙawarin ba shi Naira miliyan 80 a wani lamari da ake zargin yana da alaƙa da tsafi. Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 29 ga Agusta 2026, bayan matashin mai suna Yusuf Mahmuda, ɗan asalin Rano, ya je ofishin ’yan sanda domin kai ƙorafi. A cewar Kiyawa, Yusuf ya shaida…
Read More
Rikicin Amurka da Iran ya ɗaga farashin ɗanyen mai zuwa Dala 100 a ganga

Rikicin Amurka da Iran ya ɗaga farashin ɗanyen mai zuwa Dala 100 a ganga

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya yi tsalle zuwa kusan dala 100 kan kowace ganga a ranar Laraba, yayin da ƙara tsanantar rikicin soja tsakanin Amurka da Iran ke ƙara jefa fargaba kan yiwuwar samun matsala wajen samarwa da safarar ɗanyen mai a duniya. ƙarin tashin farashin ya biyo bayan wasu sabbin hare-haren soji da suka shafi jiragen dakon ɗanyen man Iran da kuma sojojin Amurka da ke Jordan, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin ‘yan kasuwar mai kan yiwuwar rikicin ya haifar da tsaiko wajen samarwa, safara da fitar da ɗanyen mai daga…
Read More