ukarofi

12471 Posts
Shaye-shaye ya sa na rasa aiki a kamfanin mai — Wani ɗan Nijeriya

Shaye-shaye ya sa na rasa aiki a kamfanin mai — Wani ɗan Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗan Nijeriya mai suna Abraham ya bayyana yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi suka janyo masa rasa aikinsa a wani kamfanin mai, suka lalata dangantakarsa da iyalansa da abokansa, tare da jefa kusan shekaru 10 na rayuwarsa cikin asara. Abraham, wanda a yanzu yake kan hanyar murmurewa daga jarrabar miyagun ƙwayoyi, ya bayyana irin abubuwan da ya fuskanta a shirin NarcoTales S4 E8, wanda aka watsa a tashar YouTube ta Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ranar Juma’a. A cewarsa, ya fara fahimtar girman illar da shaye-shayen suka yi masa ne bayan…
Read More
Dalilin da ya sa kamfanin Uber ya fice daga Nijeriya bayan shekaru 12 – FAAN

Dalilin da ya sa kamfanin Uber ya fice daga Nijeriya bayan shekaru 12 – FAAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya ta Nijeriya (FAAN) ta musanta cewa tana da hannu wajen ficewar kamfanin jigilar fasinjoji ta manhajar Uber daga Nijeriya, tana mai cewa matakin da kamfanin ya ɗauka na iya kasancewa sakamakon la’akari da yanayin tattalin arziki da dokokin da suka shafi harkokinsa. Idan za a iya tunawa cewa Uber ta dakatar da ayyukan jigilar fasinjoji ta manhajarta a Nijeriya daga ranar 2 ga Satumba, 2026, bayan shafe shekaru 12 tana gudanar da ayyukanta a ƙasar. Manajan Daraktar FAAN, Olubunmi Kuku, ta ce duk da haka hukumar ta samu…
Read More
Tallafa wa ta’addanci: CBN ya ƙara tsaurara bincike kan bankuna

Tallafa wa ta’addanci: CBN ya ƙara tsaurara bincike kan bankuna

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara tsaurara sa ido da bincike kan bankuna da sauran cibiyoyin kuɗin ƙasar, musamman wajen gano haɗarin amfani da tsarin kuɗin ƙasar wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci. Matakin na daga cikin ƙoƙarin hana masu aikata laifuka amfani da tsarin hada-hadar kuɗi na Nijeriya wajen ɓoye ko jigilar kuɗaɗen da ake amfani da su wajen ayyukan ta’addanci. CBN ya ce, ya ɗaga batun sa-ido kan hanyoyin samar da kuɗin ta’addanci zuwa cikin muhimman abubuwan da yake bai wa fifiko a halin yanzu. Hakan ya sa aka ƙara mayar da hankali kan bibiyar…
Read More
Dangote ne ya kai mahaifiyata gida daga asibiti bayan ta haife ni – Davido

Dangote ne ya kai mahaifiyata gida daga asibiti bayan ta haife ni – Davido

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shahararren mawaƙin Nijeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Daɓido, ya bayyana cewa dangantakarsa da fitaccen attajirin nan Aliko Dangote ta samo asali ne tun lokacin ƙuruciyarsa, inda ya ce Dangote na da kusanci da iyalinsu tun kafin ya zama ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwa a Afirka. Davido ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a Legas, yayin da yake magana kan dangantakarsa da Aliko Dangote. Ya ce Dangote ya daɗa yana hulɗa da mahaifinsa, ɗan kasuwa Adedeji Adeleke, kuma abotarsu ta yi shekaru masu yawa. A cewar Davido,…
Read More
Hukuma ta maka Matatar Dangote kotu kan inganci da ayyukan dakon mai

Hukuma ta maka Matatar Dangote kotu kan inganci da ayyukan dakon mai

Daga NAHDI MUSA MUHAMMAD Kwanaki ƙalilan bayan kammala sanar da sayar da hannun jarin matatar Dangote ga jama’a ta hanyar IPO, sabuwar taƙaddama ta kunno kai tsakanin matatar da Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), inda ɓangarorin biyu suka tsinci kansu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan inganci da rarraba iskar gas ta propane, da kuma dakatar da ayyukan lodin kayayyakin mai a kan manyan motoci. Taƙaddamar ta ƙara tsananta ne bayan NMDPRA ta umarci dakatar da lodin propane da fitar da shi ta manyan motoci daga matatar Dangote, matakin…
Read More
Ƙasashen da suka cigaba ba gwamnati suka zuba wa ido ba – Isyaku Shanono

