12
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara shirin sauya Kamfanin Hada-Hadar Magunguna na Jihar (JIPHARMA) daga kamfanin da ke sayar da magunguna zuwa kamfanin da zai riƙa kera magunguna. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da sabuwar Hukumar Gudanarwar JIPHARMA. Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na sake fasalin kamfanonin gwamnati domin su kasance masu inganci da dorewa, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar. Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta samu shawarwari daga wasu masu zuba jari da ke sha’awar shiga harkokin kamfanin ta…