Ƙasashen da suka cigaba ba gwamnati suka zuba wa ido ba – Isyaku Shanono

Ƙungiyar 'Yartasha Peace And Unity Development Association, sun kai ziyarar ban gajiya da girmamawa ga shugaban sashen walwala da jin daɗin jama'a na ƙaramar hukumar Bichi a ofishinsa da ke sakatariyar yankin. A sanarwar jami'ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ce, da yake jawabi shugaban sashen, Alhaji Ibrahim Isyaku Shanono, ya bayyana irin yadda ƙasashen ƙetare suka cigaba ta hanyar ƙungiyoyin jama'a na ayyukan sa kai tare da haɗin kan al'umma baki ɗaya. "Shi ya sa kullum tunaninmu ya za mu taimaki al'umma, musamman ƙungiyoyi, duk mutanen da suka haɗa kai suka zama ƙungiya domin…
Read More
APC za ta samu nasara a 2027 – Sanata Yari

APC za ta samu nasara a 2027 – Sanata Yari

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau Sanata Abdulaziz Yari, wanda kuma shine darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, za ta lashe zaɓe mai zuwa. Ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a yau Juma'a a gidansa da ke Talata Mafara a Zamfara. Yari ya ce yaƙin neman zaɓen jam'iyyar na 2027 za su ta'allaƙa ne kan nuna nasarorin cigaban tattalin arzikin gwamnati shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. A cewar tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Shugaba Tinubu yana ci gaba da jajircewa wajen farfaɗo…
Read More
Manoman Nasarawa sun rungumi sabbin dabarun noma daga Sasakawa Afirka

Manoman Nasarawa sun rungumi sabbin dabarun noma daga Sasakawa Afirka

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Ƙananan manoma a jihar Nasarawa suna samun ƙarin girbi da abinci mai gina jiki bayan sun fara amfani da sabbin fasahohin noma masu jure sauyin yanayi da kuma iri masu inganci irin na zamani dake ɗauke da sinadaren gina jiki. Shirin na musamman da ke inganta abincin noma da tallafa wa ƙananan manoman wata ƙungiya da ake kira Sasakawa Africa Association SAA-Nigeria ce ke gudanar ƙarƙashin tallafin gidauniyar NIPPON ta ƙasar Japan. A lokacin ziyarar manema labarai da aka yi a cikin al’ummomin Tundun Adabu da Angwan Hamidu na ƙaramar hukumar Obi a jihar,…
Read More
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 kan tsohon shugaban bankin NEXIM

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 kan tsohon shugaban bankin NEXIM

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin Fitar da Kayayyaki na Nijeriya (NEXIM Bank), Robert Orya, kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.4. News Point Nigeria ta ruwaito cewa kotun ta yi watsi da ƙarar da Orya ya ɗaukaka, tare da tabbatar da hukuncin da Kotun ƙoli ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja ta yanke masa kan tuhume-tuhume 49. Kotun ta yanke wa Orya hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 kan kowanne daga cikin tuhume-tuhumen 49, wanda idan aka tara zai…
Read More
An hallaka shahararren mai sharhi kan siyasa na Kano, Danshagamu a gidansa

An hallaka shahararren mai sharhi kan siyasa na Kano, Danshagamu a gidansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An hallaka shahararren mai sharhi kan siyasa da ke zaune a Kano, Ibrahim Khalil ɗanshagamu, a gidansa da ke Jihar Kano, lamarin da ya jefa mabiyansa da al’ummar yankin cikin jimami. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa ɗanshagamu, wanda ke gudanar da harkokinsa ƙarƙashin sunan ɗanshagamu International, ya shahara da bidiyoyin da yake wallafawa a kafafen sada zumunta, inda yake yin tsokaci kan siyasa, addini da kuma al’amuran al’umma. ƙungiyar Amnesty International Nigeria ta tabbatar da mutuwarsa a ranar Laraba, inda ta ce an gano gawarsa cikin jini a cikin gidansa. ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama…
Read More